Kaine Rayuwata😭❤❤❤
Written By; Najaatu Shehu Naira
FKD Fans Writers 《《 01 》》
Da maraice gari yayi luf-luf, ba hadari ba sannan ba dare ba. Saif na kan kafar mahaifinshi yana kwance kamar jaririn shekara daya, yana janyo apple agefansa yana sha.Cikin sanyin murya mai cike da nuna shagwaba, yace "Daddy, don Allah ka barni naje trip dinna. Ni da abokaina zamuje fa, sannan ni ne jagoran tafiyar, ya za'ayi in ce musu nafasa zuwa? Ai babu dadi. Ni ban ma san mai yasa Mommy ta fada maka zan yi tafiyar nan ba, so nayi kawai ka ga bana nan".
Daddy ya kalleshi da harara cike da wasa, yace "oooh! Wato har kana gaya min saidai na ga ba ka nan ko? Ai shiyasa na hana, yanzun naga tsiya. Sannan tunda na sani yanzun, mutum ya fita ba da sani na ba, nasa security su lallasa min mutum., in kunne ya ji, gangan jiki ta tsira...".
Saif ya mike zaune, murya kamar zai yi kuka, yace, "haba Daddy!! Don Allah ka taimaka, wallahi na dade ban je excursion ba, kuma kamar ni ace in ba a dajin Yankari na Bauchi ba, ban san kowani daji mai dabbobi ba? Wallahi Daddy har kunyan fadi nake a gaban abokaina. Ina ta sa su suna daga tafiyar, ina cewa kimtse-kimtse nake yi, shiyasa ban sa date ba. Daddy please, kaji?".
Duk maganar da yake yi Daddy yana jin sa, jifa-jifa yana kurbar coffee din dake hannunsa. Haka Daddy yake kamar wani bakin bature.
Sai daya gama sannan ya kalleshi, a tausashe yace "Son kenan, halin tsaron kasar nan ne nake tsoro, shi yasa ba zan barka kaje ba. Yau kaji kidnapping, gobe kaji an kashe wane, jibi kaji yan boko haram. Ko zan barka sai kayi min alkawarin za ka kiyaye kanka don Allah, ka tayani tsaron kan ka. Kasan cewa bani da magaji sai kai, kagane ko?".Said yayi kasa da kai yana fadin, "ba fa a kasarnan bane tafiyar, shi yasa ma nima ban damu ba, saboda kasan kasashen waje sun fi mu nan Nigeria tsaro da sauransu. Ni dai don Allah ka barni inje Daddy, ni fa nasan yanda zan kare kaina yanzu tunda ba yaro bane ni, ni ka ma daina kirana son dan na girma".
Daddy yayi murmushi irin na attajirai mai cike da kwarjinin kudi, yace "shekaru ashirin da biyar har wasu shekaru ne? Ganinka nake kamar wani yaro dan shekara biyar. Ba komi, kuje, Allah Ya kiyaye hanya, Ya dawo min da aLkai lafiya. Amma kafin nan, ka bani lokaci, ku bari tafiyar sai gobe dan yanzu ka ga magriba na kokarin kawo kai".
Cikin murna da doki yake cewa "Daddy nagode, amma dama gobe zamu tafi da safe, don haka ba zan samu damar yi maka sallama ba".
Nan suka rungume juna cike da kauna irin ta da da mahaifi, daga nan ya tashi ya fita cike da murna yana kwala kiran sunan mahaifiyarshi, "Mom, i have a very good news for you...!".
Fitarshi ke da wuya, Alhaji Sadiq ya dauki waya ya kira bokanshi, Malam Kallah a waya. Bugu daya ya dauka cikin fara'a yana fadin, "Alhaji, dama yanzu nake son daga waya in kira ka".
Shi ma cikin fara'a yace "to Allah yasa lafiya dai?".
Maaman Kallah yace "ai Alhaji kasan cewa ba na kiranka sai da lafiya. Don da zarar na ga matsala, sai na maganceta nake kiranka".Cikin dariya mai cike da nishadi Alhaji Sadiq yace "lallai Kallah kaine Sadiq, kuma Sadiq shine kai. Menene yake faruwa? Fada min".
Malam Kallah yace "Wato Alhaji cikin duba dana yi jiya da dare, na gano kai da Saifullahi kuna takaddama akan wani abu, duk dadai baka gaya min ba..."
Alhaji Sadiq ya tari numfashinsa da cewa, "ai yanzu haka kiran da na maka don na yi maka bayani ne. Dan wajena, Saifullahi yake so ya bi abokanansa su je yawon bude ido, amma saboda halin tsaro na kasarnan shi yasa bana so ya je. Amma da ya matsa min, sai na amince mishi. Amma da yake tafiyar sai gobe, shi yasa nace bari in tuntubeka inji. Ka duba mana, in ka ga haske a cikin tafiyar, sai na barshi. Amma idan babu, sai in san yadda nayi nayi cancelling din tafiyar. Kamar yadda ka riga ka sani ne Malam, duk duniya bani da abun daya wuce Saifullahi. Shi kadai ne da na rak a duniya, magaji na, sai kanwarsa Zainab. Amma ita Zainab banI da matsala da ita, tunda ita mace ce, kuma bata da kiriniya kamar shi".
Malam Kallah yace "haka ne kam. Kuma gaskiyar magana Alhaji, ka barshi yayi tafiyar don na ga haske sosai a cikin tafiyar, shi yasa ma nace bari in kira ka in gaya maka!".
Alhaji yace "to madallah, Alhamdulillah, haka dama nake son ji. Don ni Malam Kallah wallahi ba abunda zaka gayamin naki yarda, duk sanda kuwa naki yarda sai naga ba daidai ba!".
Malam Kallah yayi dariya sosai, yace "kwarai kuwa Alhaji!". Daga haka suka yi sallama ya kashe wayarsa tare da komawa ya kishingida yana tunanin siyasa.
******
Alhaji Sadiq babban dan kasuwa ne, mazaunin garin Abuja ne. Iyayensa yan Kano ne, kasuwanci ne ya kai shi Abuja.
Alhaji Sadiq irin mutanen nanne da babu Allah sam a gabansu, daga boka sai Matarsa da yayansa yake darajawa da mutuntawa a rayuwarsa. Bai cirewa kowa hula ba. Amma in baka san shi ba, za ka dauka duk duniya babu wanda ya kai shi mutunci da iya daraja mutum.
Alhaji Sadiq dan jari hujjane, in yaga babu amfanin da za ka mishi, tsaf zai yaye ka.Yana da 'ya'ya biyu tak a duniya; Saifullahi (Saif) da Zainab ('yar auta).
'Ya'yan duk basu dauko halin mahaifansu ba.
Itama mommy kusan
halinsu daya da daddy, dama ance sai hali yazo daya ake zaman tare. Duk da cewa ita mommy bata bin bokayes, sannan tana tur da halin Alhaji Sadiq saboda bin bokayenshi. Hajiya Ummu-Salma (mommy), matace yar babban gida garin Kaduna. Mahaifinta shine tsohon Vice President na Nigeria, Alhaji Usman.Ana iya cewa don wannan dalilin NE Alhaji Sadiq ya aureta har ya samu daukaka a kasuwancinsa. Duk da Hajiya Salma ta san da haka, amma a hakan take son mijinta. Zata iya komi don farincikinsa da na 'Ya'yansu.
********
Bangaren Saif kuwa, cikin murna yake gayama momy, Daddy ya barshi ya tafi, gobe da safe zasu daga. Tayi murmushi tace "to flight din yaushe zaku bi?".
Cikin zumudi yace "haba mommy, wani flight! Ai dadin tafiya driving, mu kanmu bamu san inda zamu tsaya ba, amma zamu cika mai a mota sannan mu ajiye extra sosai".Tayi shiru chan tace "don Allah Saifullahi ka kula da hanya, albarkata tana tare da kai a koda yaushe. ku nawa zaku tafi?".
Yace "mu hudu ne, Sani, Nazir, da Ja'afar abokaina". Ta Dan lankwasa kai tare da cewa "fine my dear, Allah kiyaye hanya. A dauko mana hotuna sosai, kaji?".
Ya juya yana tafiya yana cewa "sosai mom, ai dole ko don ki gani. I love u, bye, da safe zan fita ba zan samu damar miki sallama ba".
Yana jiyota tana cewa "OK, bye-bye....!!".
Kada ka/ki manta da,
Vote
Comment
Following
Dan nuna yabawa nagode🤝

YOU ARE READING
Kaine Rayuwata😭❤❤ Complete
Romancelabarin na 'kunshe da Yaudara, Kiyayya, Soyayya, Tausayi, rikon Amana, Nishadi, Rudani, Juriya, Kaddara, Son abun duniya,......... A takaice! littafin na kulle da sako dan nishadantar, wa'azantar da mai karatu. In Summary........ Saifullahi (Saif)...