Washe gari da sassafe ya tashi ko wanka baiyi ba ya nufi ďakin ummansa, sun jima tare suna hira kafin ya fito nan sukayi kicibis da suzana ta fito gyara ďakinsa,
Umarni ya bata akan ta kawo masa breakfast ďinsa a ďaki, yaje yayi wanka ya shirya kana ya xauna yayi breakfast, bai bata lokaci sosai ba dan bayason farah ta tashi barci ta samesa, a gurguje yayi Sallama da ummansa ya fito ya sami momi falo da alama tashinta barci kenan,
Morning mom,
Morning, an tashi lfy?
Lfy ya bata amsa yana qoqarin barin gurin,
Inada mgn da Kai Assad, ya juyo a raunane yana kallonta,
Idan na dawo mom, I don't want to be late,
Shikenan Allah ya bada Sa'a,
Amin ya juya ya fice dai dai lokacin Farah ta fito da kayan barci a jikinta,Mom dake dawa ke mgn,
Me kika gani,
Ni muryar Assad naji,
Tor Kodai shi kike mafarki har kike jiyo muryarsa?
Allah mom ni muryarsa naji,
Tace tor ba shi bane, ta juya xata fice,
'mom ki taimaka ki nemomin shi, Abbana ya kasa nemomin shi, Abbana ya batar dashi ynxu ni bansan ko a wane hali yake ciki ba, naga ko ummansa bata damu ba daga ni sai Anna ne kawai,Sosai mom taji tausayin yar'ta, musamman da taga tana hawaye, ta rungumota xuwa jikinta,
Ni nace miki duk inda Assad yake yana qlw, I promise you yau xakiga Assad, da mamaki take kallon mom ďinta,
Kinsan inda yake ne momina?
A'a bansani ba amma xn nemo maki shi, ta saki wani malalacin murmushi tana kallonta,
But...... Shishshsh, is ok farah, Assad kike so I will find him for you, amma in tambayeki,Ask me mother,
What if kin sami Assad baya son ki a ynxu saboda Abinda Abbanki yayi masu,xuciyarta ta shiga bugawa, ta dubeta,
Momy we make a promise nothing will separate us between me and him, ya gayamin *Ni da shi* komai runtsi komai wuya muna tare, unless if he will break our promise......Baki amsamin tambayata ba Farah?
Tayi shiru idanunta cike da kwallah kafin tace,
Xn haqura dashi momi, amma Ina sonsa,Shikenan farah, Allah xai baki wani mijin mai sonki, xo muje taja hannunta, Farah tabita batare da ta fahimce ta ba,sai dai tana matuqar mamakin kalamanta,
Duk Wannan Mgnr da suke akan kunnuwan umma,
Kada dai momi tana son raba auren Farah da Assad ne? tafi kowa sanin son da Farah takeyiwa Assad, idan an rabasu ai an cutar da Farah, itama ai tana da iko akan Farah dan haka baxaa raba auren ba, Bari Assad ďin yaxo....
[22/12, 11:29 a.m.] Pherty🎤👯: *Bayan tafiyar farah sosai Abba ya soma rashin lfy, Anna ce ke kula dashi kullum da irin nasifar da xatayi masa akan rayuwa da ynda ya đauki rayuwa,
Khamis yaxo dubinsa daga nan yabashi invitation na aurensa, tare da neman yafiyarsa idan hr yayi masa laifi,
Sosai Anna yayi nadama Kan abinda ya faru tun daga farkon rayuwarsa yayi kuka sosai Anna ta rarrashesa, yaji baxai iya xama ba hr sai yaje ya nemi umma da momi yabasu haquri,
Shi da Anna suka sa Umar a mota yakaisu qauyensu su umma, acan sukaje suka gabatar da kansu da ynda komai ya faru,
Malam da Inna sun gamsu sai dai sunce hafsatu ďin baya xo ba,
Sosai hankalinsu ya tashi bama kamar Anna Wannan Karon ba umma ba Assad, sai gata a sume Qasa,
Suma Su malam hankalinsu ya qara tashi musamman da sukaji hr jikansu Assad wai ya bata, Abba kuwa kusan ruďewa yayi tamkar wani xararre haka ya koma,
Bayan Farfaďowar Anna yake gayamata xaije Singapore inda momi ya roqeta gafara dan yana ganin haqqintane ke bibiyarsa meyiwuwa idan ta yafe xa'a ga qanwarsa da ďansa Assad,
Anna tace sai muje tare daga nan nagano yar jikata, Allah ka bayyana min Su....
*
Yinin ranar Assad bai dawo gidan ba, yau ma umma da Farah ne suke hira duk akan Anna,Tana son Farah tabata lbrn Anna, she feels happy, tana kewar Anna domin kullum suna tare sunajin daďin kasancewa tare da juna,
Idan Farah ta gayamata wani abin da Anna tayi na tsufa takanyi dariya sosai hrda hawaye,
Farah tace kema umma haka jikokinki xasu sanyaki agaba suna yi maki dariya tunda kikewa Anna,
Tor bara na daina mata dariya tunda bakyaso farah,
Momi na kitchen tana jiyosu sai dai itama tayi dariya,
Lokacin magrib nayi kowa yaje yin sallah, bayan ta kammala ta dawo harabar gidan ta xauna da laptop ďinta a hannu, yau kam sai taga wannan abokin dad ďin da momi tace kullum sai dai taga an fita da motar, a dawo da Ita bataga mai tuqata ba, sai taga malakkin motar ko yayi deserving da hawanta,
Kusan minti talatin da xamanta, taga an hangame gate ďin, shigowar wata baqar Mota ya sanyata bata fuska dan a zatonta Wanda take jirane,
Motar ta shigo tayi parking, Meenah ta fito a fusace ranta a bace idanunta ma xaka kalla ka gane tasha kuka,
Tana tsaye gurin riqe da qugunta motar Assad na sanyo kai, ba alamar damuwa ko bacin rai yayi parking ya fito idanuwansa boye cikin baqin glass, Farah sai qoqarin son ganin fuskarsa takeyi domin ya juya mata baya, haka take ganinsa Kamar Assad, ga mamakinta sai taga budurwar ta xagaya Inda shike,
Baka isa ba Wlhy, kai baka isa ka wulaqantani ba, dan me xakace kana sona bayan kasan kana da wata mata,
Ni nace ina sonki, bayan abota kigayamin na taba furta miki kalmar so?
Wlhy qarya kakeyi, you deceive me, sai nagayawa hajiya sai ka aureni kai ka ďai nakeso, ta soma dukan qirjinsa,
Ya tabe bakinsa kafin ya xare madubin dake idonsa,
Ki shiga taitayinki fa nagaya miki mahaifiyata da matata na gidannan, idan kika kuskura kika Bari ummana taji wai Ina tare dake ranki xai baci,Duk Mgnr da yake farah bata jiyosa kamar ynda take jiyo na Meenah, sabanin shi yana mgn cikin kwanciyar hankali ita Kuwa tana ďaga murya sosai, shi wannan kenan hr gida mata ke biyosa,
Wlhy Wlhy kome xai faru sai dai ya faru, ina ruwana da ummanka ni xn iya gayamata mun dade Muna soyayya, hajiyata shaidace Kuma momi tasan da Mgnr mu, ta juya xata fice yayi Saurin fisgota Wannan Karon Ransa a bace, ta faďo jikinsa cikin tsoron yanayinsa, da yatsa ya nunata alamar gargaďi amma ya kasa ce mata komai,
Juyowar da xaiyi sukayi ido huďu da Farah dake tsaye tana kallonsu, daga shi hr Farah tsananin mamaki da tsoro ya Sanya xukatansu bugawa.....
YOU ARE READING
NI DA KE....
Historical FictionBayan fitarsa Farah ta tashi ta nufi dakinta da sauri tana kallon madubi, Ita baqar mace ce, Assad ma yafita Haske, ita ba ma'abociyar hijab bace sai gyale, haka xalika bata iya xama da Fuska batare da make up ba, tana da kawaici amma bata da haqur...