🤳🏻
🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳
нalιn dana ѕнιga...
🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳~Labarin gaske ne~
© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ
w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984
*_Not edited_*
💘 *20* 💘
بسم الله الرحمن الر حيم
Saura kwana huɗu Ibraheem ya dawo da yamma ina amsa wayarshi yakemin inna dawo Asiyah kwana biyu zanyi a Lagos zan wuce Niger, na tambayeshi lafiya dai?
Um to kinsan matsalar gidan namu sun ƙara tayar ɗa rigima sai anraba gado anba kowa nashi, jiya kawunmu yake faɗamin yace lallai nazo gida cikin satinnan saboda hankula sun tashi har suna neman zubda jinin juna..
Na dafe kai da damuwa na ce meyasane ƴan'uwanka suke haka Ibraheem? Ai dama kece kika kasa fahimtar al'amuran cikin gidanmu, amma cike yake da maɓyan matsaloli wanda gaba ɗayansu akan ƴan'ubanci ne, muryata asanyaye na ce Allah ya kyauta..
Ranar da Ibraheem ya dawo na wuni cikin farin ciki domin dawowarshi shike nuni da lokacin ganin junanmu yyai haka nan ina hangen lokacin mallakar junnamu ya yi, ya faɗamin cewar awashe gari zai wuce Niger dan kawunshi y amatsa akan lallai yaje dan abubuwan gidan ƙara lalacewa suke.
Da asuba ya sake kirana yace yanzun nna zan wuce, nace to Allah yakiyaye hanya ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya, ya amsa da amin na gode, na tambayeshi kwana nawa zakayi, sai yanda hali yayi Asiyah inna tarar maganar takwanta to, inkuma baiyiwu ba inaga sai an warware komai kamin na dawo amma insha Allahu daga can kaduna zanyo dan haka ki kwantar da kwantar da hankalinki ki kulmain da kanki dan Allah karkisa damuwa da tunani aranki kinji?
Na juya kia da faɗin karka damu, ina kuma addu'a Allah ya kwantar da rigimar dake tsakaninka da ƴan'uwanka, ya amsa da amin na gode mukai sallama.
Ina tare da Hussain Muhammad ya zo, ni suna bala'in bani mamaki yadda suka tsani juna, kamar yadda Hussain yasha faɗamin ya tsane shi ya tsani tarayyarmu haka ma Muhammad yake faɗin na tsani na gnaki da mutumin can Asiyah, ko yace dana isa dake da nahana tarayyarki da Hussian, amma gaba ɗayansu ba wanda ya taɓa cemin ha laifin wani koko ga aibun wani dan hakane nafi danganta ƙin junansu da cewa kishi ne..Ganin zuwan Muhammad Hussain yace zai tafi, nayi dariy a nace kaga abokin adawarka ko?
Ya juya kai yace kin kasa fahimta tane Asiyah, amma inda abinda naƙi jini shi ne tarayyarki da yaron nan ba, har yanzu baka taɓa cemin ga aibunshi ba, ba zaki gane bane ako da yaushe dai ina gargaɗinki ki iya takunki agabanshi kisan abinda kike yi, ya shige mota yana faɗin meyiwuwa nayi tafiya gobe dan karkijini shiru kice nayi fushi dan nasan halinki da fassara..
Dariya nayi nace to Allah yakiyaye hanya akuma gayarmin da Mama, ya harareni baza'a faɗa ba kinƙi zuwa ki gaisheta sai dai ki rinƙa yi mats miƙan gaisuwa, ina dariya nace aimin afuwa wataran zanje insha Allahu.
Bayan tafiyarshi na iske Muhammad ya cika da fushi na tsaya akanshi ina dariya ya kalloni aƙufule cikin fushi yake magana, wallahi Asiyah na faɗa niki ki fita sabgar Hussain na faɗa miki ki fita hanyarshi kinƙi ko...na katseshi da faɗin da zarar ka faɗanin aibunshi ɗaya zan fita hanyarshi, yai shiru baice komai ba, nace kaga ko baka da hujjar da zaka matsamin na rabuda shi, inhar baka son ganinshi to ka daina zuwa dai-dai lokacin da yake zuwa.
***
Na isa gidan Anti Lubah na isketa tana faman rubutu na tsaya akanta ina dariya ta ɗago ta kalleni tace wai meye abin dariya ne?
Nace kina birgeni ne wallahi, yadda kike zama ki tsara labari ki sarrafashi yai daɗi irin yadda zai shiga zukatan mutane kiyishi tamkar gaske, ni wallahi inna karanta takaedunki kaina yakan ɗaure sai naga kamar bake kika rubutashi ba, tayi dariya tace kika sani kobani ke rubutawar ba, na juya kai duk inda aka shiga ba zan yadda ba, sau nawa ina ganinki duƙe kan takarda irin haka.
Kinsan wani abu? Ta tambayeni na juya kai ina gyara zama kusa da ita, abin nan sa kai ne Asiyah, kema inkikasa kanki nan da nan sai kiga kema kin zama marubuciya mai yiwuwa kiyinfsrin jinin da wani marubucin baiyi ba matsalar dai kisa bain aranki, nayi dariya sosai nace wasa kike Anti Lubah kawai ace daga sama ka ɗauki sana'ar da ba taka ba, ba haka bane Asiyah na faɗa maki abin sa kai ne, banda wannan ba kina karatun takardu irin haka ba, tabbas, to a irin karance-karancen ne ba nan zaki riƙajin yana jan ra'ayinki musamman kinci karo da wani waje bai maki ba cikin labarin, sai kirinƙa ayyanawa aranki ai da ni ce wajan nan abu kaza zansa ba abunda marubuciyar tasa ba..
Koko kici karo da wani abun da bai dace ace ansashi a wajan da aka sanya ba sai kiji aida kece awajan ga abinda zaki sa, to ire-iren hakanne zai rinƙa jan ra'ayinki sai kema kiji kina sha'awa ahankali wataran sai kiga kema kin fara rubutun labarin, kwanci tashi sai kiga kin shiga sawun marubuta, mai yiwuwa alokacin kiga kece marubuciyar da ake yayi, da fatan kin fahimceni?
Na ce ƙwarai na gamsu dake Anti Lubah, amma duk da haka ina ganin abun kamar da wuya sai wataran ɗin zan jaraba naga ko za'a dani, amma fa saina nemi taimako wajenki tayi dariya tace zan baki taimako ko wane iri kika buƙata Asiyah.
Na ɗaga littafin da take rubutawa nace shi kuma wannan wannene ina kama haɓa ina kallonta, meya ƙunsa ne? Ki jira na kammaƙa ki karanta, in kuma zaki bari saiya shiga kasuwa ne to...
Na baro gidan Anti Lubah la'asar lis a hanyata ta zuwa gida na gamu da Muhammad ya biyo sawuna, muka jera tare zuwa gida, aƙofar gidanmu muka tsaya yana kallona yace dan Allah rakani gida na baki wani saƙo, na harareshi nace meya hana da zaka zo baka taho dashi ba sai yanzu kace ɓa wani rakaka...wallahi ba daga gida nake Asiyah, ya katseni da faɗin haka , nace to ka bari lokacin daka taho dashi daga gidan ka bani...zai sake magana na katseshi barni na shiga gida Muhmamad tun safe na fita, ba'a son ranshi mukai sallama ba na shiga ciki na barshi.Da daddare ya dawo ya kawo min abinda yace saƙo, Shagalinku Yoghurt ne na babbar roba sai damammiyar fura da aka dameta da shagalinku taji sugar gashi tayi ɗan karen sanyi, mun ɗan taɓa hira mukai sallama..
Ina shirin kwanaciya kiran Ibraheem ya shigo na amsa tare da sallama, bayan mun gaisa na tambayeshi yaya lamuran suke tafiya, yace to sai dai addu'a Asiyah, dan aynazu haka ma lutinin mai zuwa zamu shiga kotu, to akan me Ibraheem?
Na tambaya cike da damuwa, sha'aninne Asiyah sai addu'a, a yadda hankula suke atashe agaremu babu ta yadda za'ayi araba gadon nan agida saboda acikinsu kowa ya nuna ga abinda yake so, wanda acikin tsarinsu abin ya keta ƙa'ida dan kowa abinda ya ɗauka ya wuce misali, wanda dukkan dukiyoyin da Baba ya bari sun rabasu atsakaninsu, ke ko ƴan'uwanmu mata dake gidajen mazajensu basa maganarsu sai kansu, kinga dole hukuma ta shigo cikin lamarin.
Nace haka ne amma kai ka ƙara haƙuri da juriya kaine babba acikinsu, dole ka zamo mai jansu ajiki da nuna masu muhimmancin haɗin kai, ka nuna masu kuso junanku da gaskiya da amana, ka ture batun ƴan'ubanci gefe kuɗin jinin junane tushe ɗaya yayiku sai kaga insha Allahu wani lokacin an sami maslaha tsakaninku..
Ina ƙoƙarin yin irin hakan Asiyah, kuma akoda yaushe ina fata da roƙon Allah ya nunamin ranar da kawunanmu zasu haɗe mu zamo masu ƙaunar junanmu.
Wasa da wasa sai ga Ibraheem ya kwashe sati uku a Niger cikin zuri'arshi, an riga an gama raba gadonsu kowa yasan abinda yake haƙƙinshi da kadarori zuwa tsabar kuɗaɗe anraba anba kowa nashi.
To me ya rage' Ibraheem akoda yaushe ƙoƙari yake yaga ya dai-daita tsakaninshi da ƴan'uwanshi, ayadda ya faɗamin sun ɗan fara fahimtarshi har wasunsu sukan sashi asabgarsu su saurareshi in yana magana dasu, shiyasa yace min baya son tahuwa ayanzu sai yaga komai normal atsakaninsu, ni kuma akoda yaushe ƙara bashi ƙwarin gwiwa nake dan ina so ƙwarai naga zuri'ar gidansu sun fahimci juna ina so sosai suso junansu su gane su ɗin abu ɗaya ne.
Ba zanji daɗi ba ace auri mijin da gidansu bbau zaman lafiya danni gaskiya Allah ya gani ina son yin rayuwa mai tsabta da dangin mijina, wanda hakan bazai samuba sai da so da ƙauna tare da nuna kulawarsu ga ɗan Uwansu inba wannan nima tabbas ba zasuyi zaman lafiya dani ba gashi nikam Allah yayini bana son tashin hankali...
( *Na dai samu matsaya ta kwalliyar page*😂🕳🕯🕳🕯 *duk ina kuka wannan to Aysha Machika ce*)
🕳🕯Machika novel🕯🕳
YOU ARE READING
HALIN DANA SHIGA...
No FicciónKashi 80% labarin gaskiya sai kun nitsa ciki zaku gane inda ya nufa...