Kaine Rayuwata 10

1.7K 129 0
                                    

Kaine Rayuwata😭❤❤

FKD Fans Writers 《《 10 》》

By najaatu shehu naira

Sarki yari'ko hannun Zubaida, suka dawo bakin gado, yasa hannu yashare hawayen dake fuskarta,
Yatsura mata ido natsawan mintina,
sanin shakuwar da tayi da d'iyar Zinaru yarasa ta'ina zaifara yimata bayani,
Jin shirun yayi yawa ta'dago kai suna hada ido tai 'kas dakai,
Yayi gyaran murya tare da kiran sunanta yace
"Zubaida". ta dago ta kalleshi tace "na'am".......
Cikin nutsuwa yace "sanin kankine bamu muka haifi Zinaru ba,
Sannan tunda mutanan kauyannan sukasan da haka, taltali da adanan rayuwar Gimbiya da mukeso muyi bazai yuhba,
Y'armuce amma dole muka maida ita bayan gari, sabida mutan garinan bazasu amsheta matsayin tasuba,
Tun iyaye da kakanni kinsani nasani, wani bazai taba mulkin garin "Rani" ba sai 'Dan sarauta, anan nake ganin Zubaida gwamma da yakasance tunmuna raye asiri ya tonu, inba hakaba kashe mana ita zasuyi kema kinsani".

Ya 'kara 'kasa-'kasa da murya yace "naje gun Gimbiya yau, kamar yanda kikasani amma abunda nagani
banji dadib, yadda Gimbiya take rayuwa kamar baiwa, kawai dan duk a kuntata a muzguna mata!".

Tadago kai cikin bacin rai tace "waye yaimata hakan?"
Yakatseta yace "ba wannan ba tukkun, Zubaida duk yanda mukeson ta, bazamu bari muna gani a salwantar da rayuwar 'yarmu ba, kamar munsani muntake sanin kenan,
Inaso ki gane gwara mu barta ta tafi ko zata sami kwanciyar hankali,
kinga bamu saniba, ko da rabon tahadu da mahaifanta da danginta baki daya".

Tayi zumbir tamike tace "lalle bakasan ciwon taba! Idan nabar Gimbiya ta tafi, ta'ina zata fara? nikaina tunda aka haifeni banta'ba barin kauyan nanba, danhaka Wallahi bazan bar d'iyata ta tafiba".
Tabarshi wajan tace "kaga bari inje induba lafiyarta"
Yabiyota yariko hannunta yace "dawo Zubaida ashe haryanzun bakiyi hankaliba?
Nadauka maganganuna suna tasiri a kanki, ashe son zuciya yafiye maki komai?".
Yayi ajiyar zuciya yace "Toni zan je fada ana jirana, innadawo inason inji amsa daya daga gunki bakinki, nabarki lafiya".
Yatashi yafita fuuu cikin bacinrai.
Zubaida takoma gado tahau kuka,.

*************
Tunbayan ajiye Saif da tawagarsa tsakiyar fada, babu wanda yakara bi takansu,
Sunyi jungun-jungun ana jiran Sarki.
Waziri datunda akazo yanacika yana batsewa shida danshi Dauda,
kana ganin Dauda kaga wanda yake cikin tashin hankali,
Yakalli Mahaifinshi yace "Baba!, nifa duk yanda za'ayi saidai ayi,
Amma Gimbiya baza tabar garinnan ba, tun Yarinyar nan na'karama nake sonta da kaunarta, Wlh ba'inda zataje inaaaa",,,,,,,

Hannu Waziri yasa yabigemai baki da bayan hannu! Yace "Yimin shuru, shashasha wanda baisan ciwon kanshi ba,
Bakasan wahalar danake akanka nakeba? amma katsaya kana 'bata lokacinka gun tsintacciyar mage!
Ga matanan agari, kazabi wacce kakeso na aura ma,,,,,,,,,,, amma Yarinyarnan a'a gsky, zaifima kamin shuru karnaji ka 'kara tada maganar nan inkanason kwanciyar hankalin ka",.

Saif dayaga zaunu ta'ki 'karewa, yadaga kai yakalli dogarawan da suke masu kallo kamar zasu cinye, yayi karfin halin cece "Dan Allah abamu ruwa, munason muyi alwala akwai salloli akanmu!",

Dogon dogari ya zabgamai bulala a gadon baya!, yad'aga hannu zai karamai wata,,,,,,,
Sarki yashigo, karab akan idonshi Saif nabaza mur'kusun wayyo Allah.

Sarki da ranshi ke 'bace yace "wato nahana dukan nan amma Dogo saida kayi ko? Ni bazan fada kajiba",
Dogo yazube 'kasa yana fadin "tuba nake ranka shidade a yafeni, amma ruwan sallah suke naima
Ranka shidade musulmai ne!".
Sarki dake kokarin zama kan kujerarsa, yayi zumbur ya mike yace "musulmai fa kace?"
Dogon dogari Ya amsa "eh ranka shidade"..
cikin tsana sarki yace "dukkanin su ko mutun daya?".
Yace "ranka shidade dukkansu ne",

Sani da Jafar arazane suka ta'ba Saif cikin murya maikamar ra'da "hauka kake? maiyasa baka tambayemu kafin ka fad'a ba, mutanan nan fa maguzawa ne, basa kaunar addini wlh kashemu zasuyi".

Suna maganar kasa-kasa.
sukaji Sarki yace "toh anaima masu wajan ibada abasu ruwa, abasu abinci da wajan kwana, gobe zanyanke masu hukunci dawuri dan subar garinnan"
Basu Sani da maganar tabasu mamakiba,
Har Waziri saida lamarin Sarki yabashi tsoro da mamaki,
Baisan sanda yace "Ranka shidade lafiyarka kalau ko?
Ya dagamai kai alamar eh,
Sannan ya nuna Dauda da yatsa yace "shikuma Dauda kumai bulalansa yanzun",
Yanunasu Saif da yatsa yace "sai gobe yarage nasu hukuncin kawae",.

Zangalo yari'ko Dauda yana kaudakai karsu hada ido da Waziri yakwantar dashi yahau bulala,.
Jikin Waziri yayi sanyi yace "dakata",
Yakallah Sarki yace "amma abunda kayi ranka shidade kayi adalci kuwa?"
Yanuna tawagar Saif yace "suda sukayi babban laifi kakyalesu harda masauki dukda kasan addininsu amma Dauda dan gidana maijiran gado, shine kake wulakantashi a bainan jama'ah haka?"

Sarki yakalleshi rai'abace yace 'Waziri kayi shuru bansan magana".
Kamar ya'kara tsumashi yace "Wallahi bazanyi shuru kana ta'addanci da zalunci ba".
Sarki ya mike yace "inkun gama masa bulalan, kuje ku'ajiyeshi gidan ajiya harsai yagaya wanda yabashi makullin da'kin Gimbiya, dahar yajecan yasan dokane,.

Murya narawa Waziri yace "badai ka hukuntashi ba, toh maiyakawo wannan maganar kuma",
Sarki ya kalleshi cikin takaici yace "sabida nayi adalci, kamar yanda ka fad'a",.
Yasakai zaifita yace "fada ta tashi, saida safe".
Dogo da sauran fadawa suka kaisu ciki, aka nuna masu makewayi (toilet) da ruwa ma'ishi,
Bayan sun zaga sukayi alwala sukaci abinci ma'ishi, dukda badadi haka suka tuttura,.
Fadawan sukai masu sallama sukabarosu suna jero sallolin da basuyi ba.

Bayan Gimbiya tagama wanka ta kwance gashinta ta wanke tayi shafa, sannan tasa akira mata baiwa daya tazo tayi mata tausa,
Zubaida tashigo 'dakin tana kallon 'Diyar tata tattare da kauna tace "kibari nayi maki tausan, yau Uwa kike bu'kata ba kowa ba",

Ta kwantar da'ita kan cinyarta tahau tausa cikin kwarewa harta gama tsaf, sannan tamiko mata doguwar riga shimi tace "sawa nayi a kawomin su, naga kayanki duk suntsufa babu sabbi".

Ta kar'ba tace "nagode Mama",
Suna cikin haka Sarki yashigo yana kallon 'Yanmatan nashi guda biyu, yakalli Zubaida yace "kinga keda 'Yar taki, kamar Ya da 'Kanwa",
Yasake kallonsu yayi murmush cikin zolaya yace "kedai bakya tsufa, duk kaninsu sukayi murmushi.
Yasama waje yazauna yace "Zubaida kinkawo mata abinci kuwa taci?"
Zinaru ta katseshi tace "Baba na 'koshi, ba'kin nanne bansaniba kosunci abinci ba",
Ya girgiza kai yace "karki damu, aitunda sukaso cetonki nima bazan cutar dasuba,".
Tamaida kanta kan cinyar Maman,

Yashafa kanta yace "tashi kizauna muyi magana kinji Gimbiyata, gabanta yafad'i ta'dan dake tace "to Baba",

Yakalli Zubaida Yace "Zinaru munsan bamu muka haifeki ba amma ko iyayen da suka haifeki wlh bazasu nuna mana sonki ba,
bantabajin wai yau bani na haifeki araina ba,
maganar dakika gaya nakeso ki gayama Mamanki gatanan taji abunda kikeso kinji?".
Tad'ago kai tana kallonsu tace "Baba, Mama sabida sonda kuku nunamin bantaba tunanin baku kuka haifeniba",
Tatsagaita takallah Zubaida tace "Mama dan Allah kibarni naje bawai zantafi naiman iyayena bane, aa saidai zan tafine dan kusami kwanciyar hankali a ranku,
nasan zamana a bayan gari gaba d'aya hankalinku nakaina, dan haka Baba kona zauna a garinnan bazasu barmu tareba, korani bayan gari zasuyi, dagani sai namin dawa cikin tsoro da fargaba, dangirman kujeranka Baba kubarni na tafi kozan samu farinciki dani daku bakidaya",
Taja tayi shiru duk jikinsu yayi la'asar taci gaba tace "Baba banso muyi sallama sabida bazan'iya maku bankwana cikin nutsuwa ba, ina tsoron karnazo yimaku sallama nakasa tafiya,".
Sarki yagirgiza kai yace "wannan zancen banzane bazan bariba,
Kinmanta na gayamaki bazan bari kibar kauyennan ke d'aya ba, kinsan hanya da namin daji, dukda nasan kinsan kan hanya bazan bari kidau kasada ba",
Yayi 'kasa damurya yace "Kije ki kwanta kiyi barci sai da safe".
Zubaida ta tashi tabi bayanta suka kwana tare, Sarki yakoma turakarshi yakwanta,.

************
Da sassafe baifi karfe bakwai 7:00 ba,
Dogo da Zangalo suka shigo dagudu kamar zasu fa'do cikin d'akin Sarki,.
Daga bakin 'kofa Zangalo yace "gafaradai Ranka shidade",
murya narawa suna nishi shida Dogo harsuna ha'da baki.
Yace "Ranka yadade Ba'ki sungudu!! mun naimaisu sama ko 'kasa babusu".
Sarki yataso dagudu yazuba babban riga,
kafin yafito Zubaida tashigo da'kin ta gefen sasanta da gudu, tana kuka tana shashsheka tace "ka taimakeni ka ceci rayuwata Ranka yadade, banga Gimbiya ba!!!...........................

Kaine Rayuwata😭❤❤ CompleteWhere stories live. Discover now