Kaine Rayuwata 09

1.7K 137 0
                                    

Kaine Rayuwata😭❤❤

By Najaatu shehu naira

FKD Fans Writers 《《 09 》》

Nazir yatureshi yace "wlh kai kanka a dod'd'e yake,
nulurama idanunka basa gayama gaskiya,
Kana ganin Yarinya mai suffar Larabawa, dukda 'yar 'kauyece cikin datti amma kalli kalan fatanta, kyakkyawan mace kamar wannan Malam".
Duk abunda ake akan idon Dauda ake, haushi ya cikashi ganin Gimbiya, tamasu wannan kyauta,

Kafin sugama magana Dauda yakyarama dogari mai zabgegiyar dorina hiransu, yad'ago zai zuba masu,
Sai akan idon Sarki, Sariki yagirgixa kai yace "umarni nane wannan, karka 'kara dukan kowa anan kaji".
Ya amsa "toh ranka shidade".
Gabadaya hankalinsu yadawo kan Sarki dake fadin yace "ku kammala muwuce kafin rana ta fadi",.
Yari'ko hannun Gimbiya zai d'aurata kan doki Waziri yayi mazza yace "aa kabari wasu suyi aikinnan man",.
Sarki ya dagamai hannu a ta'kaice yace "kabarni y'ata ce nizanyi dakaina",
Ya 'daurata sannan yahau sukafara tafiya.

Suna tafe suna kuskus ganin an hana dukansu, murya kasa-kasa Jafar yace "wancan itace Gimbiyar ko?",

Saif ya kalleshi yace "lafiyarka Jafar? tunda kazo ka ishemu da maganarta".
Nazir yace "ni bama wannan ba, kun tawo mana da wayoyinmu ko?"
Sani ya gallamai harara yace "munmasan zamu hadu daku kenan".
Yana maganar yana ta'ba aljinhun rigarsa yace "barima na duba tawa",
Nan suka hau lalubar wayoyinsu shida Jafar,
Suka babu, taje suka fahimci cikin daji suna gudun ceton rai sukayar da wayoyin,
Sani yaja dogon tsaki yace "Kunsa kanku a bala'i kunsamu,",
Chak sukaja sukai shuru, ganin anshigo cikin gari sunacan suna surutu basusanma hanyar da akabi aka shigo garinba ,
Mutan gari suka hau shela ga Gimbiya ga Gimbiya, suna tafiya masu farincikin ganinta na 'daga mata hannu,

"Saif, Nazir, Jafar, Sani zara ido kawai suke, kai kace sunyi 'karya ko suna gaban Alkali kowannansu ido zuru-zuru kamar ace arrrr su'arta dagudu,

Ana isowa fada Gimbiya,
ta sauka da sauri ganin Sarauniya Zubaida tazo tarban Sarki Zinaru taje dagudu tafada jikinta suka rungume juna cikin hawaye,
Sarauniya ko Sarkin bata tsaya ganiba taja hannun 'yar tata suka shige gida.
Suna daki Sarauniya Zubaida na tatta'ba jikin Zinaru kamar mailalube tana kakka'be mata datti cikin kuku tace "Gimbiya haka suka maidamin ke? kamar almajira wayyo ni, wannan wani irin rayuwace!!,
Zinaru tadago fuskan Mamanta tahau share mata hawaye tace "haba Mama lafiyata fa kalau, kidaina damun kanki wlh kinji",
Tayi ya'ken dole ta share hawayenta tace "to badamuwa, maizakici a dafa maki ko maikikeso anaimo maki
Kokinaso a yanka maki wani abune?".
Zinaru tun tana ri'ke kukan ta takasa, tafashe da kuka maisauti ta rungume Zubaida tace "a'a bansan komai, kizauna kusa dani yafimin komai ayanzu karki damu Mama".
Tajanyo hannunta ta ri'ke tace "murnan ganinki kawai Zinaru bazai barni nazauna ba, dole inga nasamarmaki abunda baki samuba cikin kwanakin dakikayi a dajincan, kinji y'ata,.
Zinaru ta 'kara rungume ta tace "Mama bari nayi wanka, inaso nawanke gashina",
Tace "tohh", kamar mai nazari tayi shuru chan tace "Kiyi hakuri bansan zaki dawo yauba, da natanadar maki komai kamar yadda kikeson wanka da ruwan turare Gimbiyata,
Tayi murmushi tace "Mama karki damu yanzun duk na chanza, bazandunga damun kiba kinji",

Ta'dago kai takalleta suka hada ido tagirgiza kai tace "a'a Gimbiyata kiyi duk abunda ranki keso kinji, kece Gimbiya kuma kece........"
Zinaru tarufe mata baki da tafin hannun tana girgiza kai tace "Mama kiyi hakuri karkisa tafiyata taimun wahala, karna kasa tafiya", tana hawaye hawaye tace "wallahi babu ba'kincikin dayafi barinku a rayuwana".

Kowannan su hawaye yake zubarwa kamar ruwa,
Zubaida dake sauraran Gimbiya, tuni tashiga rudani tayi zumbur tamike hanyar 'kofa zata fita da sauri,
Sukayi kici'busss da Sarki zaishigo,
Tayi tariko hannunsa tazo gaban Zinaru tace "kaji mai Gimbiya kefadi kuwa? Wai zata barmu, bansan mai mukai mataba, kazo kaimata bayani, inaganin bata ganewa,
Batasan batada wanda yafimu santa duniyan nanba, kazauna gata ka gayamata,.

Gimbiya natsaye hawaye ke sauka kan fuskanta, tana kallon kaunan da Mama kenuna mata.
"Aranta tace "Kosu suka haifeni saihaka".
Tamarso ta dur'kusa gaban Sarki tace
Baba dan sonda kukemin karku hanani tafiya,
Kayima Mama bayani kozata gane kaji Baba",
tana maganar tana kallansu su,
Zubaida na tsaye ta tsira mata ido tana gyada kai tace "lalle Zinaru kingirma, ni banma san kinyi girman daharzaki iya tafiya kibarni ba,
dan bani na tsuguna na haifeki ba ko?".
Tadurkusa kasa kan gwiwowunta tace "dan sonda kikema Babanki dan masarautan nan, karki tafi kibarmu kinji?
kece farincikina kuma kece adon masarautannan, kinsan bamu ta'ba haihuwa ba dan Allah kitsaya har mutuwarmu Zinaru kinji?".
Tana kallonta cikin hawaye da rad'ad'n zuci tace "zaki tsaya ko? Kodan ni kitsaya Gimbiya karkije ko ina".

Sarki kanshi saida zazzafar kwalla ta sauko mashi dan kallansu, yahada gaba d'aya ya rungumesu,
sunfi munti biyar ahaka, kafin yakatse shurun da cewa "to ya'isa ku tsaya mu fahimci juna,
Wannan lamarin babbane yashafi rayuwarnmu".

Yakalli Gimbiya yace "tashi kije, kiyi wanka sannan kisa aimaki tausa, ko zakiji dadin jikinki, kinji Gimbiya?".
Ta dagamai kai alamar eh, tana kuka da shashsheka ta wuce,.

Sarki yadago fuskan Zubaida yace "Zubaida inaso ki saurareni dakyau,
Dan nayi maki bayani, inkin gamsu zaifi inkuma bakigamsu ba yarage naki, amma inaso kiyima Yarinyar mutane adalci, kar alhakinta ya kamamu kinji",

Tadago kai suka hada ido, yadaga mata kai yace "kwarai kuwa",
hawaye nabin kuncinta tace
"Tooo inajinka, gayamin".......

**********
Mommy dataga kuka bazai kaitaba, tatashi tatafi dakin Zainab idanunta sunyi jajur.
Tayi Sallama taji shiru,
Tashiga tana kwallah kiran "Zainab Zainab". muryarta taa dasashe sabida kukan datayi ya dasar mata da murya,.

Ganinta Zainab tayi kan sallaya kanta na 'kas tayi sujjada.
harta idar da sallah Mommy nazaune gefen gado tana jiranta,
Tana zaune tana aiyana hali irinna Zainab da Yayanta abun koyine halinsu na burgeni basa wasa da ibada kokadan,
Hawaye ya gangaro mata, tuna ko wani hali Son yake ciki yanzun,
Tayi sauri tatare hawayen ta kafin Zainab tagani,
Cikin zumudi bayan ta idar tace "Mommy sun bugo ko?",
Tayi kas dakai tana girgizawa alamar "aa",

Basufi 'yan muntinaba Mommy tadago kai tace "tashi muje gun Daddynku, maybe yasamu some piece of information muje muji,.
Zasu tafi Mommy taja ta tsaya tace "Ni wlh tsoroma nakeji naga kamar soyake ya maida laifin guna,
Zainab ta dafata tace "a'a Mommy shima tsorone da furgici suka shigeshi muje muji"...

Duk cikinsu babu maijin karfin jiki, suna tafiya kamar bazasuyi ba suka hau har sama gun daddy,
Lokacin Daddy yaje toilet yafi sau bakwai yana Sambatu kamar Zararre!!!,
Azaune suka tardashi yazuba ragumi!
cikin nadamar barin Son yayi tafiyar!!.

"Tunbayan maganasa da Malam Kallah yamai bayanin ya tabbatarmai
Lalle su Saif sunfad'a mugun hannu, ana azaftar dasu sa'anan duhu ya lullu'be hasken da yagani,".
Alhaji Sadiq ko amsa bai iyabama Malam Kallah ba, wayar dake hannunsa tafa'di,,,,,,
Take gudawa yayimai Sallama.....................

Kaine Rayuwata😭❤❤ CompleteWhere stories live. Discover now