page 9

149 8 0
                                    

💘 нalιn dana ѕнιga...💘

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

*Arewabooks@shooly84*






💘 9 💘




   Ban sake ji daga gareshi ba sai bayan kwana bakwai ina makaranta wayarshi ta shigo, muryarshi kamar ta rannan nai ƙarfin halin kawar da damuwata nace ya jikinka Ibraheem?

Ina samun sauƙi Asiyah sai dai tunaninki yafi addabar zuciyata fiye da ciwon da nake tare dashi, tausayinshi ainun ya kamani zanyi magana yai saurin cewa yi haƙuri Asiyah zan sake kiranki bai jira nace ba ya tsinke layin...

Nai jim ina tunaninshi da halin da yake ciki, abinda ya ƙara tada hankalina yanda yaimin sallama kamar yana cikin tsoro ko kuma zafin ciwo.

Kwana biyar tsakani ya sake kira yace " yi haƙuri Asi rannan na katseki, wallahi jaraba suke man innayi magana wai bana son na samu lafiya, ni kuma Asi ba zan iya haƙurin ɗaukar dogon lokaci ba tare da naji muryarki ba, yanzu ma wai mintuna biyar kawai aka bani.

Nace toh kai kayi haƙuri mana, bana iyawa ne Asi, yama za'ai ace ba zanji halin da kike ciki ba ai cutata akeyi, nace amma ai zakaso ka sami lafiya da wuri har kayi ƙoƙarin haɗuwarmu ko?

Yace haka ne, to kayi haƙurin daina magana dani har zuwa lokacin da za'a baka damar yin magana da kowa, to zanbi umurninki Asi zan ringa gaidaki kona second ɗaya ne, nace naji na yarda amma dan Allah ariƙa bin umurnin likita ina buƙatarka fa da wuri Ibro, na sani Asi shiyasa nima nakeson samun lafiya nazo inda kike, nace amma fa sai kabi umurnin likita, yace zanbi wallahi zanbi Asi.

Yau muna tare da Muhammad aƙofar gidanmu, ya sani gaba da azabar kallo na damu nace wai kallonnan na lafiya ne Muhammad?

Yai ɗan murmushi yace "Tausayi kike bani Asiyah, duk kinbi kin ƙwallafa ranki ga Ibraheem, yanzu inya mutu yaya zakiyi?

Naji wani abu ya tsirgarmin cikin ɓacin rai nace anyako kasan darajata Muhammad, kwarai dole nasan darajarki kodan ƙaunar dake tsakaninki da ɗan'uwana, nace toh amma nayi mamaki da bakinka ke ambaton mutuwa ga ɗan'uwan naka, ashe ba kaine zaka zamo mutum na farko acikin masu son ganin ya sami lafiya ba, amma da bakinka kake mashi fata irin haka.

Bawai fata nake miki ba Asiyah misali na baki ganin irin mawuyacin halin da kika shiga sai nai tunanin ciwo fa to inaga mutuwa yayi wane hali zaki shiga, nace toh gaskiya bana son irin wannan misalin da tunanin daga irin hakane yake komawa mugun fata , na bari Asiyah amma dan Allah kirinƙa sassautawa ranki wannan damuwar da kike tayi yawa.

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

  Abdul yake gaya min za'a fitar da Ibraheem waje, za'ayi mashi aiki a haƙarƙari, na ruɗe nace wai wane irin ciwo ke damunshi ne haka?

Yace "gaskiya yanda Yusuf ke faɗamin ciwon sunada yawa akwai karaya biyu akafaɗar dama da hannunshi na hagu ga wuyanshi da kanshi da gaɓoɓinshi sai kuma haƙarƙari wanda shiyafi damunshi da wuyanshi.

Na zuba uban tagumi tare da sawa Abdul ido, tunani nake azuciyata wai da irin wannan ciwon ajikin Ibraheem amma har yake da sukunin magana dani, yake nuna min babu damuwa mai yawa atare dashi, kai gaskiya Ibraheem yanada ƙarfin hali hakanan na yarda tabbas soyayyata mai girmace agareshi.


Cikin ikon Allah ranar bayan sallar magriba ya kirani, abinda ya fara ce man shine Asi kinji za'a rabani dake ko?

Nace kayi haƙuri Ibraheem ba rabamu za'ayi ba neman lafiyarka suke, to amma ya bazasu barni anan ba inda nake jin muryarki tamkar ina kusa dake, ka daiyi haƙuri Ibraheem, nifa nafi buƙatar lafiyarka akan komai, yace ni kuma kece damuwata Asi ya zanyi?

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now