24

525 33 1
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 25






Tace kar kiyi tunanin zan amshi wani abu daka gareki, bazan taba amsan abu daka wajan wanda sukai sanadin mutuwar mijina ba, dan Allah karki kara shiga cikin wani al'amari na na ro'keki badan niba..... Ummi ce ta daka mata tsawa tare da fadin miye haka zainab sa'arki ce!? Sannan ki daina wannan tunanin domin Amina bata da hannu wajan kashe miki miji, cikin kuka tace ummi itace ma take da hannu Sosai domin tasan komai tasan yayanta shine ya kashe min miji amma taki fad'a duk kuma saboda ita yayi, Amina tace zainab Wlh ban San saleh zai kashe yazeed ba ban taba tunanin haka ba dan Allah ki yafe min badan niba.... Da gudu zainab ta haura Sama Tana kuka Yan uwanta mata suka mara mata baya Amma Kafin suje harta rufe kofar, haka suka barta.



Amina jiki a sanyaye tabar wajan, alh Ibrahim zama yayi wanda kwana biyu baya cikin kwanciyan hankali, domin da tunanin y'arsa yake kwana yake tashi, mama ta kalleshi tace lafiya kuwa Ibrahim naga kayi shuru ka zabga tagumi, d'ago dakai yayi cikin damuwa sannan yace mama Wlh Ina nadaman abunda na aikata na tsanan y'ay'a mata duk wannan abunda su Amina da saleh suka aikata lefi nane, Harda halin da y'ata take ciki a yanzu, mama tace wace y'ar taka? Yace mama yarinyar Amina bata mutu ba, mama tace kaman ya? Labarin abunda ya faru yaba ma mama da kuma ummi da hindu dake zaune, sai yaranshi mata dake sama suna kallonsu Suma duk sunji abunda ya faru, kowa ya girgiza da Abun da saleh yayi ma yar kanwashi daya kaita gidan karuwai , mama tace ya kamata muje mu dawo da ita gida sannan shi kuma saleh tunda yana hannun hukuma zasu hukuntashi dai dai da abunda yayi...... Muryan zainab sukaji Tana fad'in nasa a sakeshi domin bana son hukuma ta hukuntashi nafi son Allah ya hukuntashi yanzu haka zanje inyi signing ne na rufe case din, alh Ibrahim yace zainab kin san abunda kike fad'a kuwa? Tace eh na sani Abba, alh Ibrahim yace karki kuskura ki fara sakawa a sako shi, ki bari a hukunta shi, tace Abba duk hukuncin da za'a ma saleh Wlh bazai sa in daina jin ciwon abunda yayi min ba, dan Allah Abba ka barni inje inyi signing nafi son Allah ya hukunta sa, Abba shuru yayi can yace muje tare, haka suka tafi ita da alh Ibrahim har police station inda tayi signing aka rufe case din tare da sakin saleh.



Alh Ibrahim da mama dasu khairat da da zarah sai ummi da Amina suka shirya domin zuwa dawo da y'ar amina Mai suna rahma, zainab dai tana gida ita da Anty hindu da aysha, koda su alh Ibrahim suka je garin a waje suka ganta Tana shan Fanta ga wasu maza nan a zagaye da ita suna ta manna mata kudi, Amina kuka ta Fara tare da fadin saleh ya cuceta ya bata mata rayuwar y'a, rahma dake zaune ta hango alh Ibrahim da sauri ta tashi ta nufeshi tana fadin au ka dawo ne, kallon su mama tayi da suke ta kallonta, ga Amina dake ta faman rusgan kuka, ummi ce ta matsa kusa da ita tace dan Allah muna son muyi magana, kallon ummi tayi wacce tayi mata kwarjini tace muje cikin gidan suka shiga inda maza da mata keta shaye shaye, wani d'aki suka shiga suka zauna, ummi tace da Farko dai Kinga mahaifinki nan ta nuna alh Ibrahim sannan ga mahaifiyarki ta nuna mata amina dake ta faman rusgan kuka, kallon Amina tayi na wajan minti biyu sannan tace bani da iyaye domin kuwa inda inada iyaye bazasu taba kawo ni nan ba dan haka ku tashi kuje kawai, zarah tace babu inda zamu sai tare dake, domin ba zamu ci gaba da kallonki cikin wannan rayuwan ba dan haka kizo mu koma Gida tare, rahma tace babu inda zani na fad'a muku banda iyaye ban da iyaye muryan saleh sukaji yana fad'in sune iyayenki, kowa waigowa yayi yana kallonsa, yace rahma nine na jefaki cikin wannan halin Labarin abunda Ya faru ya bata, rahma kuka ta farayi tare da fad'in Kun cuceni Kun bata min rayuwa, kallon Amina tayi tace ban zaci koda a mafarki uwa zata ma yarta haka ba dan kawai miji baya bukatar y'a mace, Amina tace dan Allah ki yafe min Wlh kullum da tunaninki nake kwana nake tashi Wlh Ina sonki, zarah tace sis kiyi hakuri kizo mu koma Gida tare domin can ne yafi dacewa dake ba wannan kazamin wajan ba, alh Ibrahim ya kamo hannun rahma yana hawaye yace duk laifi nane dana nuna kyamata akan y'ay'a mata , na manta Allah shine mai badawa kuma Mai hanawa, duk son d'a namiji na sai gashi Allah ya nuna min ban isa ba sai ya bani y'ay'a mata har biyar, ki yafe min rahma, cikin kuka ta Fara kokarin yin magana amma ta kasa bakinta sai rawa yake alh Ibrahim ya janyota jikinshi ya rungume y'ar tasa yana kuka saida ta nutsu sannan tace Ina jin kunyan abunda na aikata ranan daka Fara gani na Abba dan Allah ka yafe min yace babu komai yanzu mu tafi Gida tace bari ta dauko kayanta, alh Ibrahim yace sam baya bukatar ta dauki wani abu daya cikin wannan gida haka suka fita, sale ya matsa kusa da alh Ibrahim yana fadin nagode da kasa aka sakeni Ina son kamin izini in zauna daku cikin gidanka.......











*vote*
*comments nd share*

*Maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now