Kaine Rayuwata 06

1.8K 134 0
                                    

Kaine Rayuwa😭❤❤

Written; By najaatu shehu naira

FKD Fans Writers 《《 06 》》

Karyanku y'ay'an matsiyata, suna mazure suka shigo,
Dauda yamike yabuga masu tsawa yace "daman haukan da kuke zuwa yima Gimbiya kenan? aiko giwa ta rame tafi karfin karnuka sujata",
Take suka zube 'kasa suna fadin "tuba muke ranka yadade. amma muna mata hukunci daidai daduk wanda yake nanne,.

Dauda yakallesu cikin tsawa yace "wlh tallahi in Sarki yaji wannan, to ku kuka da kanku, kuma uban wayace kumata hukuncin da zakuima kowa? ko kunmanta matsayintane?" cikin tsawa yace "ku amsamin". Dogari daya ya'dago kai yace "ranka shidane mahaifinkane yasamu, Wazirin Sarki".
duk kanin d'akin suka kalla Dauda kallo irinna tuhuma,.
Shikanshi maganar tamasa nauyi, nandanan ya susuce, ya kama hanya zaifita cikin fushi.
Dogarawan suka mike suka tareshi murya narawa sukace "umarnin Sarkine, kar abar kowa ya fita ranka shidade har saiya zo".

Ya kallesu cike da mamaki yace "harkunkai matsayin ku tsayamin agaba?"
Jiki na rawa sukaja da baya,,.

Sai alokacin Zinaru ta'iya motsawa tazo gabanshi tace "Dauda kayi hakuri kajira Babana kawai, dan ko nima bazanyarda ka sa'bama maganar Sarki ba, dole inga kowani mutun na kauyannan yana darajashi kagane?".

Ya sunkuyar dakai jin nauyin maganar datayi,
Abunka da yarinta yafara karkada kafa yana fadin, "shikenan tunda kince haka",.
nan dogarawan suka fita waje suna gadinsu,.
Nazir ya kalli Saif dahar lokacin, tsoro yabayyana 'karara akwayar idonshi, yajuya yakallah Gimbiya datake Safa da Marwa a tsakar dakin.
Saif kam abun yakoma bashi tsoro dan dazaran yaso gane abunda ke faruwa, sai yaga rud'anin dake cikin maganar yafi yanda yake tunani,.  suka koma sukayi jungun-jungun adakin, kowa da abunda kesa'kawa aransa,

*********
Sani da Jafar natsakiyar daji tun sallahn subhi da sukayi basu komaba, lalube kawai suke cikin dajin suna bincike.
Kowannan su dawaya ahannunsa yana kiran wayar Saif sanin bawaya hannun Nazir yabarta mota,.
sunyi nisa cikin daji suna naiman Saif da Nazir har sunfara fargaban kar namin dawa suncinyesu, ko mutanan da sukabi sunkamasu sun kashe,.
Sunyi nisa dajin bagida gaba bagida baya,
Suna tafe suna mamakin girman dajin, nansukayi arba da kogi, Yanmata da Samari, yara damanya nawanka,
Dasauri suka juya kai suna "Subhanallah!!!",
Sani yace "wannan wani irin al'ada ce kamar suna gasan nuna tsaraici,
Aiwannan tsiyace ba komaiba Jafar",
Basu 'karasaba suka juya suka chanza hanya,
Suna tafe Allah ya hadasu da wani dan Dattijo,
Dasauri suka tareshi da Sallama ya amsa,
Jafar yace "bawan Allah, dan Allah kokaji sanarwan ba'ki biyu a cikin gari ko kuma Allah yasa ka gansu?"
Mutumin yagirgiza kai yace "gaskiya ba acikin gari nakeba, ina rayuwatane nan bayan gari, dan garinnan basa Ibada, maguzawa ne! kuma natsaya maku maganane dan naga da'alaman 'Yan'uwa musulmaine shiyasa naimaku magana, amma kusani  inmusulmi yafiye za'kewa dasan tallata addininsa, sai suso kasheshi koma a koreshi kamar yanda ya kasance dani, kudai kulallaba kubar garinan tunkan susan anyi ba'ki, dan laifi kadan a garinnan yanzun kaji labarin kisa, kwata-kwata babu kaunan Allah aransu nabarku lafiya".
Zance ba'ka'kautawa kamar mai aikin Jarida yagama bayani ya wuce kansu bude bakisuce uffan.
Jafar da Sani da mamaki yahanasu magana suka bishi da kallo,.
Suka tsaya sukai nazarin gwara kawai su koma mota zaifi masu akan wannan ba'kar wahalan da sukesha,.

Suna tafe cikin hanyarsu ta komawa cikinsu yafara kiran chiroma,
rana takawo kai hantsi ya dubi ludayi.
Kiran Mommy tashigo wayar Jafar, yakallah yanunama Sani screen din, Sani yakalleshi yace "to yanzun maizamu gayamata?".
kafin wayar ta katse Jafar ya dauka ya gaisheta cikin ladabi, ta'amsa cike da fara'a tace "sojojin daji"
yayi dan murmushi,
tace "to ni nakira abokin naka, sam wayarsa baishiga, yana ina bashi wayar".

Jafar ya kalli Sani yarasa tacewa,
Sani yakarba wayar yace "Mommy Sani ne",
Tayi murmushi tace "'Dana Sani kun isa lafiya ko?" ya amsa "eh Mommy",
tace "toh Sani sauranfa? Saif baikirani ba, ko lafiya?"
Yayi sauri yace "eh lafiya wayar tasane babu network",
Tace "toooo koda naji, nayita kira Not reachable, bashi wayar mugaisa",
Ya hadiye miyau dakyar yace "Mommy yadanje bakin kogi, yanzun zai dawo, inya dawo zangaya mai yakiraki,".
Tadanyi jimmmm sannan tace "toh badamuwa, inya dawo kasa ya kirani sai anjima".
Ya amsa "To Mommy mungode". takashe wayar,
Ya sauke wayar akunnenshi yayi ajiyar yayi ajiyar zuciya. ,.
Suka kama hanyar komawa mota.

Suna tafiya kamar basuyi,
Jafar yakallah Sani yace "nifa Sani inna lura kamar zagaye mukeyi, so uku kenanfa muna wuce gurinnan, ko lafiya?"
Sani ya daga kai yace "anya kuwa Jafar",
Kafin ya rufe baki yagansu wajen kogi, yazaro ido waje yace "kai da gaskene fa! Wannan wani irin garine".
Araunace Jafar yace "wlh Sani mun 'bace!!!",,,,,,,,,,,,,

***********
Bayan 'yan awanni, dasukaga tsayuwa bata 'kare bane suka koma suka tsuguna,
Sun jejjemai yunwa ta cinyesu,
Nazir yagaji yajanyo kwandon kayan marmarin yahauci, ganin haka Saif ma yasa hannu.
Zinaru asannan tasan maike damun cikinta, tadau tuffa daya itama taci,.
Dauda dake tsaye harlokacin bai daukaba sannan babu wanda yamai tayi,.

Chan sukaji alamun tafiya ana ma Sarki kirari,. Dogarawan nan da gudu suka fa'do dakin suna fa'din "ku kintsa Sarki yazo"!!!

Kaine Rayuwata😭❤❤ CompleteWhere stories live. Discover now