Umma ta soma faďa Kamar gske dole suka tashi ganin da gske takeyi,
Assad ma ficewarsa yayi daga gidan ya koma skul, Abba kuwa bayan komai ya lafa yaje ya nemi masauki a hotel,
Umma tace Anna a ďakinta xata xauna farah tace itama a ďakinta Anna xata xauna, Anna Kuwa tafison xama kusa da yar'ta a ynxu,
Kwana biyu ba abinda ya sauya daga Assad da farah, Iyayen sun xuba masu ido suga iya gudun ruwansu musamman ynxu da suka ga kowane na fushi da ďan uwansa,
A daren ranar yana xaune ďakinsa da tulin takardu a gabansa amma hankalinsa na ďakin umma inda yake jiyo muryar Anna da Farah suna hira da dariya, mom Kuwa daddy ya dawo daga tafiyarsa tana can,
Ya tarkata takardunsa ya tashi ya nufi ďakin Farah, sai ya sami kansa da xama a dakin dan kawai ya ganta shi ya gaji da wannan fushin nata duk akan mace, macen ma da ba sonta yakeyi ba inda ma Hauwa'u ce,
daga shi sai singlet da wandon shan iska, short niker) yana duba Wayar hannunsa, amma a xahiri hankalinsa baya kai yana Kan qofar dakin,
Da an ďan jima sai ya dubi qofar dakin ko xata shigo amma shiru, shi kansa ya kasa gane kansa a kwanakinnan, matarsa yakeji sosai cikin xuciyarsa,
Can sai gata ta shigo riqe da kofin tangaran coffee ne aciki, batayi mamakin ganinsa ba dan taga gilmawarsa lokacin da xai shigo,
Ya ďaga shanyayyun idanunshi a hankali yana kallonta,
Kallo ďaya tayi mashi ta Kau da kai, don taji kunyarsa, bata taba ganin namiji haka ba, ta ajiye coffee ďin akan mirrow ďin ta shiga toilet, bata jima ba ta fito idanunta akan sa ya rausayar da kai gefe ya lumshe Idanunsa kafin ya budesu akanta tayi Saurin kawar da kanta,
Malam ka tashi xn rufe dakina, yayi shiru tamkar badashi take mgnr ba,
taje qofar dakin tayi tsaye tana fadin,
Inace Kai ba kurma bane, kai nake jira xn rufe dakina, nan ma shiru bashida alamar tashi,Ta ďago a fusacce ta dube shi, abinda ta gani kwayar idonsa ya sanyata kokonto Anya Assad ne, kwayar idanunshi ta nuna wani mutum dake axabtuwa da soyayya, yet he's not weak, amma kamar ba shi ba
Sai itama tayi cooling, gwiwoyinta sun sage, tana jin sonsa ta ko ina, cikin murya qasa qasa tace,
Ni inajin barci, xn rufe ďakin, sai alokacin yayi mgn,
Kixo kiyi kwanciyar ki na hanaki ne,
Tace amma.... Sai Kuma tayi shiru,
Amma me? Ya tambayeta yana kallonta, ya matsa kaďan yana fadin kixo ki kwanta ni ynxu tfy xnyi, ba musu taxo xata kwanta anan ya riqe hannuwanta,Kin cnxa farah, anya kina sona a ynxu? tayi shiru tana qoqarin xame hannunta,
Kinata fushi kinata fushi without any reason, Meenah ďin da kike mawa bafa son ta nakeyi ba kuma bawai nace xn aure ta bane, wannan abin da kike min kina nuna min halin ko in kula Acikin mutane bakya tunanin na cnxa mind ďina akan Meenah dake sona,
Batayi mgn ba amma xuciyarta sanyi take, haka fuskarta ta nuna sassauci, soyayyar mijinta na kutsawa hr cikin bargo da qasusuwanta, sai ta sunkuyar da kanta ta kasa haďa ido da Assad dake kallon yanayinta, yana binta da ido da xuciya yana karantar weakness ďinta, tana da boye soyayya da Jan aji sai dai batada juriya a fannin soyayya Abinda ya fahimta kenan, can qasan maqoshinta yaji tana fadin,
tor kayi haquri nadaina..... Murmushi yayi hr cikin ransa yaji daďi,
Na haqura malamataaa.... Jin ya ambaci malamata ya sanyata kallonsa tana murmushi rabon da taji wannan sunan hrta manta ta xame hannunta ta raba ta gefensa ta kwanta haďe da juya masa baya,Wancan coffee ďin da kika ajiye baxaki sha bane,
Tsohuwa ta haďa abinta ba daďi,
Kuma kika rabata da kayanta, tayi shiru,
Yace goodnight,
Night ta faďa a hankali, ya kwanto ta jikinta,
Night kawai, nothing more? ta rumtse idanuwanta,
Yace matsamin anan xn kwanta yau,
Xumbur ta tashi xaune tana kallonsa,
Ka rufamin asiri kada mom ko umma su ganka,
Tor miye aciki tunda ke matata ce, tayi rau da idanu Kamar xatayi kuka,
Dan Allah kayi haquri ka tafi,
'OK kiss me before I go..... tayi far da idanunta haďe da xumburo bakinta,
Shikenan matsamin ya soma gyara kwanciyarsa,
'tor ka tsaya mana, ya tsaya,
Close your eyes, yace baxai rufe ba, ta matsa sai ya rufe idanunsa shi Kuma ya kafe akan baxai rufe ba sai dai ya kwana anan, ganin xai bata mata lokaci ta rufe nata idanun ta sumbace sa a goshi, not like this farah, ya janyota sosai jikinsa ya soma kissing ďinta........... sai da tayi da gaske ganin ya soma fita hayyacinsa kafin ta samu ya saketa, daga ita hr shi bamai kwarin jiki bama kamarshi da Idanunsa sunyi jawur,Ya kwantar da Ita ya lulluba mata blanket haďe da qara sumbatar ta, tana kallonsa ya juya ya fice daga ďakin,
Shower yaje ya sakarwa kansa, sannan ya fito ya shirya cikin kayan barcinsa ya kwanta cike da tunanin farah iri iri.
Washe gari da kansa yaje ya sami mom Akan abashi matarsa xasu koma gida Nigeria, ta dan dubesa hr a Ranta taji daďi,
Bn fahimceka ba, ya Sosa kansa, matata xa'a bani mom, ba amfanin xaman mu anan mom,
Idan ka koma Nigeria Skul ďin fa,
Itama Farah Skul ďin ta fa mom?
Farah is about to finish am talking about yours,
Yayi shiru,
Anan xaku xauna, Abban Farah shine uba agareka, Duk wani responsibility naka shine, shi xai siyamaku gida anan ku cigaba da xama hr ka gama Skul,A'ah umma, hr yaushe xai nema mana gidan, xamuyi ta xaman jiransa anan ne,
toh fa, yau dame ka tashi Assad, tunda kuke xama cikin gidannan baku qosa da barinsa ba sai yau,
Yayi shiru,
Ni saboda makarantar ka ne nakeso ku xauna anan garin, sannan Abban Farah yace baxata tare ba hr sai anyi maku bikin tarewa dama can ďaurin auren ne kawai babu biki,Yace shikenan, ya tashi ya fita ta bisa da kallo ko rawar jikin me yake a ynxu, koma dai menene taji daďi,.....
Kwana biyu aka sanya bikin tarewarsu, Abba da kansa yaje yaxo dasu malam da Inna, mutane, Umar da Dama an gayyata a ranar, dangi ma sunxo yan uwa da abokan arxiki ma sun xo, Ummy Aysher, Faxyfashion, Xuhura Ajiya, Rabi'atu Sk Mhs, Kausar, Serdiyer, Xarah dange, Baby Bello, Miss Aysher da Halimcy,
ďayan bangaren gasu hauwa tahir, Nuceey, Anee, Sumy Qasarawa, Ummy Uduth,xee yabour, Mmn Boy, Sally, fauxie, Anty Sis, hafsat Rano, Lilmeerahcute, leemcy, Hawy, pharty bb, Xarah Bukar, Nafee Anka,Ayusha, miemiebee, sa'adatu nahuche, Aneesa Didi, maryama kangiwa, Faree, Fatima mungono, Al'eeman, E. T. C tsaya lissafo mutanen danaje bikin page ďin xai cika batare dana gama ba,
Mom ce tsaye Kan komai sai shirye shiryen gurin suke itada umma da sauran abokan mom na garin, hrda Meenah an xo sai neman Assad take ko ya xa'a kwashe🤔,
Amarya farah tayi matuqar kyau sai kyalli take tamkar wata sarauniya, kalar fatar jikinta Mai kyau da sheqi sai ma kayi xaton ita farar mace ce, tayi kyau sosai cikin wata farar gown, an yane kanta da wani qaramin net shima fari, komai in white daga cikinta hr waje, tayi matuqar kyau sosai,
Yayin da ango ke sanye cikin wani lallausan yadi Mai shara shara fari sol har kana iya hango vest dinshi da manyan damatsanshi masu nuni da alamun Karfi da cikakkiyar lafiya da mazantaka ta ko'ina,
Kallon yadin kaďai ya isheka kimanta tsadarshi, anko ne sukayi da Abba, malam da daddy, suma Su Anna, Inna, mom da umma sukayi nasu anko na wani blue lace Mai kyau da tsada,
Kallo ďaya xakayi wa Assad ka sake marmarin kallonsa saboda Haske da kwarjininsa ya dushe hasken Duk wani matashi Mai ji da kansa Dake harabar gidan,
Dangi yan uwa da abokan arxiki sun matsu suga ango da amarya, kowa idanunsa na kan qofar da xasu fito,
Yana riqe da hannun santaleliyar matarsa suka fito duk idanu akansu, da yawa friends ďinsa na garin da basu santaba yau sun ganta sun yaba sunyi tofin albarka, sosai Meenah ta bata fuska bayan ta tashi tsaye,
Wow classy wife.... inji _fertymerh Xarah novels_,
Perfect match... inji _Pherty novels_,
Classique....inji _Big fans of Pherty._
YOU ARE READING
NI DA KE....
Historical FictionBayan fitarsa Farah ta tashi ta nufi dakinta da sauri tana kallon madubi, Ita baqar mace ce, Assad ma yafita Haske, ita ba ma'abociyar hijab bace sai gyale, haka xalika bata iya xama da Fuska batare da make up ba, tana da kawaici amma bata da haqur...