NOT EDITED ⚠️
Haka ta cika gidan da ihu sai kuka take duk ta bi ta rikice, zuciyarta na nasaltama Asim ya tafi ya bar. Yarinyar da suke tare ne taje da gudu ta faɗawa Mahaifiyarta, sai gata ta zo da gudu cikin gidan tare da Babbar ƴarta.
Dafa Namra tayi tana girgiza ta.
“Haba ke kuwa sai kace ba musulma ba? Cewa akayi ya mutu ne?”
Cikin kukan Namra ta amsa mata.
“Ban sani ba, sun ce yana asibitin Funtua”
“Yanzu ba kuka ya kamace ki ba, tashi ki wanke fuskarki Mardiya ta raka ki, kuje Asibitin”
Da sauri ta tashi ta shiga ta wanke fuskarta ta ɗauko Hijabinta ta saka, keys ɗin gidan ma sai da Mardiya ta karɓa ta rufe mata gidan, sannan ta koma gida ta shirya sannan ta suka kama hanya Mahaifiyarsu na mata Allah ya tsare.
Keke Napep suka hau ta kai du tasha, sannan suka shiga motar Funtua.
Tun cikin Motar Namra take kuka, har suka isa Funtua, kowa sai tambayar yake lafiya, Mardiya ce kawai take iya amsawa, Namra kan ji take kamar ta yi tsalle ɗaya ta ganta gaban Asim, sam zuciyarta ta kasa aminta da be mutu ba.Suna isa cikin asibitin suka tambaya, sai a nuna musu emergency ward. Hankali a tashe ta shiga gurin, sai rabon ido take, akwai mutane da yawa a gurin ga kuma ɗakunan bata san wanda zata shiga ba.
Daga gefe ta tsaya ta kira wayar Asim, ringing biyu aka ɗauka.“Ga mu cikin Asibitin yana ina?”
“Yana ciki suna duba shi, bari na fito yanzu”
Ba a ɗauki dogon lokaci ba, sai gashi ya iso gurin sanye da uniform ɗin road safety. Sai ya miƙa mata wayar hannunsa yana faɗin
“Hajiya ki kwantar da hankalin ki be mutu ba, sai dai ɗan abunda ba za'a rasa ba, ba shi kaɗai yayi haɗarin ba tare da wata babbar mota da kuma ƙananan motaci uku, duk babu wanda be ji ciwo ba, motar ma da yake ciki duk ta ƙone”
Wani sabon kuka ne ya dawo ma Namra.
“Dan Allah da gaske yana da rai?”
“Ko da muka kawo shi nan yana da rai, mutun biyu ne kawai suka rasa rai ciki, amman shi yana da rai”
“Na gode...”
“Ba komai, amman ki kwantar da hankalin ki babu abunda zai faru”
Hawayen idonta ta share, ta fidda wayarta ta saka number Anty Amarya ta kira ta, sai da kiran ya katse bata ɗauka ba, sai ta sake kiranta, sai a uku ta ɗaga.
“Assalamu Alaikum, Namra kin kira ina sallah”
“Anty Asim yayi haɗarin mota yanzu haka muna asibiti”
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Da sauki dai ko?”
“Eh sun ce be mutu ba, amman har yanzu likitoci suna kansa”
“Wace Asibitin?”
“Specialist dake Funtua”
“Toh ki kwantar da hankalin ki kin ji? Kin san abunda Allah ya ƙaddara ma bawa baya wuce shi ko? Ki daina kuka ke ma malama ce Namra, ki fawwalawa Allah komai”
“Toh Anty”
“Kin kira mahaifiyarsa?”
“A'a”
“Toh ki kira ta yanzu ki faɗa mata, Allah ya bashi lafiya, gobe zamu zo inshallahu”
“Tau Anty”
Daga haka ta kashe wayar. Ta ɗauki tasa wayar ta kira number Mahaifiyarsa. Ringing ɗaya ta ɗauka tana faɗin.
“Yanzu nake cewa a sawo min kati na kira ka, na ji ko ka isa lafiya”
YOU ARE READING
ZAGON ƘASA
Mystery / ThrillerThe Story Of three family. NAMRA FAMILY. DR. HILAL FAMILY. KALSOOM FAMILY. Sunan Novel ɗin *ZAGON ƘASA* Green snake under green grass, people with two colors. A tension, Schemed Novel of slut. Witness to regret. Witness to love. Witness to tears...