Lafiya kike kuka, me ya faru?
Kai da kasanyata a gaba kana kallonta me ya faru, ko naquda ce kukayi shiru? Nan ma sukayi shiru sai kukan Farah dake tashi,
Anna ta rarumo mopper tayo kansa,
'yau ga ďan banxa ina magana kayi min shiru, ya kauce yana dariya,Anna aure xaiyi shine yaxo yana gayamin, ki gayamasa ya sallameni baxan iya xama dashi ba,
Murmushi yayi yana Shafa kwantacciyar sumar kanshi, ganin ynda idanuwanta suka juye tana amayarda raďaďin kishin dake xuciyarta,
Anna tayi xuru tana kallonsa,
Waye xai qara aure kai ko mahaifinka,'shine ban sani ba Anna, ki tambayeta waxai qara aure nima bansani ba,
Anna shine xai qara,
Yace ni nayi Mgnr da ke, ni nace xn qara aure kibari karki hadani da Anna yau infasa komawa inda na fito, baki bude farah ke kallonsa da tsananin mamaki,Wallahi Anna haka yace xai auri Hauwa'u, wai sun dade tare shi yana son wadda xata Kula dashi tunda kin riqeni kin hana naje inda yake,
Assad ya matso inda Anna jikinsa na rawa,
Qarya fa takeyi Anna, ni na isa nace kin riqemin mata bagashi ni Ina xuwa ba, haka fa nace Anna ta kyau ta sosai da ta hana maki tafiye tafiye,Saboda tsananin mamaki Farah xuru tayi tana kallonsa baki a buďe,
Anna tace tor koma dai menene ba auren da xaka qara a ynxu, Kuma Farah tana nan sai ta haihu baqin munafi....ya Katse ta
Ballantana ma bnce xnyi ba, ni Ina bata lbrn Umar xai auri Hauwa'u ne, auren su wani sati,
Wannan ma rainin hankali ne Assad ke mata ta bata fuska sosai,
Anna tace Ashe auren umaru yaxo, Allah ya basu xaman lfy, kace Ina nemansa anjima
Anna hrda jabir fa, duk auren su lokaci ďaya ne kinga batun xuwa Singapore bai same ni ba a ynxu, auren abokaina da kuma hauwata ya faďa yana kallon Farah,
Sarai Anna ta gane Assad xolayar farah yake da hauwa,tasa kai ta fice tana fadin kai Kasani dai kai kullum baxaka canxa ba,
Ya juya yana kallon Farah
Duk kin bi kin tada hankalinki, sai kace bakece mai Assad ďin ba, harda kiran in sallameki tor kije Ina farah? Karfa ki manta ubangiji S. W. T cewa yayi ku auri Abinda yayi maku daga ďaya, biyu, uku har xuwa huďu....... tayi Saurin katsesa'Dan Allah ka auri goma idan xaka iya...... sai ga hawaye sharrrrr sai abin ya bashi tsoro naganin ta kasa fahimtar sa, shifa bawai yace xaiyi auren bane, ya dawo gabanta ya tsugunna,
Ni ďin me Farah, kin manta *ni da ke* akwai alqawari tsakanin mu, miye abin kuka aciki daga wasa?
Ta fisge hannunta ta miqe xata fita, ya sha gabanta ya xagayeta da hannuwansa, kallonta yake har cikin ido,
'idan kinga na haďa rayuwa da wata tor sai a aljannah, you are more than enough to me.... And I'm yours! Ya qara rungumeta, *ni da ke* har abada sai yar tsohuwa Anna,
Tayi murmushi Wanda ya fito daga qarqashin xuciyarta, qaunar mijinta ta qara kwanciya cikin ranta kamar ta haďiye shi dan so da qauna, sai itama ta rungumeshi sosai, ya sakar mata murmushi yana jin sonta ta ko ina a jikinsa.
*Sai shirye shiryen biki ake, sosai Assad ya taka rawa gurin ganin bikin ya qayatu na abokansa biyu, yanda suka rufa masa asiri a auren da Farah haka shima yayi gwargwadon qarfinsa na basu tashi gudumuwar,
Alhamdulillah kuma Anyi biki lafiya sai fatan Allah ya basu xaman lafiya Amin.
Sati biyu da bikin farah ta haifi sankacecen yaronta tubarakalla sak mahaifin Assad, yaron ma yafi Assad kyau,
YOU ARE READING
NI DA KE....
Historical FictionBayan fitarsa Farah ta tashi ta nufi dakinta da sauri tana kallon madubi, Ita baqar mace ce, Assad ma yafita Haske, ita ba ma'abociyar hijab bace sai gyale, haka xalika bata iya xama da Fuska batare da make up ba, tana da kawaici amma bata da haqur...