81

1K 58 0
                                    

Bayan sun gama breakfast ta shirya ta nufi inda umma, da sallamarta ta shiga,shiru ba amsa ta nufi cikin ďakinta tasameta tana haďa kayanta a qaramar trolley,

Umma Ina xakije haka? ta ďan yi Jim kafin tace tafiya xanyi,

Farah ta xauna tana kallonta,
Nima umma xnyi tafiya xnje Singapore Gobe,

Singapore Kuma, inda wa? Umma ta tambayeta tana kallonta fuskarta da alamar tambaya,

Xnje inda momina, Anna ta amince inje amma Abba bai amince min ba,

Nima ban amince maki ba,
Meyasa umma? Mahaifiyatace fa, tana fushi dani sosai saboda nadaina xuwa na ganta,

Inaso ne ki xauna dani, kiyi haquri ki xauna karki tafi,

Amma umma naga kema tafiyar xakiyi fa,

Shikenan na fasa tafiyar, mu xauna jiran Assad Ina yawan mafarki dashi ya kusa dawowa,

Jin ta ambaci Assad yasa taji wani iri har take ganin baxata iya tafiyar ba har sai Assad ďin ya dawo,

Shikenan umma xn xauna har wani lokaci, amma ki gayamin kin haqura xaki barni dashi?

Umma tayi shiru tana kallonta, yanda ta dauko farah ba haka take ba xaman da sukayi da Ita ta fahimci halayarta, Sannan ko ba komai itama yar'ta ce ai,

Kinyi shiru umma, ta Katse ta,

Allah ya dawo dashi lfy farah, Assad yayanki ne ai,
Tayi murmushi tana kallonta, umma Saura Abba, ki yafe masa, Abba bashida kwanciyar hankali, Abbana ko barci baya yi saboda ke da Assad da momina, ya daina fita aiki kullum yana ďaki, ki yafe masa,

Umma ta rufe trolley ďin bayan ta tashi, ta dubi Farah,

Anjima xaki rakani gidan Su Umar Inaso na duba mahaifiyarsa da bata lfy,

Shikenan umma.
.
[20/12, 9:57 p.m.] Pherty👯: Singapore.......

Fari ďan sirdidi Mai kyakkyawan jikin dake lamushe shekaru batare daya nuna ba, sanye yake cikin jacket da wando baqaqe yan gidan (Hilfiger),

Tsaye yayi jikin motarsa Ford Mustang, yana kallon Meenah  ta cikin glasses ďin idonsa farare sol, magiya take masa akan ya karbi soyayyarta, mamanta qawar maman farah ce, a Skul suka fara haďuwa,

Tun lokacin da take tsaye gurin tana surutunta komai bai ce da Ita bayan idanu daya xuba mata, yana so ya gano illarta yaga meta rasa daya kasa karban soyayyarta, BABU wata xuciyar tace dashi, domin komai daya keso daga mace tana dashi,  matsalar ďaya ce bata da kamun kai,

Assad...... ta kirasa da wata murya Mai wuyar fassaruwa,  ya ďauke kansa gefe tamkar baiji ba yana kallon agogon hannunsa,

We talk later Meenah, xai shiga motar ta riqa hannunsa,

What do you mean Assad? Miye laifina dan nace ina sonka, meyasa kake wulaqantani?

Nace xamuyi Mgnr anjima, idan bamu haďu a skul ba xn same ki gida,

You promise...... Promise ya katseta, ta gyada Kai tana murmushi, ya ďaga mata hannu ya juya ya shiga motar sa, tana tsaye hr ya fice kafin ta shiga tata motar......

Doguwar  tfy yayi kafin ya qaraso gidan flat house Mai matuqar kyau da birgewa, bayan an bude masa gate ďin ya shiga yayi parking inda ya saba ajiye motarsa ya fito yana tafe yana cilla makullin motar yana cafewa hr ya qarasa falon,

Wata baturiya Mai aikin gidan ya Sama tana goge gogen ta, tana ganinsa ta gaidasa ,ya amsa bayan ya xauna da remote a hannunsa,

Hajiya Maryam ta shigo jin tsayuwar motarsa, tasha kwalliya cikin sassarqar shadda ďinkin yan Senegal jikinta na fitar da wani irin sihirtaccen qamshi, tun da tashigo yake kallonta har taxo ta xauna,

Wannan kyakyawar bafullatanar mace bata tsufa, ga kyakyawar xuciya da fawwala  al'amura ga ubangiji, komai na duniya baya gabanta yafi kowa sanin kirkinta tun lokacin da ta daukoshi taxo dashi nan gidan mijinta ta maidashi tamkar yaron cikinta,tace shi jinin yar'ta ne farah, duk abinda xata iyawa farah xata mishi, ba irin gatan da bata mishi, mota ba irin wacce baya hawa sai idan babuta a gidan, ynxu ma Mgnr da ake tasanya mijinta ya nema masa aiki a garin saboda ya cigaba da xama da Ita, ya sauko yana gaidata,

Ta amsa bayan ta xauna tana kallonsa,
Anya Assad daga Skul kake Kuwa?
Me kika gani Momy?
Naganka ba yanda nasaba ganin ka dawo ba, menene lokaci ynxu,

Ya duba time yana kame kame,
'Momy daga Skul nake fa, ynxu ma.....
'Time na tambayeka ai,
'11:30am,
'Gud, qarfe nawa ka saba dawowa gida,
'2pm
'me ya dawo dakai ynxu?
'Uhm Momy... dama... nifa abu naxo ďauka ynxu xn fice ya tashi ya nufi hanyar ďakinsa, tabisa da kallo tana girgixa kanta, bai jima ba ya fito,

Tana nan inda yabarta xaune,
Sai na dawo,
A dawo lfy,
Yasa kai ya fice batare da yaso ba, saboda gajiya ya dawo, ga mata dake damunsa, ya shiga motar ya fita daga harabar gidan, wata inuwa ya samu yayi parking haďe da ciro wayarsa ya kira ummansa,

Tana ďauka ta soma mgn,
Yaushe xnxo naganka Assad hrna haďa kayana,

Jibi ne umma, Inace Umar ya gama komai na tafowarki?

Duk ya gama,

Farah fa umma, kina Kula da Ita,
Farah kake tmbyata Kuma Assad,
Eh umma, ba Wanda yayi maki bayanin komai dake tsakaninmu,

Anyi min, wai matarkace, Sannan abbanta shine yayana mansur,

What.... ya tashi xaune daga kishingide da yake,
Anya umma an gayamiki gsky Kuwa, taya abbanta xai xama yayanki, bn fahimceki ba kina nufin Kice Anna mahaifiyarkice Kece yar'ta data bata,

Kwarai Kuwa, Xnma Qarya ne, ni bansan mahaifiyata bane ko itace bata sanni ba,

Ba Mgnr waya bace umma, ya tsinke Wayar bayan ya fito daga motarsa, kamar wani xautacce haka ya koma,

Abban Farah, Abban Farah, yes biri yayi Kama da Mai, sunansa mansur, ďabiunsa sak ynda umma tabashi labari, baya son ummana, baya son babana, nima baya sona, ni Kuma meyasa xn so yar'sa? Should I divorce her or what? Yesss Yesss, shi kaďai xaiyi ya rama abinda mahaifinta nayi masu,

Wannan rayuwar daya ke ciki a ynxu tafi komai dadi, tun da baya neman komai a rayuwa,itace isolated life ďinsa, baya cikin qunci da baqin cikin Alhaji mansur shiyasa yake son ďauko ummansa ya dawo da Ita nan su xauna kamar ynda Momi ta buqata,

Kenan momin ma batasan ummanshi ne qanwar Abba na,

Ya xauna yana tunano rayuwarsa tun yana qarami, wahalar da yasha da Abban Farah, ynda mahaifinsa ma ya wahala dashi hr mutuwarsa, rayuwarsa da Farah da ynda yakeshan duka Akanta gurin Abba, momi na karesa, ya tuna lbrn da ummansa ta bashi na game da mansur, sai ya tsinci kansa cikin hawaye,

Hankici yasa ya ďauke hawayen dana xubo masa a idanuwansa yana Mai tausayin kansa dana ummansa,  ya girgixa kansa bayan ya tashi yana fadin impossible..........

NI DA KE.... Where stories live. Discover now