©®Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye ⚠FIRST FAMILY...
Ƙarfe biyar da minti arba'in da takwas na yamma, ta faka Motarta a parking space, ajiyar zuciya ta sauke ya fi sau uku, sannan ta kalli takardun da ke gefenta kamar mai tunani, daga bisani ta kai hannu ta ɗauka, ta buɗe motar ta fito.
Jiki a sanyaye ta nufi harabar gidan, gurin da Mahaifinta yake zaune yana shan iska, daman a al'adarsa ya kan zauna a habarar gidan da yamma, wani sa'in ya kan duba jaridu wani lokacin kuma ya leƙa yanar gizo, dan sanin me duniya take ciki.
Da kamar fargaba Namra ta doshi gurin da yake, zuciyarta na raya mata abubuwa da dama.
talkamin ƙafarta ta fara cirewa tun kamin ta ƙasara kusa da carpet ɗin da aka saba shimfaɗa masa, sallama ce ta fito bakinta kanta na ƙasa kamar mai jin nauyin kallonsa.
“Assalamu Alaikum”
Bai amsa sallamar ba, sai dai ko kaɗan hakan bai bata mamaki ba, daman bata tsammaci zai amsa mata ba, sai kawai ta ɗora da gaisuwa.
“Abban sannu da hutawa ya aikin?”
Ya yi jinkirin amsa mata na daƙiƙon da zai kai ashiri zuwa ashirin da biyar, sannan ya amsa mata can ƙasan maƙoshinsa
“Al-hamdulillah”
Bata yarda wata kalmar ta ƙara fito daga bakinta ba, sai kawai ta tashi jiki ba ƙwari ta saka takalminta, ta nufi hanyar da zata sadata da part ɗin Mahaifiyarta.
Sai da ta share hawayen da suka zubo mata kamin ta kai hannu ta murɗa ƙofar falon ta shiga. Babu kowa a parlor sai air conditioner dake ta aikinsa, Kai tsaye ɗakinta ta wuce zuciyarta cike da rauni.
Saman gadonta ta zauna ta lumshe ido tana sauraren bugun zuciyarta, kalaman da Mahaifinta ya yi mata ɗazu da safe suƙa riƙa dawo mata, irin yadda ya riƙa aibanta ta, yasa ta ta yi saurin dafe kanta, sai kuma ta fashe da kuka tana murza zoben dake hannunta.
Haka ta zauna a ɗakin bata fito ba har sai da aka yi sallah Magariba, bayan ta yi sallar ta fito ta nufo parlor fuskarta babu yabo babu fallasa.
Duk ƙannenta suna zaune parlor suna kallon Dadin kowa, babu wanda ya lura da fitowarta sai Mahaifiyarta. can nesa da Mahaifiyarta ta zauna tana gaisheta.
“Anty barka da dare”
Bata amsa mata ba, sai kallonta take tana karantar irin halin da ƴarta take ciki.
“Tunda kika dawo daga makaranta Namra kina cikin ɗakin, so kike yi damuwa ta yi miki yawa ko? Yau ranar girkina ce amman saboda ke Abbanku bai leƙo nan ba, na shiga sashensa na rasa gane kansa, so kike ki kashe min aure ko Namra? kin fi son ki rayu da son zuciyarki fiye da farincikin iyayenki? bana ƙin zaɓin ki Namra, amman tun da mahaifinki ba ya so barin shi ya fi alheri”
YOU ARE READING
ZAGON ƘASA
Mystery / ThrillerThe Story Of three family. NAMRA FAMILY. DR. HILAL FAMILY. KALSOOM FAMILY. Sunan Novel ɗin *ZAGON ƘASA* Green snake under green grass, people with two colors. A tension, Schemed Novel of slut. Witness to regret. Witness to love. Witness to tears...