Kaine Rayuwata 12

1.5K 121 1
                                    

Kaine Rayuwata😭😭❤

By; najaatu shehu naira

FKD Fans Writers 《《 12 》》

Rana daya da wuni daya Daddy ya zabge kamar yai fama da cutar ajali,
Inbaka saniba ka'dauka an aikomai da sanarwan mutuwar Saif ne,
Mommy tami'ke ta kalleshi tace "Alhj tagumifa banaka bane, katashi ka naimomin d'ana duk inda yake dan kai ka bashi damar tafiyar",
Ta juya kai taja guntun tsaki tace "Karka maidani jahila, kaikasan nasanka kamar yunwar cikina,
bayadda zakabar Saif yayi tafiyarnan batare da kakira jahilin bokanka Kallah ba, dan haka katashi kasan abunyi nagayama kenan",
Ta fashe da kuka tace "haba dan Allah, yau kwana biyu kenan ana aikin abu d'aya",

Zainab nazaune jingine jikin cushion tana tunanin ko wani hali Yayanta keciki yanzun, takalli Iyayen nata dake hayaniya ta girgiza kai cikin takaici tace "nizan koma 'daki if u get any information u let me knw",.
Batajira amsarsu ba tafice.
Mommy tayun'kura tace "bari ina wayata ma",.
Ya kalleta yace "wazaki kira kuma awannan halin da muke ciki? Hajiya Salma karmu bari yanwaje suji labarin nanfa, they will take advantage of us, think about it,
ta dagamai hannu tace "Malam nasan abunda nakeyi, number commissioner nake kira"
harta gama ringing bai 'dagaba,
Tajuya tace "toh koma mainene lets it be, wlh ko arzikina zaikare kan d'ana, koma mai zaifaru nidai yadawo gida, kai gwamma kai koyanzun ka 'kara aure wata zata haifama,
nikam subiyu kachal Allah yabani masumin addu'ah".....................
Daddy yakalleta ata'kaice yace "nidai Salma zanso naga hankalinki wataran",..
Ya lallubi wayarsa yakira Manager layin sadarwa na MTN branch dinsu dake Abuja......

*************
Saif yakaimai Yarima tokari, yakoma da baya tanga-tanga samarin dake gurin suka rikeshi sunafadin "Yarima bakaji ciwoba ko?".
Yafuncike yatsaya, yana kallon Saif yana muzurai,
Chanyaji lema na gangaromai gefen baki, ya ta'ba bakin da yatsa yaga jini,
ya zabura ya cakumi Saif,
Jafar da Sani suka shiga tsakiya suna bada hakuri,

Saif ya kalleshi yace "banhana ka dukana ba, ni namijine! amma bazaka doke mace ina kallo na kyaleka ba, kafin yarufe baki,
Yarima yasa hannu ya kifamai mari yace "matarka ce inna doketa!? Wlh zakasan ka ta'bani a garinnan",.

Ya janyo hannun Zinaru data kankame bayan Saif yace "zomuje",
Saif yari tsintsiyar hannunta ya kalle fuskarta data tamke idonta dan tsoro
yace "ke bude idonki",
takara tamkewa, ya buga mata tsawa yace "kinaji na?"
Ta bude ido tsna rawar jiki yace "kinyarda kibishi?"
Ta tsaya tayi shuru tana kallon Yarima a tsorace.

Kafin tabada amsa Nazir yajanye hannun Saif yace "kabari kawai, muwuce Saif",.
Yarima ya kalli Saif yace "waikai uban wanene ma? Ko dayake zanji dakai daga baya, kujirani in ajeta indawo duk sainayi maganink",

Dantani dake gefe kamar an tambayeshi yace "Haba Yarima ya kake haka "Kanwarshi ce fa",
Sani da Jafar dake tsaye cirko-ciko sukace "Eh eh Yayanta ne",
Nazir aranshi yace "lalle bakusan wannan 'Yarba, yanzunnan zatabaku kunya".........

Yarima ya kalleta cikin zafin rai yace "ke dagaske Yayanki ne?"
Tagyada kai dasauri jiki na rawa tace "eh hakane",.
Yarima yad'an sosa keya, kyace bashike rashin mutuncinba yace "tooo toooo ai bansani bane".
Cike da fara'a a fuskarshi yace "lalle dara taci gida, aiii gama kama nan!!!, dan Allah kuyi hakuri".
Yadawo tsakiyarsu yace "muje gida ayi magana, tunda dai yanzun wasan Dandalinma bazai yuhba".

Nazir yayi sauri yace "a'a mu munada masaukinmu gidan Ladan,
adai bari gobe muyi magana amma yanzun zamu wuce mukwanta dare yayi",.
Yarima yagyada kai yace "toh amma ita kubarmin ita, dan Mahaifina yace gobe zai 'daura mana Aure!, saikuma kuzo da safen",.

Take Jafar yace "ai ba haka akeyiba, aure ai baiyuhwa saida magabatan yarinya",.
Duk suka amsa "kwarai kuwa bazai yuhba kabarta gunmu yaso da safe masa aimana isoo gidan Sarkin, kaji?" Jafar ke maganar yana kallon Yarima.
Yarima tsaya yayi jimm kamar mainazari, ganin sunfishi gaskiya a maganar yace "toh badamuwa Allah kaimu goben, aiduk dayane yauda goben awajan Allah".

Kaine Rayuwata😭❤❤ CompleteWhere stories live. Discover now