Kaine Rayuwata 03

2.4K 159 0
                                    

Kaine Rayuwata❤❤😭

Written by; Najaatu shehu naira

FKD Fans Writers 《《 03 》》

Suna tafe yamma takawo kai,
jikinsu duk yai la'asar suka shigo Maiduguri, daganan suka dauki hanyar Chad.
anan Sani ya mi'ke yana gyara jiki ya kalli Saif yace "Sarkin tu'ki bani na taimakama, kadan kwanta ka huta munemi gidan Mai (petrol station) nankusa mu'kara cika motarnan, dan nagalon dinnan gwara mubari in munshiga daji maiya'kare mayi amfani dashi",

Saif yagyara parking yana fadin "wlh ka taimaki rayuwana",
Sani yakarbi motar yana tuki cikin kwarewa suka dauki hanya,
Cikin maiduguri suka sami gidan mai suka cika tanki, nansuka 'karama mota gudu sai border,
Tsakanin Maiguduri 'kasa Nigeria da Chad yan custom suka tsaresu da tambaya, Nazir ya nuna masu ID card, suka sara masu suka bude masu hanya suka wuce, "Nazir babban custom ne (controller)" ,

Sun shiga garin Chadi gaba da magriba suna tsakiyar daji, Saif dake gefan Sani yace "to mufara yada zango anan yaso bayan kwana biyu mashiga cikin gari,"
Nazir yayi zumbir yakalle su, yace cikin dajinnan!!?, anya kuwa zamu iya?"
Saif da Sani suka kwashe da dariya Sani yace "Haba officer ai dadin tafiyar kenan,"
Sani yai parking guri maikyau suka fiffito daga mota kowa yana salati da goran ruwa ahannu, suka kama ruwa sannan sukayi alwala danyin sallah,.

Suna idar da sallah suka koma mota, nan suka dau firan Duniya, Nazir ya kallesu yace "dolefa muji dadinmu tun muna Samari, dan inmunyi aure wace macene zata barka fita trip haka, ai saidai shopping din kayan makwalashe,"
duk sukahau dariya Saif yace "Mata ai sunji kwadayi, danma za'ki baicika masu illah ba," Nazir yace "nizan fada maku wannan, danku nagama har tsoransu kukeji,"
allokacin Sani yadawo da dubansa gunrinsa yace "To ina amfanin yaudara Nazir?",
tunda Saif yaji haka yasan dawasa suna iya fara rigima akan wannan yar maganar yace "A'ah kunga mubar maganar nan kowa da kiwon da ya karbeshi, ko kunsan,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,"

Jafar ya katse maganarsa cikin hanzari yace "kai kutsaya kuyi shuru naji kamar motsi agurin nan",
Gabadaya gabansu ya fad'i sukai kasa dakai dukda duhun wajan, chan sukaji tafiyar mutun biyu suna tafe, amma saukar tafiyan su kadauka mutun dubune ke tafiyar,. Har sukazo suka wucesu basu lura akwai wani abu agurinba, suna tafe suna fira muryarsu asha'ke,.

Saif zai bude 'kofa Sani ya rikeshi yace "bakada da hankali ne Saif!? maike damunka ne? Inama zaka? Kasan sune? wallahi ka kiyaye kanka karka kai kanka halaka,". Cikin murya dabata futa 'kasa'kasa yakemai maganar,.
Saif ya kwabemai hannu yace "barni kaji damairai akeyi, indai bakayi bani guri,"
yabude motar a hankali yafita,
Nazir dake baya yace "Jirani koda mutuwa ke jiranmu, ai yafi ace munbada labari mun mutu, da ace bamu gani ba bamu jiba, Guys da mairai akeyi,"
shima yabude suka fice suna taku ahankali suna sand'a sunabin wa'innan mazaje biyu masu kirar samudawa, har saida suka 'kure masu mutanan nansuka shiga wani 'daki kwara daya a dajin da ke rufe da kwado, suka bude suka shige,.

Bayan kamar awa uku suka fito da wata Yarinya da batafi 'yar shekara sha shida ba, suna zaginta suma fadin "mai kwadayi dama karshensa wulakanci, kizagaya kiyi bayan gida muna jiranki munafuka", suka buga mata tsawa "kina ji ko?",
Cikin rawar murya tace "eh inaji, duk wannan abun akan idon Saif da Nazir akeyi,. Tayi tafiya mainisa sannan ta tsaya ta tsuguna.

Nazir yataba Saif cikin murya ra'da yace "Dan'uwa anya wad'annan ba aljanu bane?"
Saif yagallamai harara yace "idan aljanune zaka iya ganinsu? ni nafiji ajikina kidnapping din Yarinyar chan sukayi, ka kallah dakyau fa,".
Saif yakuma dubanshi yace "kaga jira, muzagaya ta baya mugudu da ita man,"
Nazir ya ru'ko hannunsa yace "Abokina mudaiyi tunani kar musa kanmu a musiba,"
Saif ya'bata rai yace "kai in bazakaba, ni zani, mukasani ko daga karshe su kasheta?",
Nazir yadago kai yana gasgatawa yace "hakane fa mutanan nan basu da imani muje kawai",.

Suka rarrafa ahankali cikin ciyayi, sukaje gurinta tana tsugune har lokacin,
Saif ne daga naisa yace "Sallamu alaikum yanmata karki tsorata,". Kafin yarufe baki tafasa wani gawurtaccen  ihu mai kururuwa!!,. Tsorata da ihunta Saif shima yasa iwuh "wayo Allah,"
ta'kara fasa ihu tace "nashiga uku",
yan tsuntsayan dake dajin suka hau ifac- iface suma, jin ihun tsuntsaye Jafar da Sani dake mota, atsorace suka bude motar suka fito,

Sani yace "Allah yasa wad'annan marasa jin basusa kansu a musibaba!, tunkan gari ya waye sun fara janyo mana wahala, yanzunma haka wayasan inda suke"
Jafar baice 'kalaba suka jingina da mota cikin jimami da tunanin taina 'karan ihun yatawo,

******
Agefan Saif da Nazir kuwa, kafin tagama ihun wa'innan mutane biyun suka chafke su,.
Kai kace mutunne yari'ke jaririn 'Da, suna gurnani kamar zaki yaga nama,.

Cikin ru'dani da tashin hankali suke furta "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un,". Saif nakwala kiran "Sani",.... Nazir na kwala kiran "Jafar dan Allah kuzo ku taimakemu!!!".
Wa'innan mutanan suka daukesu suka toshe bakunansu da tafin hannu, suka suresu ba kakkautawa suka tafi dasu ukun, suna har harba 'kafa,..........................................

Kaine Rayuwata😭❤❤ CompleteWhere stories live. Discover now