Kaine Rayuwata 49

1.6K 124 16
                                    

Kaine Rayuwata😭❤❤

Written By; Najaatu Naira

FKD Fans Writers 《《 49 》》

https://www.facebook.com/groups/459234504875663/

♡Put your hand in mine, and give it a chance. I will show you down a brighter path, trust me♡

Aunty Jiddah ta taso da gudu,
A firgice tayo kan Zinaru tare da 'Yan'uwanta arude,
Ta janyeta daga hannun Saif ta rungumeta muryarta narawa tace "lafiya Aslam menene",
Cikin kuka Zinaru tace "yaji, yaji tawatsamin",
Tsam Saif ya sunkuya ya sunkuceta ahannun Aunty Jidda dasauri yatafi da ita bayi,
Ruuu suka bisu Aunty Jiddah na rike da hannunta,
Ganin nandanan waje ya hargitse Jamila tasa kai zata gudu,
Daddy yai ram da'ita,
Zatai magana ya dauramata mari fau yakuma dauramata,
Dakyar aka janyeta ahannunsa,.
Mommy dake gefan Daddy fadi take aida ka 'karamata, mara mutunci, rashin mutuncinki haryakai kiyi tunanin zaki tada taronnan wlh karya kike Jamila",
Tasa hannu zatakai mata mangari, Hajiyar Nazir ta janyeta da sauran Dangin Mommy,
Daddy yakallah Mommy a harsale yace "kice afitadda ita daga Hall dinnan konasa a wulakanta ta",
Yasakai yatafi Fuuuu baitsaya ko'inaba sai restroom da Zinaru ke ciki,
Ruuu duk akabishi, sunje suna shirin fitowa, har ta'iya bude ido.,

Hajiyar Nazir ta rungumeta da sauri tace "Aslam lafiyarki kalau ko?"
Zinaru ta gyada kai tace "eh",
Daddy yasa tafin hannunsa kan goshinta yace "mutafi gida ko?"
Dasauri ta gyada kai cikin gajiya tace "eh dan Allah",
Sauri Saif yayi ya riko hannunta, cikin zafin rai yace "muje, ina Jamilan wlh yau nalahira saiya fita jin dadi",
Dasauri Zinaru ta jiyo tace "a'a Yaya dan Allah ka kyaleta",
"Babu ruwanki" yafada a takaice.
Ido ta kashemai tasa bakinta kan kunnensa cikin ra'da tace "Yaya koni zanyi abunda yafi wannan idan naganka tare dawata 'Ya mace baniba, yau ranan farinciki nane kuma na yafe mata, inama zata 'kara ganina, dan Allah murabu da'ita kawai My Nur",
Akunyace yasaki murmushin nishadi,
Nandanan ya nemi 'bacin ransa yarasa,
Yakallah mutanan wajan akunyace yana sosa kyeya yace "muje kawai muci gaba da taro, Allah yafita",
Gaba daya aka kwashe da dariya,
Daddy yaja kunnensa cikin raha yace "kaiko Son Allah shiryeka",

*******
Karfe shadaya aka kawo motar kwasan Amare,
Daddy kawai yarakasu har bakin mota,
Cikin nutsuwa Daddy yakallah Saif yace "dan Allah Saifullahi ga Aslam,
amanace gunka, kuma 'Yar'uwarkace, dan Allah karike amana",
Ya 'kara kausasa murya ya nunasa da yatsa yace "Saifullahi gwanmama kariketa amana, dan idan kasake kaci, karka manta ba Marainiya bace wlh tafika gata, ra'ayinkane kazama 'Dana ko Sirikina yanzun, amma bazan saurarama ba idan kacutarmin da Aslam domin Aslam bani da wanda yafita gudan jinin Farouq 'Dina........."
Cikin kuka Daddy ya 'karasa maganar yana sharar kwallah,
Dasauri Saif ya rungumeshi,
Daddy yasa hannu ya janyo Zinaru ya hada ya rungumesu baki daya yana  'kib-'kib da ido,.
Basufi dan mintinaba ya'dagosu yace "kuje Allah yabaku zaman lafiya",
Saif baiyi wata-wataba yashige mota,
Daddy yasa Zinaru gefensa fuskanta a lilli'be yana sanya mata albarka tare da lallashi,,
Saif ya'dagama Daddy hannu Daddy na dagamai Driver yajasu sai Maitama....

Nazir da Zainab suna bakin mota suna jiran Daddy yagama dasu Saif da suke iya hangensu,
Ya gangaro yasamesu yana murmushi maicike da bege yace "Autana,"
Dagudu Zainab ta rungumeshi tana kuka,
Ya hau shafa matakai cikin rarrashi yace "ya'isa haka Zainab, kinji ya'isah nace",
Yakallah Nazir yace "nasan wannan maganar baikamata inyitaba amma dan Allah karike min Zainab Amana Naziru, tunda inbaccin tanuna tana kaunarka bazanbar Zainab tayi aureba yanzu, kasan Zainab Yarinyace, dan Allah gatanan karike amana",
"Toh insha Allah Daddy" Nazir yace kansa akas,
Daddy ya janyeta daga jikinshi, yamika mashi ticket yace "Jiddah taimaku Booking room a Sharaton na Sati kafin kudawo gidanku ankammala ginin, kuje Allah kiyaye hanya",
Nazir yakarba yayi godiya yaja hannun Zainab tana kuka suka wuce..

Kaine Rayuwata😭❤❤ CompleteWhere stories live. Discover now