ZAGON ƘASA___25

2.1K 185 0
                                    

NOT EDITED ⚠️

KALSOOM POV.
Ta daɗe a gurin tsaye duniyarta na juya mata, kunnuwanta sun kas ɗaukar abunda suka ji Hilal ya faɗa mata, idonuwanta kuma sun kasa yarda da ba mafarki take ba.
Makomar aurenta take tunani, yadda zamanta a gidan zai kasance yake mata yawo a ƙwaƙwalwa, taya zata biya abunda bata ɗauka ba? Akan me zai nuna dubu ɗari uku sun fi aurenta daraja a gareshi? Dan me idonsa zai rufe har yayi mata wannan furucin?

Ta kasa zaɓa tsakanin igiyar aurenta da kuɗin da idan har ta bashi zai iya tabbatar masa da lallai ita ɗin ce ta ɗauka.
Hawayen dake idonta ta share, ta tashi ta ɗauko akwati ta buɗe wardrobe ta ɗauko tufafinta ta saka aciki, ta ɗauki jakarta ta saka wayarta da duk wasu abubuwa da tasan zatayi saurin buƙata, ta zari mayafin ta yafa ta jayo akwati ta fito. A lokacin Hilal yana zaune falon ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya.

"Ina zaki je?"

"Gidan mu, ba kace na kawo kuɗi ba ko kuma a bakin aure na? Ni ba zan iya biyan abunda nasan ban ɗauka ba, amman Allah yana nan baya bachi baya angaje zai bayyana gaskiya, amman ni ba ɓarauniya bace"

Tasowa yayi ya ƙaraso kusa da ita.

"Look Kalsoom ..."

Sai kuma yayi shiru ya kasa magana, ya kuma kasa kallonta. Ganin hakan yasa t share hawayenta ta cigaba da jan akwatin. Sai ya riƙe ya kai hannu ya riƙota, kuma ya kasa mata magana, shi dai ji yake babu daɗi ya rasa abunda ke damunsa, sai yanzu yake jin nadamar furucin da yayi mata, mamakin yake yadda ya alaƙanta sakinta da kuɗin da basu taka kara sun karya ba a gurinsa, bayan kuma baya da tabbacin ita ɗin ce ta ɗauka.

"Ban aureka dan dukiyarka ba, balle har ya kai ni ga yi maka sata, nayi tunanin kasan darajar aure, ashe na yi kuskure, daman an faɗa min baka son haihuwa kana son kayi amfani da wannan damar ne ka wulaƙanta ni ko? Zan bar maka gidan ka sai ka zauna da wanɗanda ba ɓarayi ba!"

Kalamanta sun harzuƙa shi matuƙa, sai kawai y saki hannun nata.

"Kije duk inda zaki je, amman bari na faɗa miki duk wani abu ya samu cikin nan na ki, Wallahi sai kin yabawa aya zaƙinta"

Cikin wani irin ɓacin rai ya nufi ɗakinsa, ita kuma ta bishi da wani kallo na takaici na baƙinciki, kamin ta saka kai ta fice.

Ɗakinsa ya koma ya zauna, rasa yayi abund ke masa daɗi, dawowar da yayi ɗaukar kuɗi sai ya kasa komawa. Ba shi ya fito ɗakin ba sai da lokacin ɗauko yaransa daga makaranta yayi har ya gota, sannan ya fito daga ɗakin.
Kukan Rafiq yaji da yaji yasa shi ya nufi ɗakin Kalsoom dan shi sam ya manta da Fariq na bachi.

Ɗaukarsa yayi ya ɗora a kafaɗa yana jijjigashi, ya fito ya buɗe motarsa ya saka shi gidan gaban, sannan ya zagaya ya shiga ya tashi motar.
Ko da ya isa ɗaukarsu duk sun ƙosa, ga Rafiq sai kuka yake masa, har suka dawo gida.
Da gudu suka shiga falon, sai suka tsaya a gurin da Kalsoom ta saba nuna musu su aje safunan su suka aje sannan suka nufi ɗakinta suna rigangan.
Ganin bata ɗakin yasa suka fito suka nufo kitchen da gudu, nan ma basu ganta ba, sai suka nufo dinning gurin da Hilal yake tsaye yana haɗawa Rafiq madara.

"Daddy ina Anty?"

Yi yayi kamar be ji su ba, har sai da suka ƙara tambaya sannan ya kalli Ezzah kasancewar ita ce babba.

"Anty ku taje unguwa"

"Yaushe zata dawo?"

Ulfah ta tambaya. Sai da ya sawa Rafiq madara a baki sannan ya amsa musu.

"Ni ma bata faɗa min ba"

"Daddy ta dafa mana abinci?"

"A'a bari Rafiq ya gama zan muku takeaway yanzu"

ZAGON ƘASAWhere stories live. Discover now