page 3

191 13 0
                                    

🤳🏻

🖤💘 нalιn dana ѕнιga...💘🖤

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984



*S͢A͢D͢A͢U͢K͢A͢R͢ WA G͢A͢R͢E͢K͢U*...

*ᴷᴴᴬᴰᴵᶻᴬ ᵁˢᴹᴬᴺ*
*ᴺᴬᴮᴵᴸᴬ ˢᵁᴸᴬᴵᴹᴬᴺ*
*Ɗᴬᴵᵞᵞᴵᴮᴬ ᴵᴰᴿᴵˢ*
*ᴴᴬᵁᵂᴬ ᴬᴸᴵᵞᵁ ᴿᴬᴮᴬᴴ*
*ᶠᴬᵁᶻᴵᵞᵞᴬ ᴰᴬᵁᴰᴬ*


💘 3 💘


بسم اللة الرحمن الر  حيم




*December 2003*

   Na dawo gida agajiye liƙis sakamakon tafiyan ƙasa da na sha, dan yau banje da mota ba, Abdul ya fita da ita ni kuma ban jira ya dawo ba na tafi dan kar na makara gashi muna da jarabawa.

Mami dasu Abbas afalo nai masu sannu da gida na wuce ɗaki na aje takarduna na shiga kitchen na ɗebo abinci na dawo falon kusa da Mami na zauna ina ci, na kusa cinyewa Abdul ya dawo ya miƙo mani makullan motata na amsa ina faɗin an shanye min mai ko?

Ya yi dariya yace "mune mai fa Asiyah", Mami tai dariya tace aifa mai aiki a Refinary har anyi mashi gorin mai, nayi dariya Mami ahaka dai kullum sai su adana nasu motocin alallaɓo ma tawa sai an ƙarar da mai azo a aje babu bayani sai na tashi naga babu komai...

A yau dai anyi maki abin arziki danna cika maki tanki, cewar Abdul, na harareshi, Allah ba wasa ba tambayi Abbas, na kalli Abbas dake gefenmu yana amsa waya, zanyi magana ya ɗaga min hannu karma na dameshi kenan...

Nayi dariya nace, da kuna irin haka ai kullum aron mota ba musu, yayi dariya ke ko da son kuɗinki, in an baki kuɗin man saiki ta tarawa ko?

Ai Asiyah akwai shegen son kuɗi, Bashar daya shigo ya tsinci maganar daga sama ya faɗa, su Mami sukayi dariya ni dai bance komai ba dan ina magana zai taso mani kamar zai cinyeni.



Da yamma nai wanka na shirya abina cikin ƙaramar Tshet fara, rigar ta kama jikina ainun hakanan baƙin siket ɗin dana sa shima ya matseni tsantsan, ni arayuwata haka nake son ganin duk kayan da zan sa sun kamani, na ɗora ƙaramin gyale bisa kaina zuwa ƙirjina.

Na fito na leƙa Mami ina faɗin zanje gidan Anty Lubah, tace to Farida ma na can...

Kamin na wuce gidan Anty Luban sai da na tsaya wani Business center dake nan kusa damu na siya kati ina sama wayata...

Ina tsaye gun muna magana da wata maƙociyarmu Saratu, muna magana game da ɗinkunan dana ba yayarta zatayi mani.

Sallama akayi ta bayanmu duk muka juya ga mai sallamar ni da Saratu kenan.

Saurayine kyakkyawan gaske mai yawan dariya, muka amsa sallamarshi, dan Allah katin MTN nake so ku bani, nai mishi nuni ciki da yatsa ina faɗin ga masu siyarwa can...

Yai godiya ya juya wajansu suna ciniki, mu kuma mukaci gaba da maganarmu, amma ina satan kallonshi ta gefen ido.

Shigarshi tafi ɗaukar hankalina, gashi fari mai ainihin kyau, tsayayyen namiji tsayinshi abin sha'awa dan ya yi irin tsayin da nike son ganin namiji, wato irin tsayin da inna tsaya kusa dashi zai rinka ganin tsakiyar kaina.

Sai dai gaba ɗaya shigarshi ta baƙi ce wato abinda ya haɗa da kaya takalmin ƙafarshi agogo da baƙin glass ɗin daya rufe idonshi, da yake kallone bana sosai nake mashi ba shiyasa ba zan iya banbance yaya kamanninshi suke ba balle na ɗorar.

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now