🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳
нalιn dana ѕнιga...
🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳~Labarin gaske ne~
© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ
w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984
*_Not edited_*
🕳 *33* 🕳
بسم الله الرحمن الر حيم
Kwananmu biyar da aure zuwa wannan lokacin na gane kuskurena na kiranshi Yaro ƙarami domin kuwa takowane fanni ya nuna mani yaron ne amma da aƙidar manya, naji jiki har wata ƴar rama na soma yi ta fargaba.
Shirya kayana nake cikin ɗan madai-daicin akwati na lefena, na gama sanya duk wani abu dana san zan buƙata na rufe na saukeshi ƙasa, daga nan wanka na faɗa na fito na shirya cikin riga da zani na wata Holland yellow da ratsin kore ajiki, na ɗauko babban gyale shima kore da takalmi na aje gefe , na zauna bakin gado ina jiran Labid ya dawo daga gidan yayanshi ɗauko mota, domin wai ƙauye zamu wajen mahaifiyarshi naga danginshi suma su ganni.
Babu wani ɓacin rai a tare dani dan zani ƙauye danni tun asalina rayuwar mutanen ƙauye tana birgeni domin akwaisu da zumunci da kuma kara, zaman minti ashirin nayi sai gashi ya shigo yana faɗin na taso mu wuje kafin rana ta ƙarayi, ya ɗaukar mani akwatina ya fice zuwa mota, sai da na tabbatar da na kulle ko ina sannan na fita muka wuce.
Ana kiran sallar magriba muka shiga cikin garin, inata ware ido naga ƙauyen ƙayau sai naga ashe babban ƙauye ne domin local gov't guda ne, ƙauye ne babba da tarin jama'a acikinshi, n gyara zama ina kallon garin har muka iso wani layi mai jar ƙasa ya shiga akan gida na biyu naga yayi fakin motar.
Gida ne gunin sumunti da fenti ruwan madara, akwai ƙatuwar baranda daga wajen gidan shafe da sumunti sai ƙaramar ƙofar da zata sadaka da zauren gidan sannan ka shige babban tsakar gida da tarin ƙofofin ɗakuna irin tsarin ginin karkara dai.
Hayaniya ce tako ina cikin gidan ta yara da manya, aka hau yi mana barka da zuwa har falon mahaifiyar tashi, falon yasha saitin kujeru masu ruwan ƙasa sai tails ƙasan falon an malala kafet samanshi, sai kuma tv ƙarama da madubin gado afalon, babu laifi arayuwa irinta karkara yayi kyau.
Kafin ƙanƙanin lokacin anyi dafifi cikin falon ana zuwa kallon amaryar Labid, duk wanda ya kallan muka gaisa saiya riƙe baki yana faɗin masha Allah, Labid wannan bafullatanan mata taka haka kyakkyawa inaka samota?
Ins jin sanda yake maida ma wasu amsar toh kada dai kusa kanta ya yi ƙato tayi tunanin kyawon nata ya shahara ne, wata daga cikinsu tace kai ja can shiyasa ashe ka kwanta ciwo kamar zaka mutu ka gano kyakkyawar mace duk ka ruɗe mana ciwon zuciya zai kamaka, ya yi dariya yana faɗin to ku ton mun asiri kuja ta rainani, ayadda suke taƙalar juna na fahimci abokan wasanshi ne.
Sai can bayan isha'i mutane suka tsagaita sannan ne muka samu gaisawa da mahaifiyar tashi, kallo guda naima mahaifiyar tashi na gane inda ya samo baƙi da siranta, sai dai ga fuska ko alama basu kamanni danyafita kyau nesa ba kusa ba.
Duka ni da ita kunyar juna muke ji, dan tun gaisuwa babu maganar data sake haɗamu, sai dai ina kallonta tana satar kallona , ko mamaki take ya akai na auri ɗanta oho.
Ya shigo falon da sallama ya zauna kusa da mahifiyar tashi suna ƙara gaisawa, sannan yace mata Mama bari mu ƙarasa can gidan Yaya sai gobe afara kaita taga dangi ko? Tace toh abinci ba ba zakuci bane, ya matso wajen wasu kululi guda biyu da aka aje mani tun ɗazu ya buɗe.
Tuwo ne na dawa baƙiƙƙirin dashi sai miyar kuka datasha manshanu, yayi saurin rufe kular yana faɗin nikam dai bana ci bansan Asiyah ba, Mama babu fura ne?
YOU ARE READING
HALIN DANA SHIGA...
Non-FictionKashi 80% labarin gaskiya sai kun nitsa ciki zaku gane inda ya nufa...