2

1.1K 100 4
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM💘*

PAGE 2




Dr ya girgiza kai tare da fadin mace aka samu, wani irin shock Alh Ibrahim yaji Lokaci daya duk wani jini dake gudana a jikinsa Ya tsaya dan bakin ciki da takaici, saida Dr ya tabashi sannan yayi firgit Dr yace zaku iya shiga, Dr na fadin haka yayi gaba abunsa, Alh Ibrahim kam juyawa yayi da nufin barin asibitin ba tare da yaje yaga matar tashi ba da kuma yar da aka haifar mishi ba, mama ce ta kira sunanshi wanda yasa ya tsaya cak, karasowa tayi kusa dashi tare da daura hannunta akan fuskanshi tana shafawa tace Ibrahim kaje Kaga matarka, cikin bacin rai yace mama mai zan mata mai zan mata bana bukatar ganinta ita da abunda ta haifa, mama na tabbata tunda kika haifeni Nasan Nima zan haifi d'a namiji, y'a mace ba komai bace bata da amfani a wajena Ina bukatar d'a namiji wlh inda zan sami namiji guda daya da bazan so kara haiyuwa ba domin shi kadai Ya isheni Ina bukatar wanda zai gajeni mai kula da duka harkokina, mai mace zata iyamin, mama kuka takeyi tare da fadin kayi hakuri wasu matan suna haka sai su haifi mata biyu sannan su haifi namiji, jin haka yasa ya kalli mama da sauri alaman dagaske? Kai ta daga mishi alaman eh tace muje kagansu bai musa ba yace muje.



Ummi dake window duk taji abunda suke fada jin zasu shigo yasa ta koma da sauri ta kwanta, koda suka shigo Alh Ibrahim baiko Kalli inda yarinyar take ba, sai ummi da yayi ma ya jiki, ta amsa da lafiya bai kara cewa komai ba, sai mama ce ta katse shurun da fadin baka dauki babyn ba gata kaman Kai, baiso tashi ba amma haka Ya daure ya tashi ya nufi yarinyar yana ganinta yaga sak shi kaman anyi kaki, daukanta yayi yarinyar ta saki murmushi wanda ya kara mata kyau, baiyi ko minti daya da daukanta ba Ya ajiyeta, tare da fadin zashi Gida anjima zai dawo, aka bar ummi daka ita sai baby da mama, Bayan fitanshi kukan da ummi take boyewa ya fito amma bamai sauti takeyi ba dan Kar mama taji, *MIYE ILLAR Y'AY'A MATA* da mijinta yasa yake kyamarsu koya manta da mace dana miji Allah ne ke badawa, wasu na nan na neman haiyuwa ko wani Kala ne amma Allah bai basu ba, shi gashi Allah Ya bashi amma yana fushi da kyautar Allah lallai da yasan irin tausayin da y'ay'a mata suke dashi da ko kadan da baiyi burin samun d'a namiji ba, kallon yarinyar tayi cikin tausayi wacce take bacci abunta, lallai tana tausayawa yaranta musamman zarah data fara girma bata samun wani gata na uba ko sakewa data samu cikin nan nema ya fara Dan sakema zarah dan a zatonshi namiji zata haifa gashi mace ta haifa haka taita tunani tare dajin tausayin rayuwan y'ay'an nata.



Kwananta daya aka sallamesu tunda Alh Ibrahim Ya tafi bai dawo ba sai dai ganinsu da yayi a gida, zarah na ganin ummi ta nufeta da gudu tayi hugging dinta tana dariya, Alh Ibrahim kam ko kallonsu baiyi ba, mama ta taimaka mata suka haura sama zuwa dakinta, Alh Ibrahim fushi yake Sosai wanda ya kasa boyuwa saida Ya fito fili, duk yanda mama taso ta mishi dan ya sauko amma Abun ya faskara Dan haka ta kyaleshi, ummi yanda taga baya kulata Abun ya dameta Sosai gashi ita ba dangi ba balle ta kirasu su dibe mata kewa tun tana karama iyayenta suka rasu gashi ita daya suka haifa, bata san inda zata ga dangin mamanta ko babanta ba dan ance daka nijar suka zo, riqonta ya dawo wajan liman din anguwansu a wajanshi ta taso har Alh Ibrahim Ya ganta yace yana Sonta ya aureta gashi bata son fadama limam matsalanta dama inna adama na nan ne matar limam din wacce ta dade da rasuwa tunda ta rasu bai kara aure ba wannan kenan shine labarin ummi bari muji na Alhaji Ibrahim shima.




WAYE ALHAJI IBRAHIM?

Alh Ibrahim Dane ga mlm ayuba,mlm ayuba manomi ne yana da kudi Sosai yana da mata fatima suna zaman lafiya, yan asalin garin kaduna ne zazzagawa kenan amma suna zaune a u/kanawa, suna da yara biyu Ibrahim sai kanwarsa hindatu wacce suke kira da hindu, tana aure a garin adamawa, Ibrahim yayi karatu akan fannin business Dan haka yaba mahaifinshi shawara akan su bude company na sana'an hannu mahaifinshi Ya yarda inda aka fara ginin katon company din mai gefe daban daban, akwai inda ake hada atamfofi da shadda, akwai gefen da ake hada kayan kwalliya akwai gefen da ake hada kayan hannu na yara wato wanda ake saqawa, Bayan an gama komai mahaifinshi yace ya mallaka mishi company din halak malak, tunda ya mallaki company din yake samun mahaukanta kudade inda Ya fara gini a anguwan rimi ya Gina wani mahaukacin Gida, suka koma tare da iyayenshi yace ya Gina gidan shida yaranshi dazai Haifa koda sunyi aure bai yarda suje ko Ina ba, basu dade da tarewa ba Ya auri ummi, shekaranta daya ta haifa zarah, tun a lokacin yake nuna mata ra'ayinshi akan son haiyuwan d'a namiji, shekaran zarah uku mlm ayuba ya rasu, sunji mutuwarshi Sosai Dan abunda Ya bari aka raba musu gado haka rayuwa taci gaba da kasancewa, tun zarah na karama bata wani samun kulawa wajan babanta Dan shi bashi da burin haiyuwan y'a mace Dan yace wahala ce y'a mace wannan kennan yanzu zamu dawo kan labari.......










     *vote*
*comment nd share*

*maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now