26

108 8 2
                                    

🤳🏻

🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳
нalιn dana ѕнιga...
🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*

🕳 *26* 🕳


بسم الله الرحمن الر حيم






{ *_Ki ban banta tsakanin ya'yanki mata da maza,a wajen kwanciya,kai a wajen abubuwa da dama,matukar sun fara wayo sun fara bambamce tsakanin halittan ya mace da na miji,kada ki bawa yaranki na miji ya yiwa yarki mace tsarki ko wanka,bar ganin ciki daya suke,wannan zaisa ya fara na zari akan halittan ya mace ,daga nan wani tunanin zai iya darsuwa a ransa, na son gano a salin hallitan mata,kada ki bari yarki mace ta saba da hawa jikin Dan uwanta koda ke kika haifesu duka,ki koyamata nesantan taba jikin na miji, idan ta saba da tsoran kusantar jikin Dan uwanta to zaiyi wuya ta kusanci Wanda ba Dan uwanta tunda kin hanata hawa jikin Dan uwanta ma to ta hakan zatasan cewa a kwai wani abu mai girma da kikeson fahimtar da ita_*}


Sati kusan biyu kenan da zuwan Ahmad Ali wajena, farin cikin haka yasa na gaza fahimtar bai sake waiwayata ba sai ni ce jefi-jefi nakan ɗan taɓoshi awaya ta chatt, shima sai ai wuni guda zungur kafin inga ƴar taƙaitacciyar amsar shi, waya kam zanyi ta kira bai ɗagawa, sam ban damu ba dan dama kusan haka muke tun farko ni ce mai yawan nemanshi koda yaushe.

Rannan ina hanya zanje kasuwar gari dan ina son yin ƴan siye-siye na kayan buƙatu..

Na hau mashin kenan dan ban fito da mota ba tana buƙatar service dan haka na barta a gida na ɗale mashin, wayata na cikin handbag ɗita naji tana ta tsuwwa.

Na fiddo ganin mai kiran yasa na shafa na sanya akunne, saboda iska da yanayin gudun da mai mashin ɗin keyi yasa na ƙure volume ɗin wayar sannan na soma jin muryar Ahmad Ali yana faɗin Asiyah ce na ganta ɗale a mashin?

Cikin dariya na ce ni ce fa a ina ka ganni? Shima dariyar ya yi yace yanzu dai ya samu waje ya ajiye mani ke, yana faɗin haka ya kashe wayar, nima nace ma mai mashi malam ɗan Allah inka samu waje ɗan gangara ka saukeni za'a ƙarasa dani..

Gefen hanya ya tsaya na biyashi kuɗinshi ya ƙara gaba ni kuma na soma duban hanya minti biyu tsakani Maroon ɗin motar Ahmad ta faka agabana, ya sauke gilashi yana ƙare mani kallo daga tsaye ina cikin doguwar rigar wani farin material mai manyan fulawowi ja da yalo sai takalmi mai dunduniya saboda ya ƙaramin tsayi, kaina kuma na naɗeshi da jan gyale madai-daici, fuskata tasha light make-up sai ƙamshin *Humra da sweet candy* nake.

Shi kam sanye yake cikin light blue ɗin shadda, sai da na shiga motar na fahimci ɗinkin ƙarami ne irin na yayi, sanyin Ac da ƙamshin turarikanmu suka cika motar, na lumshe ido wani daɗi yana ratsani...

Murmushin saman fuskarshi bai ɗauke ba lokacin daya harba motar kan titi ba tare daya juyo ba yake tambayata sai ina Asiyah zata haka cikin rana?

Na juyar da kai ina dariya, wallahi kasuwar gari zani, ya ɗan kalleni ya mai da kai ga titi bai sake cewa komai ba, dan haka nima na lumshe ido..

Tafiyarce naji tayi tsayi dan haka na buɗe idon saina tsincemu kan titin Barnawa yanata sharara gudu, cikin sauri na kalleshi da wani irin yanayi ina faɗin ina zamu ne wai?

Ya ɗan kallan yana murmushi, ya maida kai kan titi yana faɗi sai da ke zanyi, kinsan kuwa zakiyi kuɗi Asiyah, jin abinda yace yasa na ɗanyi murmushi ban sake cewa komai ba, duk da wata zuciyar tawa tana aiyano mani nace ya juya amma na kasa furta komai dan bana son ranshi ya ɓaci dani.

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now