Kaine Rayuwata❤😭
Written By Najaatu shehu naira
FKD Fans Writers 《《 16 》》
Saif yakalleta yace "wow, Gimbiya kinmin daidai,".
Nazir dake tafi, yasunkuya ya dago Danliti, yana dariyar mugunta yace "ya haka abokina? kasan abunda kakeyi kuwa? Iya rashin kunyar naka kenan daman".
Zinaru tadanja baya kamar mai nazari, idanunta suka cika da kwalla tadago kai, takalli Danliti tace "kayi hakuri, bawai nayi niyan cin zarafinka bane, kayafemin....Saif yadawo gefenta yace "wato kingama cin zali, kinkoma kin marairaice ko? adai dungayi ana tsoran Allah Gimbiya,".
Nandanan kwallan sukahau bin fuskanta,
Yamatso dasauri yace "haba ke Sarkin kuku, wasa nake maki, aini kinburgeni dankinmin maganinsa, next time duk wanda ya kara yimaki raini, karki jira, ki chachchake shi".Yagoge hawayen dake fuskarta da tafin hannunsa yace "ya'isa haka kinji".
Sani da Jafar, sheda sukajeyi wajan Danliti,
Jafar ke sokomai tambaya yace "Danliti dama kasantane?".
Danliti Yadago kai, fuska cike da tsoro yace "wai Gimbiya? To waye baisan Gimbiyar Rano ba? Dama nidai bansanta a ido ba, amma babu wanda baisan labarin Gimbiya ba, kyanta da izzar mulki dazaran ta yanke hukunci ko Sarki bai sa'bawa,
Aini Ku zantambaya, su waye ku? A'inama kuka hadu da ita? don nadaisan Sarki ita kadai yahaifa,".Yana magana ko hadiye yawuh bayayi yace "Babanta fa shike mulkan har Sarkin kauyenmu, mu kauyenmu karamin kauyene acikin garin Rano, amma mu munada musulmai sosai, itakuma garin Gimbiya maguzawane basa Sallah,".
Jafar yace "hmmm Danliti kenan, shine dan tsoro nandanan kazube kamar zakayi sujjada? Lalle kacika matsoraci".
Danliti yamaida kanshi gun Jafar yace "tsorofa kace!? To wlh inma bakasaniba na fad'ama mutanan nan babu Allah aransu, kasan wlh da acikin garin Rano na aikata laifinnan dahar aka koreni, toh da wlh yanzu sun kasheni Malam".Can kuma yayi shuru kamar maitunani, yakallah Nazir yace "toh amma maigimbiya take anan tare daku? nifa abun mamaki yake ban, kumamafa dubi yadda tabari Yarima yadunga jibgarta, dubima shigarta gaskiya akwai matsala, inbaccin nasan labarin yanda ake fad'in kyanta gasky bazan yarda itabace,".
Nazir ya dafa kafadarshi yace "infa baka yarda ita bace, mukira maka ita ka tambayeta,"
Danliti yazaro ido waje yana girgiza kai yace "rufamin asiri kar a tsireni,"
Duk sukai murmushi, Sani dai tunda ake maganarnan baice uffanba,
Danliti cikin rawar jiki yabar gunsu yakoma gun Saif da Zinaru dake gefe, tana kwashe kifi,
Yana'isa ya amshe kifayen dake hannunta yace " Ranki shidade kibari Ni na'karasa sauran, bari naje na naimo kara aha'da wuta".Ta'dago kai tagirgiza kai tace "a'a kayi hakuri kabari nagode",
Zaiyi magana Saif yace "axa ke ba'a haka",
Ya karba kifin daga hannunta, ya mikama Danliti yace "gashi, dan Allah kayi sauri dan musamu muwuce,"
Ya karba jiki narawa yace "to angama insha Allah"
Takallah Saif tace "ni banaso gsky, gargadin Babana yaimin dole in 'kas'kantar da kaina aduk inda na tsinci kaina, karkasamin girman kai kutafi kubarni da wahala, shima Danliti nabayyana masa koni wacece dan nasamu yarabu danine".Duk maganar datake Saif nakallon bakinta da tsabar 'kan'kanta kamar badaga bakinta maganar ke futaba, yayi murmushi kamar saukar aradu yace "maiyasa bakiyi Sallah ba? gashi duk munyi".
Takauda kai tazum'buro baki tace "ni ba musulma bace",Nazir daga naisa yana gangarowa yace "kajika da naiman zance, kasanfa bata sallah toh meye na tambayar?"
Sani yace "wai maiyasa duk wani abun arziki bakaso Nazir? Burin duk wani musulmi na kwarai, yaga ya tallata addininsa ako ina,".
Duk suka 'karaso Jafar yazo gabanta yana murmushi yace "keda aka tsinceki, kika sani ko asalin Iyayen naki ma musulmai ne, koma badan hakaba dole kiyi addini kodan kisami haske aduk abunda kikasa gaba,"
![](https://img.wattpad.com/cover/173403386-288-k686329.jpg)
YOU ARE READING
Kaine Rayuwata😭❤❤ Complete
Romancelabarin na 'kunshe da Yaudara, Kiyayya, Soyayya, Tausayi, rikon Amana, Nishadi, Rudani, Juriya, Kaddara, Son abun duniya,......... A takaice! littafin na kulle da sako dan nishadantar, wa'azantar da mai karatu. In Summary........ Saifullahi (Saif)...