ZK___30

2K 193 6
                                    

NOT EDITED ⚠️

Ƴan ƙuɗin da suka mata saura a jakarta, da kuma dubu ashirin ɗin nan Hajiyar gidan ta bata, su ne take ta maneji ta su tana siyen abinci.

A kullum gidan su Mardiya take kwana, wani lokacin har zanenta take ɗaurawa, kamin ta ɗinka kala biyar a cikin kuɗin. Tayi ta zuba ido tana jiran kuɗin Anty Amarya har ta gaji, tun tana sa ran zata ta kira wayar har ta gaji da jiran ta fara tunanin wata mafitar.
Da ta fito daga gida kai tsaye ta nufi gidansu Hajiya Saratu, har ta isa zuciyarta na nuna mata illar abunda zata yi, ko ba komai zai nisanta ta da Ubangijinta, sannan duk wanda yasan abunda ta aikata mutuncinta zai zube a idonsa, ashe Allah zai jarrabeta da wani matsi har kuma ta nemi tsaɓa masa, idan har ta yi haka bata kasance cikin nagartaccin bayi ba.

Juyar da fuskarta tayi gefen ti-ti tana kallon motocin dake kai da kawo, hawaye na silalawo daga idonta, wani bangare na zuciyar yana ƙoƙarin rinjayarta akan idan har ba ita ba, bata da wata mafita, babu kuma wanda zai taimake ta sai ita. Haka ko wane bawa zuciyarsa take nasalta masa alheri da sheri duk ɓangaren daya rinjaye ka shi zaka aikata.
Hannu ta kai ta share hawayenta, tana mai jin ƙyamar abun a ranta, yanzu idan taje garin aikata ta mutu fa? Me zata cewa Allah? Haƙiƙa an jarrabi wasu gabaninta da suka yi haƙuri kuma sai Allah yayi musu mafita, kuma bayan ita za a jarrabi wasu a bayanta, haka Ubangiji yake jarraba bayinsa dan ya auna imaninsu da kuma yarda da ƙaddara.

"Haƙiƙa za mu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawayar dukiyoyi da rayuka, da ƴaƴan itatuwa , ka yi albishir ga masu haƙuri (Wajen jure waɗannan jarabce-jarabcen) Waɗanda idan masifa ta same su sai su ce INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN ma'ana :- mu ga Allah muka fito kuma a gare shi za a maiyardar mu. Wanɗannan gafara da kyakkayawan yabo daga Ubangijinsu sun tabbata gare su, da rahama kuma waɗannan sune shiryayyu." (Baƙara: 155-157)

Tuna waɗannan ayoyin ya ankarar da ita abubuwan data manta, ji tayi kamar an tsikareta, gashin jikinta ya tashi, a nan ta soma tambayar kanta, dan me zata yarda zuciyarta ta rinjayeta ta tsaɓi Ubangijinta? Ta fita daga waɗancan bayin da Allah ke yabo? Ashe Ubangijinta be mata dukan gata ba? Ashe daman Imaninta ƙanƙane ne?

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"

Ta furta a fili, har sai da mai Napep ɗin ya kalleta.

"Hajiya lafiya dai?"

"Lafiya ƙalau dan Allah juya da ni ka kai ni babbar Asibiti"

"To amman fa wasu kuɗin zaki sake biya"

"Na ji mu tafi"

"Tau Hajiya lafiya kike kuka?"

Sai a lokacin ta tuna da hawayen dake fuskarta, sa sauri ta share hawayen ba tare data ce masa komai ba har suka isa asibitin, sannan ta fita ta ciro kuɗinsa ta ba shi.
Ko da ta shiga cikin ɗakin Asim na zaune, kamsa ya kumbura sosai har idonsa ɗaya ya liƙe, hankalinta ya tashi dan yanzu wannan kumburin ya fi na jiya.
Kusa da shi ta zauna zuciyarta cike da tausayinsa, har idaniyarta na ƙoƙarin zubar masa da ƙwalla.

"Asim kaga har yanzu Anty bata kira ba, kuma bata aiko ba, ni kuma bana da wata mafitar, ga kuɗi da ake bina ma ban san yadda zan yi ba, wannan kumburin naka yana tsorata ni"

Ya matse ƙallah data cika masa ido.

"Namra ko gida za mu koma ne?"

"Idan mun koma za su ce mun kwaso ciwo mun dawo"

"Likita yace idan ba allura nan aka min ba yana da wahala naji sauƙi da wuri"

Hannayenta tasa ta rumgume shi tana kuka. Shi kuma a take yaji sha'awarta ta saukar masa, ya kai hannu yana ɗan shafa ta. Data anƙaro da abunda yake nufi da ita sai tayi saurin ɗagowa daga jikinsa.

ZAGON ƘASAWhere stories live. Discover now