Kaine Rayuwata😭❤❤
Written by; Najaatu shehu naira
FKD Fans Writers 《《 28 》》
Dakyar ya rarra'ba ya 'kai dakinsa, jiyake kamar ana huramai wuta a kirjinsa, zuciyarsa na turnu'ku'ku yari'ke kirjinsa da hannu bibbiyu, yasamu yalafe kangado harsaida zuciyarsa tarage 'kuna, yatsunduma tunanin maiyasa Daddy ke nuna masa rashin kauna da halin ko inkula.
Kanshi ya 'kulle babu wani positive answer, azahiri yafurta "toh dama anama maza Auran dolene kodai naiman bala'ine irinna Daddy kawae", ya'kullah wannan ya kwance wancan, shikadai yana kwance yana sokama kanshi tambayoyi, wata zuciyar tacemai "toh why not kayi auren mana kawai Saif awuce wajan", nandanan yahau girgiza kai kamar yana gaban wani, yana rayawa ransa da jaddadawa "a'a ina bazai yuhba, bani da budurwa kuma baza'amin dole ba, faqqat" ahaka barci ya daukeshi,Jin ana kwadamai kira "Yaya-Yaya"
ya tashi ido ciki-ciki sabida tunani da kunci da yakwanta dasu,
Yakallah Zainab dake gefensa yace "Auta lafiya?" Tad'an batarai tace "munzo gaishekane naga haryanzu baka tashiba, kamar baka da lafiya ko?" Kai kawai ya girgiza mata yace "lafiyata kalau, Daddy keso ya 'batamin rai, wai zaimin Aure" cikin zolaya yai maganar.
Zainab tayi kini-kini da fuska tace "aure kuma?" Yace "eh wai Jamila yarinyar Uncle Sa'id"
tayi zumbur ta mike tace "kuttt Allah kiyaye, Yarinyar da takeji kamar bazata taka 'kasaba, ga isah ga iyayi tunda akaba Babanta CBN Governor tadaina shiga harkan kowa, ai Yaya dahakama in auranne har gwandama ka Auri Zinaru" ta dafa kafadar Zinaru dake tsaye jinin jikinta yatsaya chak jin maganar da suke.
Ya d'agokai, alokacin yasan Zinaru na dakin idonta na kanshi tace "ina kwana Yaya" dadi yaji har ranshi, zuciyarsa tayi fari 'kal tuna yau a under protection dinsa takwana yace "Gimbiya ya kwanan gidanmu?" Zainab tayi sighting idonta gun Zinaru, cikin murya mai kamar rad'a tace "wallahi Yaya kace Zinuru kawai"
Ganin Zinaru nawajan yasa ya 'bata rai yace "ke wai ina wasa dakene, nace maki ina Sonta ne?" ya'kara shan mur kamar badashi ake hira rimi-rimi ba yace "maima yakawoku da safennan haka"
Ran Zainab ya 'baci cikin muryar da bata fita tace "tacemin kace zaka kaita school" nan 'kofofun tunaninsa da Daddy ya toshe suka bude yace "hakanefa namanta," yakallah time 8:20 yayi dan tsaki (hissing) yace "gashi har time yatafi," ya kallah Zinaru data zubamai na mujiya kallon tuhumane ko kallon tsana ita tabaima kanta sani yace "kije kishirya mutafi,"Kai tad'aga tace "toh" tafita tabar d'akin dan dama ta 'kosa tabar wajan da yake, yakallah Zainab yace "ke bakinki bashida pull stop bare comma ko" Yaja tsaki Ya fada bayi,
Fitowa tayi tashige dakin Zinaru danta tayata shiryawa,
Azaune ta tarar da ita tayi nisa a kogin tunani, har Zainab tashigo ta dafa kafadarta cikin sanyaryan murya tace "Sister bazaki shirya bane, kunyi latti fa," Zinaru tayi dan ya'ke tace "eh inazuwa,"
Ta mike jiki ba kwari tashige
Bayi (bathroom),
Batafi munti biyar (5minute) ba tafito a gaggauce, tazauna gaban madubi batafi munti 6 ba tami'ke dukda batayi makeup din azo aganiba, amma ahaka saida abun yaburge Zainab irin kanshin da Zinaru ke bugawa bakace yarkauyen da aka kawo kwanakin baya bane,
Zainab dai takasa boye curiosity dinta tace "Sister wai wannan kamshi haka, gaskiya Hajiya naji dake" murmushi kawai Zinaru tayi, tana gaban wardrobe ta dauka doguwar riga jallabiya ba'ka da qaramin mayafinta tayi Rolling, tasa hannu ta janyo takalminta dake bayan jaka,
Vinci ne guda 5 duk flat, Hajiya tasa aka kawomata hargida ta za'ba,
Takallah Zainab da bakinta ke hangame don mamakin irin chanzawan da Zinaru tayi, lokaci daya tagoge tana komai cikin kwarewa. Tace "muje ko Zainab na gama,"
Wacce tazo gyara sai yazam ita ta 'karu, eyeliner da lipsglove tasa amma kwalliyan tafaso, abunka da jarfata Zainab tafada aranta, azahiri kuma tace "Wow Sister kin ganki kuwa? Wlh kinyi kyau"
Murmushi kawai Zinaru tayi dan haryanzu bawai tana jinta a right mood dinta bane tace "Nagode, muje karyaita jira" Zainab ta mike tace "aikam muje"...Ganinsu yasa yatsaya chak da gyara karin wulansa, ya Subhanallah ya furta aransa, kasa dauke idonsa kan Zinaru yayi harta iso gab dashi, ta dago kai sukai 4eye cikin idanunta farare tas da ratsin kwalli da zara-zaran lashes, kamshin turaranta ya doki hancinsa, tace "na shirya" baiji muryartaba dan yariga ya dod'e kunnansa bayaji baya sauraro saidai gani, yayi nisa cikin shagaltuwa da kallonta, saida Zainab ta ta'bashi tace "Yaya kayi sauri mana" akunyace ya saukar da idonsa yace "kuje bakin mota kujirani ga key inazuwa" ta dauki key din taja hannun Zinaru suka fita,
Yazauna turusss bakin gado yana admiring din hallittar data fita yace "Wow, i need to stop dis, Saif u need to stop dis weird look", azahiri ya furta yayi zazzafar ajiyar numfashi aranshi yace "its Normal macece kuma she is like a Sister to me, inda So ne tunfarko zanjishi ba yanzuba, yayi yar gajerar tsaki ganin yazauna tunanin banza lokaci yatafi.
Yafito cikin shadda gezina ash colour sai buga kamshi yake, abunka da maikaunar kamshi,
Zaiwuce sukaci karo da Mommy tafito, tana ganinsa ahaka, wanni annurin dadi ya ziyarceta ta washe baki ta sakarmai murmushi, shima ya maida mata, ta matso tace "Son ina zaka haka da safenan tunkan kayi breakfast?" Ya lumshe ido kamar wanda baiso yayi magana yace "Ni?" Tayi yar dariyar zolaya tace "a'a ni Son"
Ganin Son ahaka hankalinta ya kwanta domin tunda Alhaji ya gayamata yadda suka kaya da Saif gabanta ke fadi,
Yayi murmushi yace "Mommy bari naje, Zinaru zankai makaranta"
sabo da hali nandanan tayi kini-kini da fuska, amma sanin halin da suke ciki yasa tace "Allah kiyaye hanya"
shima ciki-ciki kamar an sha'keta dole saita fad'a,.
![](https://img.wattpad.com/cover/173403386-288-k686329.jpg)
YOU ARE READING
Kaine Rayuwata😭❤❤ Complete
Romancelabarin na 'kunshe da Yaudara, Kiyayya, Soyayya, Tausayi, rikon Amana, Nishadi, Rudani, Juriya, Kaddara, Son abun duniya,......... A takaice! littafin na kulle da sako dan nishadantar, wa'azantar da mai karatu. In Summary........ Saifullahi (Saif)...