ZK___19

2K 194 3
                                    

NOT EDITED ⚠️

Baki har kunne Asim ya isa gida da kuɗin, tun daga yanayin sallamarsa Mama ta gani yana cikin farinciki. A ƙuryar ɗaki ya same ta tana zaune saman sallaya ya zauna kusa da ita yana murmushi.

Wani kallo tayi masa ta ɗauke kai, dan ita yanzu wani haushi ma yake bata ji take kamar tayi ta dukansa. Takardar kuɗin dake aljihunsa ya ciro ya aje mata gaban sallaya tare da zinarin da Namra ta bashi.
Ba a ɓoye zinari yake ba, ko yanzu ka tashi daga bachi aka nuna maka shi zaka iya gane shi, musamman irin wannan na Namra da aka siya daga Dubai. Gabanta ya faɗi, sai ta kalli sarƙar ta kalleshi kusan sau huɗu sannan ta ce

"Ina ka samo wannan sarƙar Ibrahim?"

Da dariya ya amsa mata

"Nawa ne"

"Na ka? Sata ka fara ne? Kamar fa zinari nake gani"

"Ba kama bace zinari ne, wannan kuma takardar kuɗi ce na miliyan biyu da dubu ɗari uku"

Ta daki ƙirji ta da ƙarfi.

"Miliyan biyu Ibrahim? Ina ka samo wannan kuɗi?"

Yanayin yadda tayi masa tambayar da ƙarfi, yasa ƙanensa shigowa ɗakin da gudu suna tambayar miya faru.

"Kuɗi na samo mana miliyan biyu da dubu ɗari uku, ga kuma sarƙar zinari"

Ƙanensa ya zauna kusa da shi da mugun mamaki.

"Ya Asim taya ka ɗauko?"

"Ba ɗaukowa nayi ba, Namra ta bani tace nayi hidima da su"

Duk tsalle suka saka suna murnar Yayansu ya samo kuɗi, sai Mama tayi saurin riƙe so

"Dan Allah ku rufa mana asiri, kar aji a dirar mana cikin daren nan"

Sai da suka natsu sannan ta kalli Asim

"Da gaske ita ta baka Ibrahim?"

"Wallahi ita ta bani yanzu nan, sai da ma nayi kamar ba zan karɓa ba, sannan na karɓa kuma tace ba zata faɗawa kowa ba"

Hannu Mama ta ɗaga sama.

"Al-hamdulillah Allah mun gode maka"

Ƙanensa yayi dariya yana faɗin

"Mama ke da baki son ta"

"Ai suma ba dan Allah zasu aura masa ita ba, kai kana ganin masu kuɗi kamar Alhaji Usman zai yarda Ƴarsa tayi aure irin gidan nan idan ba da wani dalilin ba"

Asim ya sauke ajiyar zuciya kana yace

"Wallahi haka kowa ke faɗa, ni kwata-kwata ma ta fitar min a rai, kawai dai zan aure ta saboda na fita kunyar masu ganin kamar ɓa zata iya auren mutun iri na ba"

Mama ta mere baki

"Wallahi ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba, da abun nan be faru ba ba zasu taɓa yarda kmsu barta ta aure ka ba, Amman wannan shi ake cewa gobarar ti-ti ko ba komai dole dai a kira ka da surukin Alhaji Usman kuma ko yaƙi ko ya so dole ne ya samo maka wata hanyar, kuma Allah kaɗai yasan ribar da zaka ci akan wannan auren"

"Haka abokaina ke faɗa, wai wata hanyar ce Allah yayi min"

"Sosai tun dai baka ci amanarta ita ta nemi ta ci taka ai dole Allah ya saka maka"

"Yanzu wannan kuɗin tace min aje a haɗa lefe dasu kuma da su zan kama gidan hayan da zamu zauna a katsina"

"Amman Ibrahim zaman ka a nan be fi ba? Karatun ka fa?"

"Can ɗin zai fi Mama, kin ga zan samu sana'ah mai ƙwari, kuma ƴan'uwanta basa zasu sa mana ido a zamantakewar mu ba, idan muna da shi aci idan babu a haƙura, babu wanda yasan mun ci ko ba mu ci ba"

ZAGON ƘASAWhere stories live. Discover now