Kaine Rayuwata😭❤❤
Written by: Najaatu shehu naira
FKD Fans Writers 《《 30 》》
Tana fita nantake ya dauki waya yakira "Malam Kallah"...
Dukda andau tsawan lokaci Daddy baikira Kallahba dan har a lokacin gani yake Kallah ne silan tashin hankalin dayake ciki,.
Bugu daya Malam Kallah ya dauka cikin gandauki yace "Alhajin Allah"
Ciki-ciki Daddy ya amsa, yai kini-kini da fuska kamar Malam Kallah nagabanshi yace "inajinka Kallah"
Jin haka yasa Kallah yafahimci akwai damuwa yace "Lafiya Alhaji?".
Shuru Daddy yaimai,
Ganin Alhaji yayi banza dashi yace "Alhaji wallahi kullum kan aikinka nake ba dare ba rana, duk sanda zan buga 'kasa magana 'dayace, haske da alkhairy lamarin tsakaninku da Yarinyarnan, daidai da rana daya banta'ba ganin akasin hakaba Alhaji, abin al'ajabi yanzu saidai mujira muga ikon Allah muga maike 'kunshe cikin lamarin,"
"Al'ajab din mai? Nace Al'ajabin me Kallah?" Daddy yafada cikin tsawa,
"Kallah Idan hannunka yafara sanyine ka gayamin na chanza Malami kwararre wanda zai'iyamin aiki akan lokaci, rabasu kawae dazakai ya gagareka, Kallah common ka rabata da 'Dana ka kasa, kasa shiririta a zancan" masifar da Daddy yake kamar zai aribaki yasa Kallah yace "Alhaji ni zan'iya mata kurciya ta rabu daku inta kama, amma sar'kar'ken lamari irin wannan dahar mutanan mu suka kasa samun gamshashshan wuja, munfisan ajira ajinkirta Alhaji"
Daddy yayi tsaki yace "basai kamata kurciyaba idan inaso inkoreta zankoreta dakaina, nidai inason hankalin danwajena Saifullahi yabar kanta, yadaina rawan jiki akanta, yabar bijirema maganata akan tsintacciyar magen nan".
Malam Kallah yace "toh Alhaji amma kuma saikusa kula, domin datse kauna ba 'karamin aiki bane sai munbi ahankali"
"Zanturoma kudi anjima ta account" Daddy yafada had'i da gimtse (hangup) kiran, yana huci aranshi yace "yaro mankaza inbanda abun Son hada zuria da Alhaji Sa'id fa (CBN governor) ai abun Saif alfarma ne.
Nandai ya zauna ya 'kulla wannan ya kwanche wance yana 'yan tunane-tunane ganin barci na shirin daukansa azahiri yafurta "bari na kira Son naji daga gareshi"...Bugu daya Saif ya dauka yace "na'am Daddy," dukda alokacin Alhaji Sadiq yasa tashin hankali da rashin adalci agaba, jin muryan dan nashi daya tilo yaimai dadi yayi yar ajiyar zuciya yace "inason ganinka yanzun" toh kawai Saif yace ya kashe wayar,.
Yakallah Zinaru data tasa littafin "easy ways to learn ENGLISH agaba" shikuma yanama Zainab Lesson akan Jamb din da takeso tazana kafin Malamin Lesson dinda ya naima musu yazo cikin satin da za'ashiga yace "Daddy na kirana, daganan zanje na kwanta Miss english saida safe",
Jin sunan yasa Zainab sakin dariya mai sauti tace "Yaya karfa sunan nan yabita"
Zinaru ta zum'buro baki tace "ohoh tun rannan yafara cemin, kuma nace banaso"
Saif yadaga gira yace "ah toh, nadaina saida safe, ayi karatu akoya, akoya mana" murmushi ta sakar masa yabar daki.Hadiza ta kawo mata takardan da nufin takaranta lokacin hutun karshen mako. (During weekend),
Da dukkan alama takardan na taimakawa domin Zinaru ta ri'kesa kamar ibada, badare ba rana.Dakin Daddy yawuce katsaye yatarar dashi yana kallon labaran dare na aljazeera news,.
Ganinsa Daddy yakashe TV ya gimtse fuska yaimai nuni dahannu yace "sama guri ka zauna" hakan bai daga hankalin Saif ba dan shi yama mance yaushe rabonda yaga fara'ar Daddy gwangwan, tunkan zuwan Zinaru.
Ya naimi guri ya zauna ya tankwashe 'kafa,.
Daddy ya fuskanceshi cikin nutsuwa yace "Son ina maganarmu ta kwana?"
'Dib yaji kamar ansaukemai gajiya nandanan kirjinsa yahau dukan uku-uku cikin kasalalliyar murya yace "Daddy wacce kenan?",
Harara Daddy ya jefaishi dashi yace "Son sokake ka maidani mutumin banza ko ya? Wannan Yarinya datazo nan Jamila zuwa yanzu wani hukunci ka yanke akan Auranku?"
Saif ya had'a girar sama data 'kasa dukda yasan maganar dazai furta bazaima Daddy dadi ba yace "Gsky Daddy kumabar maganarnan, ni Yarinyarnan bataimin ba, bata da tarbiya kwata-kwata batasan ki..........."
"Yimin shuru mutumin banza" Daddy yafada yana huci yace "Wallah Son 'karya kake kace mu bamu isa musaka ko mu hanaka ba, tunkan naima iyayen Yarinyarnan magana, nabaka dama nace inkanada wacce kakeso kayi magana kace a'a toh sai yanzu zaka maidamu 'kananun mutane, kasan bazai yuhba"
'Kololuwan ma'kura Daddy yakai Saif danhaka yace "toh fine Daddy kaban lokaci kadan zanfitar da wacce nakeso"
Kai Daddy ya girgiza yace "innna innnna ai aikin gama ya gama, kashirya auranka nanda wata daya (1month) bayan biki da kwana daya kud'aga Morocco zansiya hannin jari a Merced Benz chan, inaso katsaya kakula da ayyukan chan".
Ru'ku'kui da 'kunar da zuciyar Saif keyi yasa yakasa magana, dibbbb kansa yayi baice uffanba,
Daddy yace "kana jina ko?, ita kuma wancan 'yar da ka tsinto saika maida ita inda ka daukota kan lokacin, domin bansan tarbiyantaba danhaka bazanbarta itakadai da Zainab agida ba, gwanma ka tattarata ka maida ita inda tafito"
Zuwa lokacin Daddy yagama kai Saif bango ya dagokai, idanunsa sunkada zunyi jajir, murya na sartsewa yace "ba inda zata Daddy, 'kafana 'kafar Gimbiya, Amana tace bata da wanda yafini ayanzu danhaka bazan mata butulciba".
"What!!!!!!" Daddy yafada, yami'ke ya zare dan glashin (eye goggle) dake fuskanshi yace "Saif ni kake mayarma magana?" Kan Saif na 'kasa yace "Zanje dai Morocco amma banyarda kace kai zaka za'bamin macen aureba Daddy wannan hurumin banaka bane".
Turus Daddy ya koma yazauna idanunsa nakan Saif yakasa gasganta abunda kunnansa ke sauraro,
Nan ya saisaita murya yana 'ko'karin daidaita tsayuwar numfashinsa ya kallah Saif yace "Saifullahi"
Saif yadago suka hada ido,
Yanayinsa kwarai yafara furgita Daddy Idanunsa sunkunkunburo kwallah na dirara,
ganin halin da 'Dannashi yashiga cikin rarrashi yace "Saifullahi ni mahaifinkane bazan taba cutar dakaiba, yau da 'yar gurin 'Dan'uwana Farouq.................. nanan da ita dama mukai burin hada Auranka, amma Allah yayi ikonsa bata, toh naga itama Jamila 'yar'uwarka ce meye laifinta, inma wani abu takeyi da bakaso saika gaya mata tadaina, tunda tanasonka ai kwarai zata bari, kokuwa Son?!"
Bib-biyu Saif ke ganin Daddy zuciyarsa naturnu'ku'ku yace "Daddy bafa na sonta kawae".
Tashi kafita Daddy yafada cikin tsawa ya kauda fuska, zuwa lokacin shima kanshi yafara daukan chargy.
YOU ARE READING
Kaine Rayuwata😭❤❤ Complete
Romancelabarin na 'kunshe da Yaudara, Kiyayya, Soyayya, Tausayi, rikon Amana, Nishadi, Rudani, Juriya, Kaddara, Son abun duniya,......... A takaice! littafin na kulle da sako dan nishadantar, wa'azantar da mai karatu. In Summary........ Saifullahi (Saif)...