page 5

159 12 2
                                    

🤳🏻

🖤💘 нalιn dana ѕнιga...💘🖤

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984



*S͢A͢D͢A͢U͢K͢A͢R͢ WA G͢A͢R͢E͢K͢U*...

*ᴷᴴᴬᴰᴵᶻᴬ ᵁˢᴹᴬᴺ*
*ᴺᴬᴮᴵᴸᴬ ˢᵁᴸᴬᴵᴹᴬᴺ*
*Ɗᴬᴵᵞᵞᴵᴮᴬ ᴵᴰᴿᴵˢ*
*ᴴᴬᵁᵂᴬ ᴬᴸᴵᵞᵁ ᴿᴬᴮᴬᴴ*
*ᶠᴬᵁᶻᴵᵞᵞᴬ ᴰᴬᵁᴰᴬ*


💘 5 💘


بسم الله الرحمن الر حيم




Cikin ƙanƙanin lokaci soyayyar dake tsakanina da Ibraheem ta bayyana ga kowa, duk wanda ke mu'amula dani yasan Ibraheem abakina yasan irin girman son da nake mishi...

A wajan Anty Lubah ko wannan sunyi sabo sosai, sau tari ya kanyi waya yace yayo ne kawai ya gaisheta wani lokacin kuma yace ni kam Anty kici gaba da taimakona kina kula min da soyayyata a wajan Asiyah, dan haƙiƙa sonta na neman zautani akullum bani da wani sukuni saina tunaninta, shin Anty Lubah ya zanyi Asiyah ta soni kamar yarda nake sonta?

Anty Lubah takance dani Asiyah na kan rasa amsar da zan ba Ibraheem, ako yaushe dai ina ce mishi kina matuƙar sonshi, inna gaya mishi hakan ya kanyi doguwar ajiyar zuciya yaiwa Allah godiya.

Sau tari tana ce min Asiyah ki tausayawa bawon Allah nan karki biyar dashi ta irin hanyoyin da kika saba biyar da sauran samarinki, dariya nake inta faɗi haka ince Anty Lubah Ibraheem da ban yake da sauran maza, awajena sonshi wani irin sirrine atare dani.

Wallahi duk yanda nakai da fayyace miki irin son da nake mishi ban taɓa zaton na faɗi kwatan yanda nake jinshi ba, dan haka Anty Lubah Ibraheem nawane, burina na mallaki abuna..


Shi kuwa yanzu Abdul hirarmu ako yaushe ta Ibraheem ce, akullum ina mishi naci don ya kwatantamin kamannin Ibraheem, sai dai yace "Asiyah duk yanda zan kwatanta miki shi zan iya kuskure, ma'ana ina iya rage abubuwa da yawa dangane dashi, abinda zance miki kawai kiyi haƙuri har lokacin da Allah zai haɗa fuskokinku.

Tsakanina da Ibraheem daga waya sai test, aikinmu kenan kullum safe rana dare muna manne da waya, hakanan ta wannan hanyarne muke ƙara cusa ma kawunanmu ƙaunar juna da farantawa ranmu ta hanyar dadaɗan lafuzzai...

A test ɗinshi na yau cemin yai shin wanne irin taimako zaki iya yiwa ran dayafi kowanne rai ƙaunarki Asiyah?

Na maida mishi amsa da cewa, taimako ɗaya ne Ibraheem na baka kaina na baka soyayyata inaso ka sani ni takace burina ɗaya na kasance tare kai.

Ya dawo min da cewa haƙiƙa Asiyah ba'a taɓa yi min kyautar data ɗaukaka farin cikina ba irin wannan, dan haka ma na rasa wane irin tukuicine ya dace da wannan kyauta taki, amma bari nayi maki wani alƙawari nayi miki wata irin ajiya wadda ba zata iso wajenki ba sai ranar da Allah ya haɗamu ƙarƙashin inuwa ɗaya a waje guda...ki dai jira lokacin karki gajiya.

Nai doguwar dariya bayan na gama karanta saƙon, naji harna ɗokanta da zuwan lokacin...

Da daddare kuma da yayo min waya ina ɗauka abinda ya fara cemin shine Asiyah kina sona kuwa?

Na dabirce amsa ta kasa fita bakina sakamakon haushi da tambayar tashi ta bani, shida ya dace ya baiwa wani labarin son da nake mishi amma shi zai bijiro min da tambaya irin haka.

Kamar na kashe wayar sai kuma na daure na tambayeshi me yasa kaimin wannan tambayar?

Yace " shin Asiyah kinsan ko yanda nake jinki araina?

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now