ZƘ___16

2.3K 186 2
                                    

Natsuwa tayi sosai ta tattara dukan hankalinta ta mai da gurin takardar, sannan ta buɗe ta soma karantawa.

_SALAM_
         MY DEAR NAMRA.

Na zo gidan ku ance min baki nan, na kira wayarki ban samu ba, mahaifiyata kuma ta shaida min kina nema ma, ban san ta yadda zan iya ganin ki ba amman ga sabon number waya na ki kira ni dan Allah. 08036126660

Urs ASIM.

Wani dogon ajiyar zuciya ta sauke, ta rumgume takardar a ƙirjinta ta lumshe ido, tana sauraren bugun zuciyarta.
Ta ɗauki daƙiƙa goma zuwa shabiyar kamin ta buɗe idon, ta tashi ta nufi ɗakin Maryam.
Dariya ta tararda Maryam na ƙyalƙyala kamar wata sabuwar mahaukaciya, har ta zauna kusa da ita bata san ta zauna ba, tana taɓa ta ta zabura.

“Wayyo Allah na”

“Ke lafiyan ki?”

“Wallahi wani littafi ne nake karantawa mai shegen dariya”

“Littafi kuma ai ke Allah be raba ki da karatun littafai ba”

“Wallahi Anty Namra yayi daɗi kamar me, da zaki karanta kema da kin sha dariya”

“Idan na samu time zan karanta, meye sunan littafin?”

“Noor na Khadeeja Candy”

“Okay ni dai ara min wayarki wani abu”

“Ke dai ce zaki kira Asim ba wai kiyi wani abu ba”

“Naji ni dai bani”

Sai da tayi saving ɗin page ɗin, sannan ta miƙa mata wayar tana zolayarta. Namra dai bata ce mata komai ba ta tashi ta fice tana faɗin.

“Ina fatar da Akwai kuɗi a ciki”

“Kai kaji ki da wata magana, manyan Babe's irin zasu zauna waya ba kati, taf mune tare da manyan samarin garin nan fa, kin san ko dan karya dole a saka mana manyan kati ”

Da dariya Namra ta fice, ta koma ɗakinta. Takardar ta ɗauko ta saka Number ta danna kira. Ringing biyu zuwa uku yayi picking da sallama.
Sai da ta lumshe ido ta buɗe da murmushi sannan ta amsa masa.

“Wa'alaikassalam. Asim”

“Namra...”

Daga cikin wayar tana jin lokacin daya sauke ajiyar zuciya, sannan yace

“Namra wai Abban ki ya yarda na aure ki?”

Kai ta ɗaga masa kamar yana gabanta, hawaye suka silalo mata.

“Ya yarda Asim, shiyasa na neme ka”

“Alhamdulillah”

“Ina kaje Asim? Ashe zaka iya tafiya wani guri ka bar ni?”

“Namra idan mun haɗu zamu yi magana”

“Yaushe zaka zo?”

“Ba zan iya zuwa gidan ku da sunan hira ba, sai dai mu haɗa ta layin su Azeema”

“Okay gobe da ƙarfe tara dan Allah”

“Allah ya kai mu I Love You”

“I Love You More”

Daga haka ya kashe wayar. Sai ta rumgume phone ɗin tana murmushi tare da hawaye.

KALSOOM POV.

Kusan kullum sai Doc. Hilal ya kirata a waya sun gaisa, sai dai fira ce be cika zuwa ba sai jefi-jefi. Sau biyu ya taɓa kawo mata ƴaƴansa suka gaisheta ita kuma tayi musu goma na arziki.
Ana sauran sati biyu biki Doc. Hilal ya nemi ta bashi list ɗin abubuwan da zata yi na biki. Bata rubuta wasu abubuwa masu yawa ba, bayan abubuwan da al'ada ta tana da.

ZAGON ƘASADonde viven las historias. Descúbrelo ahora