"Nooooooooooo"
ta soma girgixa kanta, impossible,
ta ďago tana kallonsa,Assad can't divorce me Abba, wannan ba Assad ďina bane, Assad baxai rubutamin wannan abin ba hr Gobe ni matarsa c....... Abba ya dauketa da Mari,
Ashe ke shashasha ce, marar hankali, dan ubanki ni xn rubutomaki takardar ne kome, ni ke aurenki?
Hannunta dafe a kuncinta hawaye na xubo mata ta dubi Anna kafin ta maida kallonta ga Abba,
Don't mean to hurt you Abba, Assad wani jigo ne a rayuwata, yana sona Ina sonsa, wlhy baxai sake ni ba, munfurcine aka qull.... Bata qarasa ba ya sake dauketa wani Marin karo na biyu wnda yasata tsananin gigicewa hr tana neman hanyar fita, Anna ta riqota,
Nine xn maki Munapurci kenan, ni Farah ni kike gayawa haka Akan ďa namiji? Ni mahaifinki, wlhy akan Assad sai na yafeki kuma tunda Babu aure tsakanin ku ynxu dole sai kin auri khamis dama shine mijinki tun asali,
Anna tace haka ne Farah sai ynxu nagane mahaifinki na sonki da gsky, Ashe Assad bashi da kirki mutumin banxa ne, duk yarda da halaccin da aka masa da wannan Xai sakamana, ya toxartamu a idon duniya Gashi sai xancen ake a dangi, nima naji baxan iya yafewa Assad ba, ko dawowa yayi baxaki auresa ba ke ko bayan rai na,
Na shiga uku ni Farah, ta xube qasa dafe da kanta tana wani irin kuka mai tsuma jiki,
'why the hatred Anna and Abba? It can't be Assad, don't hate him please Anna, ke kadaice keson Assad Dama Abba baya sonsa Wlhy........ yayi cikinta xai daketa Anna ta hanasa,Karka daketa mansur, kabarta, guguwar so ne ke ruďarta,kinsan *sabon salon ďa namiji* ne(Lubieee) ?, kinsan Waye namiji Kuwa, yaushe kika girma hr kikasan miye so, tun kafin a haifi mahaifinki nasan ko Waye namiji, Muna nan xaki xo ki samemu, bake ba Assad ki rubuta ki ajiye....... ta juya a fusace ta fice, haka Abba da khamis ma, suka barta nan falon tana darxar kuka,
[03/12, 9:59 p.m.] Pherty👯: Wasa Wasa hr Anyi 2 months ba labarin Assad,Abba ya daina nemansa ya cire hannunsa a ciki, haka ma khamis sun cigaba da harkokinsu kamar da,
Anna ma bata da wata damuwar Assad a xuciyarta illah bacin ransa duk ta tuna dashi ko ta dubi halin da Farah ke ciki sai tayi Allah ya tsine masa(abinka ga tsofi😱)
Wani sa'in ma idan Farah na kuka bata ganin laifinta sai dai tace
Ba laifinki bane Farah, laifinane nida na cusa maki sonsa lokacin da bakyasonsa hr naxo na aura maki shi yayi maki wannan sakayya, nice nan naja maki wannan matsalar da kike ciki, ta soma sharar kwallah ,
Farah Kan ďauke idanuwanta akanta cikin halin ko in kula akan maganganunta ta watsar tayi shigewarta ďaki, komai xasuyi baxata iya barin Assad ba kuma xata korasa ko wane lokacine baxata auri khamis ba,
Tayi wata irin Rama sosai, hr wani haske tayi, idanunta sun qara fitowa sosai, skul ma idan taje sai dai taje Nata lectures amma baxataje karantarsuwa ba cos she can't, idan ta duba class ďin ba abokin fadanta Assad,
Jabir da Umar ma suna cikin wani yanayi duk iya qoqarinsu sun kasa gano inda abokinsu yake ballantana suji dalilinsa na Sakin Farah, Gashi duk safiya sai Hauwa'u ta xo masu tana kuka tana tambayar ko an sami labarin inda Assad ďin yake?
Amsar ďayace A'ah 😞
Akwai wani lokaci da Anna ta sami Farah ďakinta tana kuka tana sambatu akan Kada Assad ya gujeta ba laifinta bane dole aka mata,
Anna ta dafata fuskarta da alamar tambaya,
Macece damuwarki Farah akan Assad, kullum kina kuka kina neman afuwarsa me kikayi masa gayamin naji ko shine dalilin Sakin da yayi maki?Ta girgixa kanta tana hawaye sosai,
Anna sun cuceni Wlhy sune suka rabani da Assad, sun batamin rayuwa 😭Jikin Anna na soma rawa sosai, cikin tashin hankali ta nemi guri ta xauna ,
Gayamin Farah, kigayamin nace menene meyafaru dake?
Sun min fyade Anna bayan sun sumar da Assad K...... ta kasa qarasawa saboda kuka da yaci qarfinta hr shiďewa takeyi idanunta sunyi jawur a kumbure,
Subhanallah, na shiga uku ni Hadixa, sun miki fyade Farah, su Waye su? Meyasa suka keta maki *Martabar ki*(Ummi Aysha), itama Anna ta soma Kuka sosai,
Shikenan dole Assad ya sakeki yasan abinda kenan, amma nayi xaton ynda muke dashi Komenene xai haqura ya xauna dake Farah, Allah ya isar miki akansu,
Farah bata ce komai ba sai kukan da take,
Tuntuni meyasa baki gayamin ba kika boye?
Nan ma shiru ba amsa,
Tor amma idan kika auri khamis yasan halin da kike ciki ai xai wulaqantaki ya toxartaki Farah, gwanda ki haqura ki xauna kada ki aure sa hr Allah ya kawo maki wani mijin kirki, amma Assad baxai so ki a Wannan halin ba,
Farah ta qara tsananta kukanta,
Amma naga kinyi period ai kenan Babu tabbacin Kinada ciki ko?
ta girgixa kanta, naje asibiti babu,
Alhamdulillah, qilama babu fyaden sharrin kine kawai dan ki sami Assad,
Farah ta ďago tana kallonta kafin ta maida kanta jikin cinyoyinta batare da tayi magana ba,
Anna ta tashi ta fice Bari Abbanki ya dawo xn sanardashi da wuri yasan halin da kike ciki,
Farah tayi shiru tana kallon xoben hannunta na Assad daya sanyamata,
Idan hasashen Anna ya xamo gsky kenan Assad ďin baya sonta da gaske,
Sunyiwa juna alqawari komai runtsi komai wahala baxasu rabu da juna ba amma meyasa Assad ya fara karya doka, Dan me xai saketa bayan yasan ba laifintabane? ta soma share kwalla, ta xare xoben hannunta ta jefa cikin mirrow, koda sonsa xai illatata ya kashe ta tabbas ta haqura da Assad tunda hr xai iya rubuta mata saki, dama can ya saba gayamata *NI DA KE* bamu dace ba, baxan iya soyayya dakeeeeeeeee ba, Ashe da gske yake ya yaudare tane,
Ta tashi tana kallon kanta ta mirrow ynda ta dawo duk saboda dashi, xata dawo Farah ďinta ta manta dashi, xata yaqi xuciyarta nagani ta cire sonsa a xuciyarta.......
Tun daga lokacin ta soma yaqi ďa xuciyarta akan soyayyar Assad, ta daina xaman kadaici domin shike kawo mata tunaninsa, tana xuwa lectures akoda yaushe, haka tana qoqarin ganin ta cusa wa kanta abinci ko yaya ne dai taci, haka tana walwala sai dai ba Kamar da ba, duk ynda tayi Assad ďinnan na maqalewa dai a xuciyarta.
Abba da Anna sun ga sauyi sosai daga Farah ta soma dawowa kamar da, sunji dadi hankalinsa ya kwanta, ranar da Anna tagayawa Abba halin da Farah ke ciki Kuwa hankalinsa yayi matuqar tashi sosai......
Da sassafe ya shirya ya fito cikin motarta, gateman ya buďe mata gate ďin ta fito kamar daga Sama ta tsinkayo keke napep tayi parking qofar gidansu Assad,
Ummansa taga ta fito daga ciki fuskarta da fara'a yau xata ga Assad ďinta da ta dade bata ganshi ba kuma bata ji muryarsa ba,
Farah na xaune a cikin Mota tana kallon ta, lokacin da take jido kaya daga cikin napep tana ajiyesu a qasa kafin ta ciro kuďi a qaramar Jakarta ta bawa mai napep ya fice kana ta juya ga gidan tana yi masa kallon mamaki yanda ya sauya ya dawo sabo anyi masa fenti mai kyau.........
YOU ARE READING
NI DA KE....
Historical FictionBayan fitarsa Farah ta tashi ta nufi dakinta da sauri tana kallon madubi, Ita baqar mace ce, Assad ma yafita Haske, ita ba ma'abociyar hijab bace sai gyale, haka xalika bata iya xama da Fuska batare da make up ba, tana da kawaici amma bata da haqur...