page 15

89 4 0
                                    

🤳🏻

⏳🕹⏳🕹⏳🕹
нalιn dana ѕнιga...
⏳🕹⏳🕹⏳🕹

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*


💘 *15* 💘


بسم الله الرحمن الر حيم




Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Zumbur na miƙe tamkar wadda kunama ta harba ban furta komai ba illa falon dana bari cikin sassarfa...

Sai da na isa ɗakina naja ƙofa na rufe sannan na ce da haske kaine Ibraheem?

Yai murmushi kina mamakine Asiyah?

Wayyo ni doguwar ajiyar zuciya nayi na faɗa da baya kan gado haka kawai naji kuka mai ƙarfi ya ƙwacemin, wanda ni da kaina sai da na nemi jin dalilin kukan shin na farin ciki ne kona me?

Meye abin kuka Asiyah? Ya faɗa da alamar ruɗewa atare dashi, yaci gaba da cewa; ko ba kiyi farin ciki da jina bane?

Na ɓata maki rai ne Siyah?

Dan Allah kiyi hanƙuri wallahi in kince bakyaso sai na haƙura amma Allah ya gani bana son damuwarki, dan Allah ki daina kukan nan bakyaso na kyaleki ko Siyah?

Na juya kai muryata na rawa na ce yi haƙuri...to! to!! to!!! aini kukan naki ne bana sonji, kiyi shiru ki share hawayenki sai muyi magana.

Nabi umurninshi na share hawayen nai ƙoƙarin tsaida kukan nawa...

Naji ajiyar zuciyarshi ya sassauta murya ya soma magana ahankali cikin natsuwa.

Siyah na me zai samanke kuka me zai tayar da hankalinki irin haka, ko dai da gaske ne da akace ba zaki kulani ba balle batun soyayyata ta samu waje a zuciyarki?

An tsoratani ainun akanki amma na daure na ce zan tunkareki naji tabakinki, ashe ko abinda mutane ke cewa ba ƙarya bane da gadke bakyaɓsona gashi kinyi baƙin ciki da jina...ba haka bane, na katseshi muryata adakushe, to maye? Ya faɗa muryarshi ƙasa-ƙasa.

An haddasa min damuwa ne game da kai an raunana zuciyata akan soyayyarka na dasamin azababbiyar ƙaunarka azuciyata amma aƙarshe an ruguzamin duk wani shiri da buri danaci game da kai da soyayyarka, to taya yau kwatsam na jika ba zanjini cikin wani irin hali mai rikitarwa ba?

Um kinada gaskiya Siyah to amma aiba kukane ya kamaceki ba sai kiwa Allah godiya daya fito miki da Real Ibraheem saɓanin wancan na bugin.

Na ware ido me kake nufi?

Yayi ƴar dariya ina da masaniyar duk abinda ya faru, wancan karo kusan nace maki dasa hannuna amma dan Allah bana son tada maganar aimin afuwa arungumeni da soyayyata.

Nayi sansanyar murmushi da gyara kwanciyata, gaskiya Ibraheem bazan cuci kaina ba game d akai, Allah ya gani ya sani ina sonka ina ƙaunarka inaa jinka araina irin yadda ma bs zan iya kwatanta maka ba dan haka ba zaiyiwu naiwa zuciyata kwauron abinda take so ba...

Ataƙaice dai tuni na sallamawa rayuwata kai, ina sonka Ibraheem so irin wanda ba zai faɗu ba..sassanyar dariyarshi ta katseni, na gide Siyah ina alfahari dake ina farin ciki da kasancewarki tare dani, nayi na'am matuƙa da soyayyarki na ƙarɓeta na rungumeta ina maraba dake cikin rayuwata.

Na gode na faɗa asanyaye, nine da godiya Siyah, saboda me?

Abubuwa da yawa aciki hadda soyayyata da kika tallafa ba tare da kin wahalar dani ba, nayi murmushi kasan matsayinka awajena kuwa?

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now