page 32

188 12 1
                                    


  💘 нalιn dana ѕнιga...💘

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

*Arewaboomks@shooly84*

*_Not edited_*

*32*


Kusan awa guda ya ɗauka a ɗakin sannan ya fito falo lokacin harna fara gyangyaɗi azaune, zaman da ya yi kusa dani yasa na buɗe ido ina kallonshi fuskata aɗaure, yana sanye cikin gajeran wando na bacci sai rigarshi mai ƙaramin hannu, muna haɗa ido ya sakar man murmushi yana faɗin Babyta harkin fara bacci ne?

Harara na sake dallah mashi na kawar da kai gefe ina jin wani irin takaicinshi, murmushi ya sake yi yana janyo ledar daya ajiye ya shiga fiddo kayan ciki, ƙunshin kaza guda biyu sai freshmilk mai sanyi, da kanshi ya tashi ya shiga kitchen ya ɗauko plate da cups biyu ya zo ya ɗora kazar akai, sannan ya zuba mana madarar a cups ɗin ya kalleni yana faɗin zo kici dannan san dai da ƙyar inyau kinci wani abincin kirki.

Na haɗiyi miyau jin ƙamshin kazar yadda ya cika mani hanci, amma maimakon na sanya hannu naci ɗin saina ja tsaki kawai na miƙe da niyyar barin wajen, aiko ya sanya mun ƴan siraran ƙafarshi ya taɗiyoni na faɗo kanshi gaba ɗaya.

Ya yi maza ya tureni yana harara da faɗin lafiyarki lau kuwa haka kawai zaki rakwarkwashe ƙashin *Yaro* ko ƙasusuwan ɗan tatsitsin ƙirjina zaki ɓalla?

Bance mashi komai ba na sake yunƙurawa zan miƙe ya riƙeni, riƙo irin wanda ba zan iya ƙwace hannuna ba, na kallai da ɓacin rai na ce sakarni bacci nake ji, sai kin tsaya kinci wannan kazar, domin Allah bana asararta dole kici kazar amarci nan ya ida faɗa yana wannan munafukin murmushin..

Yunwa nake ji bata wasa ba, dan haka na aje makaman yaƙina na ci abinda cikina zai iya ɗauka, nasha kofin madara ɗaya sannan na miƙe bako sai da safe na wuce zuwa ɗakina.

Kai tsaye kewaye na wuce na wanke hannu nayi brush nayo alwalla kuma na zo na soma nafila ina roƙon Allah biyan buƙata, wajen awa guda na ɗauka sannan na miƙe idanuna sunyi nauyi na cire hijab na haye gado bayan na ɗan ƙara ƙarfin fankar sama na kashe wuta, sai ya zama ɗan hasken fitilar tsakar gida ce kawai ta haska ɗakin kaɗan ta window.

Ina kwanciya bacci ya ɗaukeni, amma kuma bani zaton nayi ko minti ashirin da baccin naji anata shafa mun fuska ahankali, na buɗe ido cikin ɗan hasken daya ratso muka haɗa ido da Labid, ƙirjina yai wani irin bugawa amma dan masifa sai nace mashi meye haka kuma?

Me zanyi maka? Kaje naka ɗakin mana kazo ka wani kwanta kusa dani dan rashin kunya, Baby laifi ne dan miji ya kwanta kusa da matarshi? Na hasala nace wacece matar taka? Kai nan har wani namiji ne?

Me zaka tsinana mun, ni ai kayi man kaɗan ina neman namijin daya amsa sunanshi ne ba kai ba Yaro ƙarami, murmushi ya yi ya miƙe zaune kan gadon sai lokacin na fahimci ya cire rigar jikinshi sai gajeran wandon kawai, kafin na gane abinda zaiyi naji kawai nima ya miƙar dani zaune cikin sakonni ƙalilan ya fincike rigar jikina ya wurgar ƙasa, cikin tashin hankali na sanya hannuwana na kare ƙirjina ina watsa mashi mugun kallo.

Wane irin wulaƙanci ne haka Labid?

Turani baya ya yi na kwanta kafin na taso yaiman rufa da ƙaramin ƙirjin nashi danake kira, yasa hannayenshi ya ɓanɓare nawa ya haɗesu baya yadda babu wani taimako da zanma kaina dasu, ya soma magana hannunshi ɗaya  afuskata.

Na farko dai Baby ni ɗin mijinki ne dake da iko akanki ahalin yanzu, kome naki mallakina nane sai yadda nayi dashi, tun daga nan ya soma yawo da hannun nashi kan sumar kaina har zuwa nan da nan, ya sauko kan fuskata ya yi ƙasa kan wuyana kafin ya kawo hancinshi yana shinshina mani wuya, nan take na soma jin kamar wutar lantarki na jana.

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now