74

1K 66 0
                                    

Ta soma murmushi tana kallon gidan ya birgeta sosai, ko Ina Assad ya sami kuďi yayi gyaran gidan domin yayi mata baxata, sai ta tsinci kanta da sanya masa albarka,

Tayi amfani da key ďin dake hannunta ta buďe gidan ta shiga, yaran dake Unguwar Su suka Kama mata ta shigar da sauran kayanta a cikin gida,ta juyo tana kallonsu da murmushi,

Ina autana Assad ina yaje,

ďayan Yace mu bamu sani ba mundaina ganinsa,

Tace tor shikenan, ku nemo minshi kuce masa yaxo ummansa ta dawo, yaran suka fice da gudu xuwa neman Assad,

Harabar gidan take kallo sosai, yanda yayi kyau ya tsaru ta shiga sashenta komai Alhamdulillah an gyara sai dai qura da gidan yayi, tor Kodai Assad ďin baya xama a gidan ne? Hankalinta bai taba bata taje sashensa ta duba ba, sai ta soma gyaran gidan cikin lokaci qanqani.

Farah Kuwa hankalinta yayi matuqar tashi da ganin dawowar umman Assad, sai taji ta kasa driving baxata iya xuwa Skul ďin batayi Rivas ta koma cikin gidan, da gudu ta fito ya nufi cikin gidan tun a falo take kwalawa Anna kira,

Anna..... Anna...
Anna ta fito tana fadin, ke lfy menene wannan kiran haka?

Umman Assad ce naga ta dawo, sai da gaban Anna na fadi amma sai ta nuna ko a jikinta,

Tor menene meya faru dan ta dawo,

Idanun Farah suka kawo kwalla,
Anna Assad, me xaki gayamata,

Kajimin yar banxar yarinya, ni na batar da Assad ďin ne kome? Waya sani ko yaje ya buya wani gu ne saboda ya rabu da aurenki shi macuci, nifa haďa aurenku shine *Babban kuskuren dana tafka*(Rash Kardam), dan danasan shi mayaudari ne baxan barki auren sa ba, amma Alhamdulillah da Allah ya nuna mana halinsa tun baki tare ba, nifa ynxu na tsanesa,

Farah tayi shiru cikin qunar xucci, hawaye sai xuba suke a idanuwanta,

Anna ta sauko tana fadin ni xn jira mahaifiyarsa ingani xataxo tambayata Assad ne tunda da xataje qauyensu tabani ajiyarsa ne.

Shiru shiru kusan Awa huďu fa dawowarta ba Assad ba labarinsa, Gashi hr ta gama gyaran gidan tsab bai dawo ba,

Taje sashen sa a rufe yake, ta window ta leqa falonsa, sabbin kujeru tagani masu kyau da tsada, hankalinta yayi matuqar tashi da gani tsarin falon kamar mai sabuwar amarya, komai mai kyau da tsada ne a falon,

Meke faruwa? Ina Assad ko ya siyarda gidan ne shiyasa taji yaran na fadin sun daina ganinsa,

Noo Assad baxai mata haka ba, saboda yafi kowa sanin gidansa ne na gado a gun mahaifinsa baxai siyarda shi ba, sai idan aure xaiyi,

Tana tsaye gun sai ga Umar ya shigo a hanxarce,
Ina wuni umma Ashe kin dawo?

Assad fa Umar ina yaje,

Umma Kibari ki huta tukunna mayi mgn, komai nason natsuwa, tana jin haka tasan ba lfy hankalinta ya qara tashi,

Wace nutsuwa kuma Umar, hr xn iya samun nutsuwa batare danaji halin da yarona yake ciki ba
[04/12, 9:53 p.m.] Pherty👯: Kagayamin Ina Assad ďina, meke faruwa?

Xn gayamiki komai umma amma sai kinmin alqawarin baxaki tayarda hankalinki ba,

Assad ya mutu ne Umar?

Shine ban sani ba umma, Allah ne masanin gaibu idan Assad na raye ko a mace(nan ya gayamata komai)

Kuka take sosai jikinta na rawa, tsayuwa na neman gagararta Sannan ta kasa xama,

tunda shi ba kowa bane ba ďan kowa ba, ba Wanda ya damu da ya nemi halin da yake ciki,na tabbata sace min yaro akayi saboda wannan yar'tasu,

Umma naji kamar ance ya aiko takardar saki ya bata, idan basun boye sa ba ina suka sami takardar? Sun sa ya saketa ne dan kawai su aura mata khamis, duk Unguwar nan Mgnr ake kowa yasan an cutar da Assad,

NI DA KE.... Donde viven las historias. Descúbrelo ahora