Kaine Rayuwata😭😭❤
Written By Najaatu shehu naira
FKD Fans Writers 《《 11 》》
Wattpad; Najaatu_naira
Ta dur'kusa gabansa tana kuka tace "tagudu ranka shidade, naduba ko ina bata".
Yari'ko hannuta dasauri yace "tashi muje muduba".
nan yabar dogarawan tsaye bakin 'kofa.
dakin Zinaru yashiga yaduba bata, sukayo waje yaduba bata, Jakadiya na 'ko'karin shigowa yatareta yace "yauwa zonan mazza-mazza kije kisanar aduba Gimbiyata tako'ina, bata!"
Rike baki tayi tazaro ido tace "Gimbiya kuma?!.
Ya amsa da sauri "Eh mazza je kisanar a dubata". Tafita dasauri.
Sarki yakallah Zubaida yace "ya akayi kikabari tafita kema?",
Idojajir duk hawaye tace "wlh nabarta tana barci"
Yakauda kai yace "hmmmm sakaci dai"...Jin labarin Gimbiya ta 'bata,
Dauda yahada tawagarshi, su biyar da dawakai sukadau hanya sunyi nisa ganin babu alamarta yaja yatsaya yace "wlh saceta sukazoyi bakomai ba", yakalle abokan tafiyar yace "kai duk wanda ya nemomin Gimbiya, zanbashi ra'kuma biyu, sannan inkuka kama ba'kinnan ku tabbatar kun kashesu, karkubar kodaya rai"... sukace "toh ranka yadade".
suka lula cikin daji nemanta,.............********
Chan ta 'kofar baya Gimbiya tashigo cikin gida,
Zubaida dake jikin Sarki takasa tsayuwa da 'kafarta, tayi zumbur tamike dasauri ta tarota tari'ko hannunta tahau kakkabe jikinta tana fadin "lafiyanki kalau? ba'abunda yasameki Gimbiya,?"
Ta gyada kai alamar "eh"
Tasaki ajiyar zuciya ta rungumeta,
Sarki dake gefe yayi murmushi yagoge kwalla aranshi yace "lalle Zubaida akwai aiki ja'a gabanta".....
Yakallah Zinaru Yace "Gimbiya ina kikaje ne haka?"
Ta sab dakai tace "naje bayan garine na dudduba",
Yasaki ajiyayar zuciya yakalleta yace "to sannu inzaki fita kidunga sanarda Mamanki, Ni zanfita yanzu ana jirana a fada", yabarsu,
Zubaida narungume da Zinaru kamar za'a kwace ta,.Sarki yakalli jama'an gari yace "to jama'ah anga Gimbiya dama bayan gari taje Sarauniya ta tsorota ta tada hankalinta tadauka tatafine, duba da yaune dama Gimbiya zata wuce!,.
Yakara daga murya yace "inaso nayi amfani da wannan dama na sanardaku, daga kan Gimbiya dokar kauyennan zata chanza".
Fada ta dauka da surutu kowa sai tsokaci,
Sarki yadaga hannu yace "ya'isa ku tsaya ku fahimceni, bawai zan tursasa ku bane, amma saidai jawabina zaima kowa dadi acikinku",
Sukayi shuru hankalin kowa yadawo gun Sarki,
Yamike daga kan kujera yace "daga yau, ba'ko agarinnan dole a darajashi akarbeshi hannu bibbiyu kamar dan gari, sannan addini kowani iri inmutun yaga daman yin abunshi yaje yayi, babu ruwan kowa da addininka".Suka hau tsalle dan murna!,
Ganin farincikin dake kan fuskokinsu Sarki yayi nadamar rashinsa sauke dokar tun farko,.
Waziri dake gefe yace "amma Ranka yadade, banda Gimbiya acikin dokannan nan ko?"
Sarki yakalleshi cikin takaici yace "ainace daga kan Gimbiya, dannayi adalci agunku dasauran mutanan gari
Gimbiya anjima zata wuce tare da Sarkin Daji intashiga cikin gari, saiya barta yadawo",
Ba'ki kuma da suka tafi abarsu suwuce, bansa kowa ya naimaisu ba!!",
Waziri yakalle shi yace "to ranka yadade hukuncin su fa?"
Yajuyo ya kallesa cikin tsana yace "Inka gansu! kayimasu",
Yaja tsaki yabar Fadan,.
Gabadaya mutanan gari sunji dadin hukuncin Sarki, hakan yaxkara dawomai da martabansa da 'kima wajansu,.
Wasuma harda jajantamai kan tafiyar Gimbiya.......Gida Sarki yakoma ya kwanta a sassansa, yagaji sosai ga damuwar dake damunsa na tafiyar Gimbiya tasakar masa ciwon kai.
*******
Dauda dayaga alamun babu Gimbiya babu alamarta, ya yanke shawarar dawowa gida, ahanya ya tambaya wasu 'yanmata ko Gimbiya tadawo?,
Suka amsa cike da fara'a "eh ranka yadade".Murna ta lullube shi, yaja doki da gudu yashiga cikin gida zaiyi 'bangaran Gimbiya!.
Waziri nazaune yana zaman jiran shigowarsa, yayi wuff ya janyoshi wata 'yar lungu murya 'kasa-'kasa yace "Ashe kai bakada hankali?
Inakaje kana cikin doka? Sokake a sami abun fa'da akanka?
burina nason kazama Sarki kakeso ka tarwatsa".
Dauda yakalli mahaifinshi cikin sanyin rai yace "Baba wlh ina matukar son Gimbiya,
bazan iya ruyuwa babu ita",.
Waziri ya dakamai tsawa yace "dakata sakaran banza,
baccin bata takai, ba kaunarka takeba kowa yasan yanda ka dauketa bahaka ta daukeka ba",
Dauda yakallah Waziri ido narai-narai yace "nima nasani Baba! amma sonda nake mata ya'isa mubiyun, basai tasoni zan sotaba Baba, nasan kai kafara tusamin Son Zinaru araina, amma yanzun bazan iya cireta ba",.
Yadur'kusa 'kasa kan gwaiwarsa murya narawa yace "Ka taimakeni Baba, dan Allah karkabar Zinaru ta tafi,
Itace Rayuwata!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!"
Waziri ya tureshi yace "wallh albasa batayi halin ruwa ba, sakarai kawae ga hanya, kaje Ubanta yasa a kamaka tunda kamanta kana dakin ajiya, kunnan 'kashi yasa kabaro, toh kuwa inkabari Sarki yasan anganka cikin gari zakagane kurenka".
YOU ARE READING
Kaine Rayuwata😭❤❤ Complete
Romancelabarin na 'kunshe da Yaudara, Kiyayya, Soyayya, Tausayi, rikon Amana, Nishadi, Rudani, Juriya, Kaddara, Son abun duniya,......... A takaice! littafin na kulle da sako dan nishadantar, wa'azantar da mai karatu. In Summary........ Saifullahi (Saif)...