Kaine Rayuwata😭❤❤
Written By Najaatu shehu naira
FKD Fans Writers 《《 07 》》
Dauda dake tsaye ya samu waje ya zauna dasauri,.
Sarki da tawagarshi suka shigo dakin,
Da gudu Zinaru tatashi ta rungeme shi tana kuka yana goge mata hawaye da rigarsa,
Ganinta ahaka ya'kara dagamai hankali yace "ya'isa Gimbiyata, kiyi shuru gani nazo",
Wata zazzafar kwalla ta gangaro kan kuncinsa, tayi sauri ta goge mai ta'dan 'ban'bare jikinta daga nashi tare da rike hannunsa suna kallan juna,
Lokaci daya kewar 'Yarsa yasa jikinshi yayi la'asar,
Duk wanda ke dakin saida jikinsa yayi sanyi dan tausayawa,.Nan danan mutanan Sarki suka had'a fada, tare da fadawan da yazo dasu,
ciki harda Wazirin Sarki agefe,
wanda tun sanda yazo duk abunda ake idonsa na'kas,.
Dakin yayi tsit,
Sarki yayi shuru kamar mai nazari ya tsurama Nazir da Saif ido dake zaune opposite dinsa, ganin haka sukayi 'kas dakai,.
Yayi gyaran murya ya kallah fadawansa yace "sune matasa biyun da sukazo sace Gimbiyata?"
"eh ranka shidade" suka amsaSaif da Nazir suka mike arikice tare da dafa kirji suna zaro ido harsuna hada baki "SATA KUMA!!!?"
Suka kalleta alamun tatayasu yin bayani, fuskarsu tattare take da firgice, mamaki hadi da rudani,
Basu karayaba saida Zinaru Ta kauda kai tajuya fuskarta,.Wani zabgegen dogari yatashi cikin zafin nama ya zuzzuga masu dorina yace "ku natsu kuyi ladabi gaban Sarki kuke",
Kanya rufe baki Saif da Nazir sunyi zube suna rike baya, Nazir na aiyana "lalle yau dayazo da bindiga, ba'abunda zaisa bai harbe azzaluman nan ba".Zinaru takallah Babanta saikuma tasab dakai.
Yafahimci tanasan magana yace "inkinada magana kiyi, ai danke mukazo nan",
Tadubi Sarki tace "ranka yadade, basusan dokar kauyen nan ba'a magana afada har sai anbada dama ba,"
Ta kalla Saif da Nazir tace "dan tsira da lafiyarku ku kiyaye, karku kai kanku ga halaka".Sarki ya kalli Waziri yace "daga ganin wa'dannan ba'kine, sasu akayi su sace Gimbiya, idan antuhumesu angano wani Sarkin daya turosu toh kuyi masu azaba, daganan ku kashesu a aikamai da kawunansu, umarnina ne".
Yakallah Dauda yace ma dogarai, "shikuma wannan kukamashi kutamke amai bulala dari uku sabida karya doka, yatake doka yazo gun Gimbiya batare da tsoran hukunci ba",.
Waziri yataso da zafin rai yace "Sarki Dauda nefa dan gidana" ,
Sarki ya dagamai hannu yace, "doka nakan kowa danhaka, dole ya karba hukuncinsa".
Dole Waziri yayi shuru badan ranshi yaso ba,.Sarki yakalleta yace "mainene gaskiyar lamari Gimbiyata? Naga duk damuwa tabaiyana a fuskarki".
Ta kalleshi cikin dimauta dajin hukuncin da yayanke masu tace "ranka yadade, narantse taimakona sukaso yi,
Sundauka saceni akayi, sabida tsangwama da kyara da Dogan dogari da Zangalo sukemin",....... ......... .Sarkin yayi jimmm dajin furucinta, daga bisani yakallesu yace "kumin bayani maiya kawoku nan, sa'annan maikuke a dokar daji?",
Saif yayi ajiyar zuciya tareda Sallama, Nazir kadai ya amsa,
Yaci gaba da bayani cikin zullumi yace "Wallahi Allah yaga niyanmu ba munzo sace ta bane",
Ya nuna Zinaru dayatsa yace "kekinsan taimakon ki mukasoyi, abunma da yakawomu dajinnan kuwa yawon bude ido mukazo, kayarda damu, mubama 'yan 'kasarnan bane daga Nigeria mukazo".Dauda dake gefe yana cije-cije yajuyo yace "karya suke Ranka shidade, nazo nasamu suna kokwowa da Gimbiya suna 'ko'karin gudu da'ita, harma garinson nataimaka mata nafito da wuka suka fisge, wannan mugun",
Ya nuna Saif da yatsa yace "ya yanketa a gefen ciki, danma bataji wani rauni sosai ba".Ba Saif da Nazir da bakinsu ke budeba, Zinaru ma saida tabishi da kallo tana mamakin karya irinta Dauda,
Ya yazo gunta za'daga lifayarta yanunama Sarki ciwon,
Ta tureshi gefe cikin tsana, tamatsa da baya."Idan akwai abunda Zinaru ta tsana baiwuci karyaba,".
Sarki dajin haka yasa dogarai su kama Saif da Nazir su fiddasu waje yace "sannan ku tamke masu hannu cikin rana har saina fito,.
Wasu manyan dogarai sukataso sukai waje fuuuu dasu,,,*******
Sani da Jafar gani basauki kayarda lalle sun'bace adokar dajin, sungaji da lalubensu sukayi bakin rafi koda Allah zaisa sujisu cikin mutane,
dazuwansu bakin gaban ruwa sukaga babu kowa kamar ba'ai tsiran wani dan adam agurinba,nanma mamaki yacika su ganin abun suke kamar almara kamar bagurin suka bari da pam da mutane,
awannan karan Sani yarasa abun fada na 'korafi.
Yakallah Jafar yace "munbanu",
Jafar dake gefe yagyada kai yana furta "Innalillahi wa'inna'illahir raji'un"
Yana fadi yana maimaitawa,
Sani ya ta'bashi yace "lafiya Malam Jafar salatin na mainene?",
Jafar baice 'kalaba yayi nuni dayatsa,
Zabura Sani yayi dakallon setin hannun Jafar, ya koma da baya yazaro ido atsorace yace "innalillahi wa'inna ilahirraji'un lalle Jafar yau itace ranar mutuwarmu"............................................
YOU ARE READING
Kaine Rayuwata😭❤❤ Complete
Romancelabarin na 'kunshe da Yaudara, Kiyayya, Soyayya, Tausayi, rikon Amana, Nishadi, Rudani, Juriya, Kaddara, Son abun duniya,......... A takaice! littafin na kulle da sako dan nishadantar, wa'azantar da mai karatu. In Summary........ Saifullahi (Saif)...