Page 1•

536 15 0
                                    

BAYAN WUYA

® Basira Sabo Nadabo

Bismillahir-Rahmanir-Rahim

1•

NASABAR TORONKAWA

Abinda yasa akece musu TORONKAWA saboda sun zamna ƙasar Toro itako Toro ƙasa ta cen gefen yamma maso kudu na Afirka ta yamma, sun taso daga wajjen Durisina cikin ƙasar Sham sun biyo daga gefen Afrika ta yamma har suka sadu da Toro suka zamna wurin, sukayi yawa ƙwarai har lokacin da aka aiki Ukubatu da yaƙi zuwa Afrika ya sadu dasu sai suka shiga addinin musulunci bada faɗa ba Ukubatu ya amri ɗiyar sarkinsu mai suna Bajjo Mangu, to su Toronkawa suna daga cikin zuriyar Rama ɗan Isa ɗan Ishaku ɗan Annabi Ibrahimu (A.S), Bajju Mangu ta haifi ɗiya huɗu da Ukubatu sune (1) Deita (2) Woya (3) Roboba (4) Nasi, to waɗannan sune asalin dukkan Filani su suka fara magana da fillanci, daurin Toronkawa hausarsu Wakuru to sa'an nan ɗiyan Ukubatu suka yawaita suka kasu kashi huɗu sune (1) Ɗiyan Deita daga gare su kabilar Songhay suka fito, (2) Ɗiyan Nasi suko daga gare su dangin Ba'awina suka fito da dangin Wolorbe, (3) Ɗiyan Woya suko daga gare su dangin Forbe suka fito, (4) Ɗiyan Roroba su kuwa daga gare su dangin Wolobe suka fito, waɗannan sune asalin ɗiyan Ukubatu bayan ga haka sukayi yawa suka hayaiyafa suka tafi suka zamna wuri da ake kira Falgo suka rabu da Toronkawa na Futa-Toro.
Lokacin da sukayi karfi sai suka ɗauko yaki babba suka taso ma Futa suka ci amanar sarkin Futa suka kashe shi shina Sallar Idi, suka kama ƙasar Futa suka zamna suna ɓannace-ɓannace sa'an nan wani Malam Ibrahim daga cikin Toronkawa ya tashi yayi jahadi dasu yacu su ya rinjaye su, ya gyara ƙasa ya zuba adilci ya kyautata zaman Toronkawa sai sadda ya rasu Filani ɗiyan Ukubatu suka komo suka sake yaƙi da Toronkawa suka kore su, suka sake kama ƙasa suka sake shiga ɓannace-ɓannace bayan haka kuma sai Toronkawa sukayi shirin yaƙi da Filani ɗiyan Ukubatu suka taho da yaƙi sukayi faɗa dasu mai tsanani suka rinjaye su mugunyar rinjaya saboda haka sa Filani ɗiyan Ukubatu suka kasu ukku, kashi guda suka bi Toronkawa kashi na biyu suka koma Falgo inda suka fito kashi na ukku yayo gabas suka tasamma Masar suka ce zasu inda ƴan uwansu Larabawa saboda ubansu Balarabe ne, wasu daga cikinsu sun isa har ƙasar Larabawa wasu ko suka kasa suka tsaya nan wanda a babbansu sunanai Dunrundi to waɗannan da suka gaza isa suka tsaya nan sune dangin Beni Yalalɓe da Walanɓe da Gumborawa da Galankwa'en da Filanin Adamawa, waɗannan sune dangogin da suke daga cikin zuriyar da suka taho Naskanga tare da Dunrundi, su waɗannan mutane sunfi Toronkawa yawa kuma bayan haka sai waɗancen Filani da sunka koma Falgo suka sake ɗaukar yaƙi suka taso ma Futa sukayi yaƙi da Toronkawa sukaci su, suka koma halinsu na ɓannace-ɓannace sa'an nan kuma Malam Sulaimana daga cikin Toronkawa ya tashi yayi jihadi da Filani ya rinjaye su ya watse su, ya shimfiɗa adilci ya naɗa musu Sarki Abdulƙadiri bayansa kuma anka naɗa Muhammadul Aminu anka zamna cikin lafiya, Toronkawa suka amince da Filani ɗiyan Ukubatu.
Bayan waɗanga al'amurra da muka faɗi lokacin nan Musa Jakallo kakan Shehu ya taso da jama'atai don gudun fitina ya fuskanci gabas, har ya iso Ƙwanni ya sauko 500 A.H. shi kuma ɗiyanai suka kasu kashi biyar, na ɗaya ɗiyan Ali, na biyu ɗiyan Kogga, na ukku ɗiyan Baleni, na huɗu ɗiyan Raneni, na biyar Sarkin Damka ya zambace su ya karkashe su awa mutun arba'in ya kama ɗiyansu ya sashe dukiyarsu, sai ɗiyan Ali suka sauka wani wuri da akece ma Kuluba.
Dangantakar Shehu zuwa Musa Jokollo Usumanu ɗam Muhammadu Fodiyo abinda a ma'anar Fodiyo mallami kuma wanda mallami ya haifa, shi Fodiyo ɗan Usuman ɗan Salisu ɗan Haruna ɗam Muhammadu Gurdo ɗan Jabbo ɗam Mamman Samba ɗam Masirana ɗan Aguba ɗam Baba ɗan Abubakar ɗam Musa Jakollo wanda yake da ɗiyan Imamu Demba Intaha.

Imamu Demba Musa Jakollo babban malami ne a kauyen Jaada dake cikin garin Yola, shahara da ɗunbin ilimin mahammadiyya da Allah ya azirtashi dashi yasa duk faɗin kauyen ansan shi dama makwaftan kauyukan irin su Maya Balwa da Gire dama sauran kauyukan da suke makwaftaka dasu Imamu Demba yana da mata biyu Inna Hajjo da Inna Ƙariba, Inna Hajjo masifaffiyar macace wacce duk kauyen yasan da irin rashin mutuncin da take shukawa Imamu kuma shi mutun ne mai hakuri da kawaici, wannane ma yasa babban malamin kauyen Gire ya ɗauki ƴarshi sadaka ya bashi saboda yabawa da irin tarbiyya da kuma gidan data fito yasa Imamu Demba yasa hannu bibbiyu ya amshi sadakar da aka bashi a take kuma ya biya sadakinta da Alkur'ani mai girma ɗunbin mutane da sukaje ziyartar kauyen suka shaida auren kuma ziyartar juna wannan al'adan duk wani bafilati ne, koda labarin auren Imamu ya riski Inna Hajjo ba karamin haukace masa tayi ba, har sai daya haɗa da rubutu sannan ya samu ta sauko daga jakin haukarta koda Ƙariba ta shigo gidan Hajjo bata sauya zaninta na baƙin kishi ba kuma saboda ganin ta da tayi yarinya yasa ta dinga azabtar da ita kamar an kawo mata ƴar aiki, saida Imamu ya tashi tsaye sannan ya amsowa Ƙariba ƴancinta a cikin gidan kuma har yau da girma ya kamasu Hajjo bata daina azabtar da Ƙariba a bayan idon Imamu ba kuma kun san ƴaƴan Filani da kunya shiyasa bata taɓa faɗawa Imamu abinda ake mata ba a bayan idon shi, Inna Hajjo kamar yadda yaran gidan suke kiranta dashi tana da yara guda shida biyar duk maza ne sai autarta mace, Ishaka, Aliyu, Ahmad, Sunusi, Lukman sai auta Aisha itace ta ɗauko kamani da halayyar Hajjo sak babu inda ta barota saima son finta mugayen halayya tayi kuma duk yaran suna raye, Inna Ƙariba ma tana da nata ƴaƴan guda takwas kuma bakwai daga ciki duk maza ne sai ƴar autan gidan gaba ɗaya, Musa shine babban ɗan Inna Ƙariba kuma shine yayo kamannin kakanshi sak suna kiran shi Bakaam (Yaya) sai Umar, Jamilu, Shamsuddeen, Haruna, Usmanu, Abubakar sai auta Fa'iza kuma sunan mahaifiyyar Imamu ce wacce sukewa laƙani da Inna Wuro kuma yawan ƴaƴan nata ne yasa Inna Hajjo take kara bakin ciki da ƴaƴanta, Inna Wuro ƴace mai ladabi da alkunya gata da girmama duk wanda yake gaba da ita tana da kyau kamar yadda take fara haka zuciyarta yake da haske, Inna Wuro ta taso da tarbiyya da kuma ilimi domin duk kauyen babu wanda bai santa da irin tarbiyyar data taso dashi kuma haka kowa yanaji mata tausayin kalar azabar da Inna Hajjo take gana mata, haka zalika kowa yasan rashin tarbiyya da watsewar da Aisha takeyi amma ana tsoron faɗawa malam saboda an taɓa faɗa mishi makamaicin irin hakan ya faɗi sai da kyar aka samu ya dawo cikin hayayyacinsa wannan dalilin ne yasa kowa ke tsoron tada mishi hankali, yauma kamar kullun Inna Ƙariba ce zaune da ƴaƴanta tanayi musu faɗa akan abinda sukeyi babu kyau Umar ne sarkin zuciya yace

"Toh Inna fisabilillahi haka zamu zauna sunayi mana duk abinda suka ga dama haka rannan Ahmad ya kwaɗeni da mari don na rama shine Inna Hajjo take tsine min kuma ai nine gaba da Ahmad" a zucciye yayi maganar

"Nidai kullun ina mai baku hakuri akan duk abinda Adda Hajjo zata muku kuma da yardan Allah bazaku taɓa taɓewa ba kunji?"
Ta karashe maganar da raunanniyar murya Haruna ne yace

"Nifa Inna banga laifin da Inna Hajjo takeyi ba amma kullun saiki sakamu a ɗaka kina zaginta, nifa wallahi banga aibunta ba kuma tafiki sona ke bakya sona kullun sai dai kice muyi hakuri wai tayi miki wani laifine duk kinbi kin takura mata, aradu duk wanda ya kara zagin Inna Hajjo sai inda karfi na ya kare yasin dubu zan iyasa takobi akan mutun kuma wallahi koda Inn......"
Umar ne ya ɗauke shi wani wawan mari a zucciye kuma da hagu, Inna Ƙariba da tunda Haruna ya fara magana take matsar kwalla inda sabo ta saba da mummunar halayyar Haruna wasu har suna cewa kodai don Inna Hajjo tana tsaye akanta ne yasa Haruna ɗauko wasu daga cikin halayyarta

"Wallahi Haruna ina gabda ɗaukan ranki aradu inka kuma saka Innata zubda kwalla yasin saina fille kanki da takobi" a zuciye yake managa

"Bakaamdon Allah kiyi hakuri karkice mata komai aradu Ya Haruna har yanzu yaro ne bai girma ba nima kaina in yayi wani abun sai inga kamar nice babba dashi duk da nice auta don Allah Bakaam kayi hakuri"
Duk cikin kuka take magana Musa da tunda suka fara hayaniyarsu baice komai ba ya ɗago kai ya kalla Umar, shima Umar ɗin suna haɗa idanu ya sunkuyar da kai ya durkusa a inda yake sai ajiyar zuciya yakeyi rigarsa har ɗagawa yakeyi gurin saitin da zuciyarsa yake sai kuma ya fashe da kuka, hakama Usmanu da tunda Haruna ya fara rashin kunya ya sunkuyar da kanshi kasa hawaye yana sauka akan donshi saboda zuciyar data ciyo shi, gyaran murya yayi sannan yace

"Inna kiyi hakuri da duk abinda yake faruwa da Haruna na tabbata watarana zai daina saboda yaranta ke damun shi, kai kuma Haruna abinda kakeyi kacigaba karka daina akwai ranar da nida kaina zanyi maganin ka bama saina saka yayyika ba, Umar da Usman kuyi hakuri da duk abinda Haruna yakeyi watarana zai daina In Shaa Allahu kuma kutuna Imam har yanzu ba lafiya gare shiba kuma bazamu muso daga ɗakin nan aka kashe shiba sannan ku dinga kai zuciyarku nesa har zuw......" cikin nutsu yake magana dajin muryarsa zaka san ilimi ya wadatu a tattare dashi, Haruna ne yayi saurin katse shi da cewa

"Gaskiya Yabba bai kamata kana babba kana irin wannan maganar ba wato ɗakin Inna Hajjo ne zasu kashe Imam? Haba kullun mata tana sonku amma ku bakwa sonta gaskiya Yabba ka sake tunan......"
Ɗauke shi da mari akayi wanda sanadiyyar wannan marin har saida bakin shi ya garwaye da jini


ƳAR NADABO

BAYAN WUYA (On Hold)Where stories live. Discover now