NOT EDITED ⚠️
Bata taɓa sanin gume na da zafi ba, sai a wannan lokacin, wani irin nauyi ta ji kanta yayi kamar an ɗauki duniyar nan an ɗora mata, yau ganin Hilal take ya cika ko ina na duniyar idanunta.
Yau kam ba ranar kuka ba ce, tashin hankalin daya same ta ya fi ƙarfin kuka, hakan yasa hawaye ba kusanci idonta ba, ashe abu mai sauƙi ake ma kuka, ta kasa yarda yau ita ce Hilal ya kama dumu-dumu ba."Kin san kina da HIV kike ƙoƙarin ɓoyewa Rashida? Do you know what lokacin dana ɗibi jinin ki result ɗin ba ɓata yayi ba, nace miki haka ne saboda ban yarda da abunda idona ya gani ba, na dawo na ɗibi jininki da na yarana da na Kalsoom nawa dan na gwada, so that na tabbatar idan da gaske kina ɗauke da cutar ne, amman ke kin san kina ɗauke da cutar kika bar ni ina kusantar ki?
Da ba dan wanann cikin ba, da sai mu ɗauki dogon lokaci a tare da dake baki faɗa ba right? What if all of us mun kamu da cutar nan?"
Ƙiri-ƙiri tayi masa da ido, cikin ƙarfin hali ta cira ƙafarta da tayi mata mugun nauyi ta tako ta ƙaraso kusa da shi.
"Kana tabbacin ni ce kaɗai nake ɗauke da cutar? Kasan ta ina cutar ta shige ni? Miyasa idon ka zai rufe har haka?"
"Ke da kan ki kike zargin kan ki, dan me zakiyi ma Doc Sabo transfer 100,000k? Dan me zaki ce idan ya kawo jinin kamin ya auna ya kira ki? You late Rashida ko da kika kira shi na riga na kai jinin amman yaƙi ya faɗa miki saboda ya san ni kamin ya sanni kuma ya san aikinsa, daman nasan ziyarar da kika kawo min ɗazu a office bata banza bace cox na lura dake kwata-kwata hankalinki baya jikin,
Bincike da kika min da tambayoyin da kika min ya tabbatar da akwai wani abu, and now what kin sa abu a tea ki bani nasha so that kiyi iya binciken ki ko? To bari na faɗa miki if something happens to my wife hmmm you're in trouble"
Sai a yanzu hawaye suka samu damar cika idonta har suka silalo zuwa kumatunta.
"Saboda na san idan kasan ina da HIV ba zaka faɗa min ba, idan har ya tabba ina da HIV Hilal to ta hanya ɗaya na same shi, wato sex kuma wani namiji be taɓa kusantana ba sai kai, a lokacin dana bar ka ya kusance ni ban san komai ba, sai a ɗazu nasa an nemo min Doc Sabo saboda na tabbatar idan har da gaske ina cutar ne, do you know who i try to protect? You and your dirty wife, Asmee told me everything about your bride but very soon gaskiya zata yi halinta, kuma ba zan taɓa yafe mu ku ba, aje ayi gwajin"
Tana kai nan ta raɓa gefensa ta wuce cikin falon. Juyowa yayi ya bita da kallo zuciyarsa na raya masa abubuwa da dama.
Kalamanta basu kama zuciyarsa ba, amman suna ƙoƙarin zaunawa akansa, what he believe shi dai yana da protection ɗin da ba kasafai cutar zata yi saurin kama shi ba, ko baya da protection, he's Doctor ya san cutar bata saurin kama namiji kamar mace, dan namiji ɗaya mai hiv zai kwanta da mace goma to dukkan su sun zama patient living with hiv, wato sun shiga sahun masu dauke da HIV acikin al'umma.Amman mace ɗaya mai HIV zata kwanta da namiji 10 a rana, abu ne mai sauki namiji 2 ko 3 suka mu da wannan ciwon mai karya garkuwar jiki. Namiji zai iya daukan HIV kawai idan yana da wata kafa a gabansa abunda ya shafi kurji, yanka ko tsaga.
"He's lie"
Ya furta a hankali, yana murza saman goshinsa, zuciyarsa ta kasa yarda da zancen ta, duk da yasan Kalsoom take nufi, dan ita daya auna jininta be nuna haka ba, amman yasan result ɗin zai fito kuma dole gaskiya tayi halinta.
Shigowa yayi cikin falon cikin tunani da sarƙaƙiya, a saman babbar kujera ya zauna, ya dafe kansa, ɗaurewar da kansa yayi shi ya hana shi bachi har safe.
Har yayi sallah asuba ya dawo, be ji motsin Kalsoom ba, ita daya san wani lokacin ma takan riga shi tashi, a falon ya zauna yayi addu'o'insa sannan ya shiga ɗakinta, yadda ya tararda ita kwance rigingim har sai da ya tsorata, wani irin ninshari take kamarmacijin nan mesa na bachi, yayi mata girgizar duniyar nan amman ina, in ma ban da ƙara nauyin bachi babu abunda take.
YOU ARE READING
ZAGON ƘASA
Mystery / ThrillerThe Story Of three family. NAMRA FAMILY. DR. HILAL FAMILY. KALSOOM FAMILY. Sunan Novel ɗin *ZAGON ƘASA* Green snake under green grass, people with two colors. A tension, Schemed Novel of slut. Witness to regret. Witness to love. Witness to tears...