Kaine Rayuwata😭❤❤
By: Najaatu shehu naira
FKD Fans Writers 《《 48 》》
https://www.facebook.com/groups/459234504875663/
Dakinshi Saif yanufa kaitsaya
Ya tadda Zinaru azaune kan Sofa tana 'karema 'dakin kallo,
Murmushi ya sakarmata cikin nishadi yaga ta sakarmai harara cikin wani irin kallon tuhuma,
Ya langwa'be fuska yarike kunne yai narai-narai da fuska yace "am sorry, kiyi hakuri My baby",
Kauda fuska tayi tai kini-kini darai tace "dama kashirya rabuwa danine, ko kyallin hotona daya babu adakinnan, zubarwa kayi?"
Dasauri ya girgiza kai yace "a'a"
Ta sake 'bata rai tace "toh ina suke", jakar hannunsa dake gefe yadauko ya zazzage, ya kallah kwayar idonta yace "gasu,"
Kasa bude baki tayi, sai kallo maicike da kauna, muradi da kewa,
Ya bu'de faffadan kirjinsa yace "nasan kinaji kamarki rungumeni ko?",
Ta dagamai gira tana murmushi,
Ya kashe mata ido yace "toh zo",
Da gudu tafada kirjinshi rungumeshi,.
Yafada kan gado ta baya yana rungume da ita yasaki ajiyar zuciya,
Azahiri yafurta Alhamdulillah........*************
Karfe tara na safe bayan sungama breakfast,
Nazeef yakallah Umma cikin damuwa kamar zaiyi magana ya kauda fuska,
Sarai Ummah ta karanci halin 'Danta tasan yanacikin damuwa,
Cikin sanyin murya mai tattare da nutsuwa tace "Nazeefina mainene?"
Ya girgiza kai cike da damuwa yace "bakomai Ummah",
Batai 'kasa agwuiwaba tace "Nazeef nafahimci kwanannan kanacikin damuwa kuma kaki ka gayamin maike damunka, nifa Mahaifiyarkace inbaka gayamin damuwarka ba, baka da wanda yafini ko bikinnan bakawani motsi lokaci harya 'kure",
Fuska a yamutse kamar zaisa kuka yace "Mommy Zinaru, ni inaganin kamar batani takeba, tun ina hakuri inaganin zata chanza, ni walh harta futa raina sabida 'dabi'un da take nunamin, bani bane a gabanta,"
Umma tayi shuru na'dan mintina kan tace "Nazeef komai kagani arayuwa da hakuri ake binshi, ka'kara hakuri kwana nawa dududu yarage, ni akwatin nema nakeso a,,,,,,,,,,,,,",
Girgiza kan dataga yanayi yasa ta saurara,
Ya'dago kai idanu nandanan sunkada sunyi jajir yace "nasan tunfarko bata sona, amma narasa dalilin dayasa nakasa cireta raina dukda nasan bazata taba sona ba ko zatasoni banan kusaba, Ummah dan Allah kiban shawara",
Yanda yayi maganar yasa ta tausayamai kwarai,
Ta dafa kafadarshi tayi 'kasa da muryanta tace "Nazeefi maganar gaskiya nayi mamakin jin Zinaru ta tsaida kai, kuma bakomai yasaba illah Zinaru natausayin Meenal dalilin kenan dayasa zata aureka, amma maganr gaskiya shi aure ba abun wasa bane barin inbabu soyayya, kaima nasan shakuwace kawai da kaunar dake tsakaninta da Meenal yasa kaima kasata arai,"
Ta'kara tausasa murya cikin rarrashi tace "da zaka hakura Nazeefina dayafi inyaso Allah yahadaka da wacce kaima zata kaunaceka",
Shuru yayi nadan mintina kanya 'dago kai suka hada ido yalumshe yace "ni wlh nahakura, tunjiya naso ingayamata cikin dokin zuciya har nakira-nakira wayan tadaina shiga, inaga zantashi intafi dakaina inmata bayani cikin natsuwa yadda zata fahimta tunda yanzuma Meenal tarage 'kiuya, tana yarda dakowa agidannan har inasamun damar fita aiki",
Bakaramin dadin maganar Ummah tajiba,
Ta'kuramai ido tanajin dadin sauraransa kan tace "a'a tunda kasauko yanzu zakatashi katafi, kaga dududu saura kwana uku bikinnan, karsuita jira sannan suji labari mara dadi kaga badadi,, ni kaina yanzu zankira Alhaji Sadiq inmai bayani",
Ya gyada mata kai yayi murmushi yana cizan le'be yace "Ummah nagode", kanshi tashafa tana girgiza kai tace "Allah maka albarka ya'kara nitsarmin dakai, kaje karage gashinnan yayi yawa",
Ya gyadakai yamike yace "toh Mommy saina dawo, jirgi zanje nahau kawai, idan Meenal tatashi muyi video call",
"Toh Allah kiyaye hanya" tace,
tayi shiru na dan mintina tana binshi da kallo, azahiri tafurta "Allah maishiryawa,
Allah nagodema"....**********
Zinaru nazaune da towel daure akan kirji anamata gyaran jiki,
Fatannan ta'kara fari tsnasheki kamar danyan jiki,
Saif nagefe yayi daram idonshi nakai
suna hira da Aunty Jiddah harda shewa, anyi-anyi dashi yafita ya'ki,
Aran Zinaru tayi murmushi tana tunanin sanda ko zataga fara'ar Aunty jiddah saidai ya'ke,
Amma daga sanda ta amince da Auren Saif babu wanda bainannan da ita agidan harda Zainab da take nata hidimar,

YOU ARE READING
Kaine Rayuwata😭❤❤ Complete
Roman d'amourlabarin na 'kunshe da Yaudara, Kiyayya, Soyayya, Tausayi, rikon Amana, Nishadi, Rudani, Juriya, Kaddara, Son abun duniya,......... A takaice! littafin na kulle da sako dan nishadantar, wa'azantar da mai karatu. In Summary........ Saifullahi (Saif)...