ZK - 33

2.1K 190 13
                                    


NOT EDITED ⚠️

Washe garin ranar da Mama ta tafi ta dawo, guraren uku da rabi na rana. Ita kaɗai ta dawo ba tare da Hajara ba, Namra bata nuna mata komai ba ta tarbeta da far'ah tana mata sannu da zuwa.
Tana son tayi labari Namra ta tsare su taƙi ta tashi, shi kansa Asim yana son magana da ita amman ba dama, tun da Namra tana gurin.

Kamar ta san Namra bata tanadar mata komai, tun a hanya ta tayi gurin biredin ta da lemu, sai ta ta ci ta ƙoshi, sannan ta tashi ta fita.
Da kanta taje ta biya kuɗin maganin dan kar taba Namra.

Ta dawo daga biyan maganin ne, Namra ta tashi tayi musu sallama ta baro asibitin.

Har ta iso gida kuka take, tana tunanin yadda Asim yake ɓoye mata lamarin, dan ta lura da yadda suke kallon kallo da Mama, hakan ya soma tabbatar mata da abunda Anty Amarya ke faɗa mata.

"Idan har ta tabbata Asim na son yaudarata...."

Sai kuma tayi shiru ta share hawayenta, ta miƙawa mai Napep kuɗinsa ta shige gida.

*** ***
"Thank you"

Ta faɗa tana murmushi tare da kallon mutumen daya tashi daga saman kujerar ta ya nufi ƙofar fita. Sai da ya fice sannan ta kalli wayarta dake ringing, sannan ta kai hannu ta ɗauka zuciyarta na raya mata irin labarin da Asmee zata bata.

"Ƴar gari kamar kin san yanzu nake tunanin ki nace ko kin samu zuwan kuwa?"

Kuka ta fara ji kamin Asmee ta ɗora mata da zancen dalilin kiran nata.

"Rashida ina ciki matsala"

"Lafiya miya faru?"

"Wani malami ne da muke zuwa gurinsa, yana ba mu taimako, shine yanzu ake ce mana malamin yana da ciwon nan na zamani, shine tun ranar na kasa sukuni ban ma sama naje gurin matsalar ki ba"

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Asmee garin yaya? Ya taɓa sex dake ne? Ko me?"

Kuka tayi sosai har ka kasa magana.

"Ki faɗa min mana ki daina kuka"

"Ya taɓa lokacin da je neman wani taimako sai yace min sai na kawo sperm ɗin wani wanda ba mijina ba, da jinin al'ada da shi za a haɗa, ni kuma na ce masa ban san inda zan samo ba, shine...."

Ta ƙarasa da kuka

"Ke yanzu kin je an gwada jinin ki ance kina ɗauke da ciwon ne? Stop crying and tell me Asmee"

"Ban je ba, tsoro nake ji ban san wanda zan faɗawa ba sai, dan bani da ƙawa irin ki, na rasa yadda zan yi tsoron gwajin na ke, aiki ma na daina zuwa yanzu"

"Innalillahi Ya salam Ya salam"

Ta soma zagaye office ɗin tana dafe kai, da wayar a kunnenta.

"Ki kwantar da hankalin ki kinji karki faɗawa kowa, kuma karki yi abunda zai sa mijin ki ko wani ya zargi wani abu, i will call you back"

Tayi saurin kashe wayar tana tuna jininta da Hilal ya ɗiba, idai har Asmee ta kamu da cutar to itama zata iya kamuwa da ita tun da har suna using mutum ɗaya.
Faɗuwa tayi zaune zumi na keto mata ta ko'ina, hannu ta kai tana shafa kanta, tana girgiza shi kamar wani ne a gabanta.

"Ko shiyasa ya sake ɗibar jinina? Amman kuma ai da ba zai kusance ni ba, amman yanzu idan ya auna dole ya gano idan akwai shi"

A fili take furucin zuciyarta a karaye, jikinta har tsimi yake, yanzu kam hannaye biyu tasa ta dafe kanta tana tunanoma kanta mafita.

"Dole ne na dakatar dashi daga yin gwajin, kuma dole ne nima naje na bincika kai na, indai har da gaske ne Asmee kin cuce ni"

Da sauri ta tashi ta kaɗe jikinta ta fiddo hoda a jakarta ta gyara fuskarta sannan ta ɗauki jakar ta fita. Sai da ta biya ta faɗa musu fitar gaggauwa ta kamata, sannan ta fito harabar bankin ta shiga motar, ta ɗauki hanyar Asibiti.

ZAGON ƘASAWhere stories live. Discover now