ZAGON ƘASA___07

2.3K 211 10
                                    


NOT EDITED

A hannunsa ta suma, sai ya ɗauke ta ya miƙawa mazan da yake tare da su yana faɗin

"Ku shiga da ita, kuma ku tabbatar bata farka ba, har sai na dawo"

"Yes Boss"

Cikin girmamawa suka amsa, suka saka ta cikin Bus ɗin. Sai da Uzair ya ga sun bar gurin sannan ya nufi ƙofar gidan Alhaji Sani inda yayi parking ɗin Motarsa.
Bude Motar yayi ya shiga, ya ɗauko wani turare ya fesa, sannan yayi ma Motar key. Ribas yayi ya dawo ta bayan layin sai gashi a bakin gate ɗin gidan su Namra.
Horn yayi mai gadin ya buɗe masa yana gaisheshi. Guri ya samu a harabar gidan ya yi parking.
Sai ya fita ya taka da ƙafa ya isa part ɗin Abbah, dan yaga motarsa a waje, alamar yana nan kenan.
Hankalinsa kwance ya shiga falo, Abbah na kishimgiɗe yana duba jarida, Uzair ya shigo sai yayi saurin zubewa ƙasa yana kwasar gaisuwa.

Da far'ah Abbah ya amsa, yana nuna masa gurin zaman, bayan sun gama gaisawa, sai Uzair yayi shiru be ce komai ba har sai da Abbah ya kalle shi ya ce

"Uzair kana da wata magana ne?"

Abbah ya tambaya, yana mai jin son Uzair ɗin a cikin ransa, kusan ma ya fi kowa jindaɗin wannan haɗin, dan Allah ya sa masa son Uzair shiyasa komai na harkar kasuwancinsa sai ya saka shi, duk kuwa da cewar shima yana da ƴaƴa maza.

Sun-sun ya yi da kai

"A'a Abbah, akan maganar IV ne na mata, har yanzu Namra bata rubuta ba, kuma lokaci na tafiya, shine Hajiya tace na zo, na mata magana, shine nace bari na gaishe ka"

Abbah ya yi murmushi irin nasu na manya, sannan ya yi gyaran murya yace.

"Uzair sai ka yi haƙuri da lamarin Khadija, har yanzu akwai ƙurciya a tare da ita, kuma ita ba zata gane alfanun wannan auren ba har sai anyi, haƙiƙa ina son Khadija matuƙa sai dai tayi tsalle ne da ɓata rawarta tun daga lokacin data tsaya kai da fata akan lalle ita sai wannan yaron,
na bata dama na fitar da wani ta ƙyale wannan yaron amman sai ta buga min ƙafa a ƙasa ita sai Asim, shiyasa kaga na fita lamarin ta, saboda so da yawa zaka abunda mu iyaye muke hangowa ba shi ƴaƴa ke hangowa ba, a tunanin ta na yi mata hakan ne dan na cutar da ita, tun da ta nuna bata so.
Nasan anbar auren dole a yanzu, amman duk abunda na yi ma Namra ita ta jawa kanta"

Abbah ya ɗaga kai ya sake kallon Uzair da kyau yana mai nuna masa abunda yake faɗi a bakinsa shine a zuciyarsa.

"Uzairu ina fatar zaka riƙa Khadija da amana, kuma zaka nuna mata so da kulawa, irin son da zata san lallai ta yi dacen mahaifinta be mata mugun zaɓi ba, ina son ka sani duk abunda ya samu Namra ni ya sama, kuma zai taɓa mahaifiyarta, ina addu'a wannan aure Allah ya sa masa albarka, ya baku haƙuri zama da junanku"

Jikin Uzair yayi san yi sosai da kalaman da Abbah yayi masa, sai yake jin kamar Abbah ya san abunda yake son aikatawa.
Cikin rashin kuzari ya yi ma Abbah sallama, ya tashi ya fice.

Har ya iso gurin motarsa tunanin kalaman Abbah yake.

'Abunda duk ya sami Khadija ni ya sama'

Same shi ya fi tsaya masa a rai, tunani yake what if Abbah ya gane gaskiyar dalilinsa na neman aurenta? Shi kuma baya jin yana da wata mafita ta rufa ma kansa asiri bayan wannan, tun shi dai ba zai ce zai kashe Namra ba, gashi ta ce sai ta tona masa asiri.

Ya kwashe minti arba'in a gurin yana tunani, ba tare da ya sani ba. Can sai ya nufi gurin Mai gadin yayi masa magana kan ya shiga yayi masa sallama da Namra.
Cikin girmamawa mai gadin ya nufi part ɗin Anty Amarya, shi kuma ya dawo gurin Motarsa ya tsaya ransa a jagule.

In few minute Mai gadin ya dawo ya shaida masa ance gata nan zuwa. Chanji ya fiddo a aljihunsa ya miƙawa Mai gadin, sannan ya gyara tsayuwarsa yana jiran fitowarta.

ZAGON ƘASAWhere stories live. Discover now