5 minutes,
Bayan Farfaďowar Anna da Farah, Abba na xaune daga gefe jikinsa sai rawa yake hr lokacin bashida nutsuwa a tare dashi,
Umma na jikin Anna, rungumeta da Ita cikin wani irin farinciki marar misaltuwa, Anna Kuwa sai kuka take, Farah ma na takure gu ďaya tana nata kukan sosai.......
*WAIWAYE ADON TAFIYA* (Abidi & Nusee)
Sama Road Sokoto State~
Alhaji Lawal shine mahaifin Abba da umma, Anna ce mahaifiyarsu,
Mansur shine babba yana da shekara 12 a duniya, sai hafsatu qarama tana da 6 yrs itama,
Soyayya da gata ba Wanda Hafsatu bata gani gun Iyayen Nata duka biyu, soyayyace Mai matuqar wahalar samu a ynxu, ita kaďai mace qarama kuma mai lalurar aljannu Wanda sanadiyarsu sun shanye mata hannu ďaya baya amfanin komai, kanta ma a karkace yake haka bakinta yana xubar da yawu,
Tunda aka haifeta take haka, sai data shekara 3 kafin ta iya xama shima da taimakon Allah da taimakon malamai,
Tana shekara huďu ta soma rarrafe, qafafun kuma ba dai dai ba, batada hayaniya batada rigima, inda kika xaunar da Ita hr kije kidawo baxata taba matsawa daga gurin ba, abincima bata iyaci da kanta sai an bata, tana da 5yrs suka saki qafafunta takanyi tfy sannu sannu shima kai a karkace Sannan hr lokacin bata taba mgn ba, basu taba jin muryarta ba, sautin kukanta ma daban ne, kullum da kalar sa, haka duk kukan da xatayi baxaka ga hawayenta ba,
Tsananin tausayinta ya Sanya soyayyarta a xuciyar iyayenta biyu, duk da lalurarta suna matuqar sonta da kula da ita, basa kyankyaminta ko kaďan sukan sanyata a jikinsu, jininsu ce ita bayanda xasuyi da Ita,
Saboda qaunar da suke nuna mata ya Sanya mansur tsanarta, ganin ita nakasashiya ce amma suke nuna Sunfi sonta akansa, suke bata lokacinsu akanta batare da sun damu dashi ba, ko da yaushe suna tare da ita, yana baqin ciki abokansa su xo suganta tana qanwarsa, yana hantarar ta da nuna mata qiyayya, sai dai tayi ta kallonsa ba bakin mgn
[13/12, 1:01 p.m.] Pherty👯: Asibiti, malamai ba wanda basuyiba sai dai aci kudinsu, duk da haka suna Kan nema mata Magani,Tana da 6yrs ne abin ya soma sauqi, yawun ya daina fitowa amma Kai na karkace da shanyayyen hannunta ďaya, duk wannan qiyayya da mansur ke nuna mata bata taba jin haushinsa, tana sonsa tana son xama dashi amma data kusantoshi xai fara matsawa daga gareta cikin kyankyami yana hantarar ta,
Akwai wani lokaci ta shigo falo ďauke da robar ice cream a ďayan hannunta, shikuma yana xaune yana game, taxo kusa dashi tana nuna masa ice cream ďin alamar ya bata a baki,
Yayi mata banxa haďe da cigaba da abin da yake, fuskarsa a murtuqe, ta qara matsowa robar ta subulce ta faďa masa a jiki ice cream ďin na xube a jikinsa,
Kan...... Ya faďa bayan ya tashi tsaye, yasa hannu ya turata tayi baya ta fadi ragwab, ya soma dukan hannuwanta da remote hrda mai ciwon ma, kuka take ba hawaye a hakan baffa ya shigo ya samesu,
Subhanallah.... Ya fincikosa haďe da ďauke fuskarsa da Mari, ya saki ihu yana tumami, ya ďauki Hafsatu ďin hrta sandare gu ďaya, kumfa na soma fitowa bakinta, sun qara juya Kan Nata, harshenta a waje,
Sosai baffa ya rude ya soma kiran Anna, da sauri ta fito daga kicin, halin da ta sami Hafsatu ta tsorata, ta juya da sauri a ruďe, baffa yabi bayanta, Akan gado suka shimfidar da Ita, maganinta suka ďauko, suna Shafa mata a jiki, Anna na shaqa mata wani a hanci,
Nan da nan jikinta na soma rawa sai karkarwa take, idanunta sun juye wani Kala, haka ma bakinta,
Anna ta dubeshi tana hawaye,
Bata taba irin Wannan abin ba, meya sameta, lfy Muka rabu da Ita a kitchen,Baffa Yace mansur na Sama yana dukanta...
Anna tayi shiru cike da bacin rai tana goge hawayen fuskarta, suka cigaba da Shafa mata magungunanta,
Da kyar da Sudin goshi suka samu suka kwanta bayan sun gama ihu, dama basu mgn su suka riqe mata baki, bayan ta sami barci Anna ta fita tabar baffa da Ita,
Mansur ta Sama yana hawaye batayi wata wata ba ta janyosa tana duka ranta a bace,
Kiyi haquri Anna baxan qara ba itace ta xuba min ice cream a jiki, ta dakata tana kallonsa,
Saboda ice cream sai ka daketa mansur, ba qanwarka bace? Tunda aka haifeta baa taba dukanta ba sai yau Kuma kai, Baka tausayinta baka ganin halin da take cikine? Qanwarka ce fa, kana gudunta, kana tsangwamarta meyasa mansur, jini ďaya fa....
Tor Anna meyasa kuke sonta akaina, meyasa komai takeso kunayi mata,
Saboda lalurarta, mun haifeta baxamu gujeta mu so ka ba, Ka kiyayenifa Wlhy ka qara dukan hafsat a gidannan sai najima rauni sosai, nafi sonta dakai sai me? Kagayamin kai menene baayima a gidannan, wane gata ne Baka samu garemu?
Ya tunxuro bakinsa yana gunguni ya juya ya fice yasa a xuciyarsa dukan da akayimasa Akanta sai ya Rama baxai barta ba, he hate her......
YOU ARE READING
NI DA KE....
Historical FictionBayan fitarsa Farah ta tashi ta nufi dakinta da sauri tana kallon madubi, Ita baqar mace ce, Assad ma yafita Haske, ita ba ma'abociyar hijab bace sai gyale, haka xalika bata iya xama da Fuska batare da make up ba, tana da kawaici amma bata da haqur...