🤳🏻
🖤💘 нalιn dana ѕнιga...💘🖤
© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ
w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984
*S͢A͢D͢A͢U͢K͢A͢R͢ WA G͢A͢R͢E͢K͢U*...
*ᴷᴴᴬᴰᴵᶻᴬ ᵁˢᴹᴬᴺ*
*ᴺᴬᴮᴵᴸᴬ ˢᵁᴸᴬᴵᴹᴬᴺ*
*Ɗᴬᴵᵞᵞᴵᴮᴬ ᴵᴰᴿᴵˢ*
*ᴴᴬᵁᵂᴬ ᴬᴸᴵᵞᵁ ᴿᴬᴮᴬᴴ*
*ᶠᴬᵁᶻᴵᵞᵞᴬ ᴰᴬᵁᴰᴬ*💘 2 💘
بسم ا للةالر حمن الر حم
Da daddare muna cin abinci afalo tare da Farida, Mami tayi baƙi suna ɗakinta,wayata tana gefe ta fara tsuwwa na duba naga baƙuwar lamba,ban ɗauka ba naci gaba da cin abincina,Farida tace bai kamata ki ƙyale ba,nace bansan ko waye ba barta kawai, kiran ya yanke...
Lokaci kaɗan aka sake kira Farida tayi saurin ɗauka ta amsa da sallama, naji tace ba ita bace bari abata, ina harararta tasamin wayar a kunne tana dariya, waye?
Na tambaya muryata adaƙile, yi haƙuri ba abin faɗa bane, na ƙara ɗaure fuska jin muryar namiji, kina saurarena? Na amsa da ummm yi maganarka...
Ya yi ɗan shiru can ya nisa yace " da fatan ba zaki damu ba"?
Nace inba abin damuwar zaka faɗa min ba, ya yi ƴar dariya da faɗin Asiyah kenan yaci gaba da cewa, da yamma muna tare da yayanki Hashim anan ƙofar gidanku na rako abokina wajenshi, kwatsam Allah ya nuna mani ke, wallahi ina ganinki Asiyah zuciyata ta harba nan take na amince wa zuciyata ina sonki so mai ƙarfi...
Yai shiru kaɗan, me kika ce Asiyah?
Zan iya zuwa mu gana?
Abinda ya ɗanja hankalina gareshi jin muryanshi ba yarinta, haka nan kalamanshi babu wasa, duk da cewa bawai na amunta da kalaman nashi bane sai naji ina son ganin nashi koda kuwa ban bashi fuskar yin wata mu'amula ba.
Kinyi shiru Asiyah me kike gani game dani?
A yanzu dai bani da lokaci...ya tare ni ba lallai sai yau ba, zuwa gobe ma in kina so ina iya zuwa, na ɗan yatsina fuska tamkar agabanshi nake nace sai ka zo ɗin, ban ƙara sauraren shi ba na kashe wayar.
Farida data zuba mun ido cikin mamaki da al'ajabina tace Allah ya kyauta, wannan hasken fatar taki da kyan fuska dana jiki ke ruɗarki kina wulaƙanta bayin Allah, Allah ya rufa asiri da ya yi ki doguwar mace da an bani, ki dai yi ahankali akwai ranar dana sani...
Washe gari na dawo makaranta na iske baƙona yana jirana, muka gaisa amutunce dan sanin abokin ɗan'uwana ne, gani nazo Asiyah, na kalleshi na gane maganarshi, kyakkyawane dan jiya ban wani tsaya na kallesu ba sai yaune na laƙanci kamanninshi.
Wankan tarwaɗa ne yana da dogon hanci da idanuwa masu girma a fuskarshi ya bar gashi ya kewaye fuskar da ƙasan hancinshi.
Ya gari? Na ɗanyi murmushi yana wajanku, ko amma dai da zakiyi adalci sai kice yana wajanku ƴan mata nace uhm kawai..
Nan ya hau zuba yace wannan yace wancan, ni dai da Allah yayini ba mai magana ba jinshi kawai nake ina gyada kai, tsayin lokaci mukai sallama bayan na nuna mashi buƙatata tason shiga gida.
Mun rabu ba tare da samun wani gamsasshen bayani daga gareni ba, ni kaina bansan ame na ɗaukeshi ba, nasan dai araina bana ƙinshi kawai.
Kullum da yamma Nura kan zama abokin hirata, tun bana iya sake mashi muyi magana harta kaiga yawan zuwanshi gareni ya sani soma jinshi ajikina, sai dai ba wai sonshi naji inayi ba, a'a mun dai yi sabone mai ƙarfi har ina rayawa araina zan iya zaman aure dashi in halin hakan ya yiwu.
YOU ARE READING
HALIN DANA SHIGA...
Non-FictionKashi 80% labarin gaskiya sai kun nitsa ciki zaku gane inda ya nufa...