6

947 90 2
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*



*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM💘*

PAGE 6



Kaman yanda mama tace hakan ko akayi Washe gari akaje neman auren Amina inda yayanta saleh ya amince kuma baiyi wani abu da za'a gane son kudinsu a fili ba, nan take aka bada sadaki inda magabatan Alh Ibrahim suka bukaci a daura auren ranan juma'a saleh yace Kai Anya hakan zai yihu kuwa, mufa talakawa ne Ina zamu iya hidiman biki nan da kwana bakwai, daya daka cikin magabatan Ibrahim yace karka damu basai kunyi komai ba alhaji Ibrahim yace shi zaiyi komai dan haka ku amince kawai, saleh yace Ayi haka kuwa? Sukace karka samu damuwa burin mu shine Allah ya basu zaman lafiya saleh ya amsa da Ameen, Bayan sun tafi amina ta shigo dakin da sauri tana murna ganin kudi dumus masu uban yawa yasa takai musu cafka amma Kafin ta dauka saleh ya kwashe bata fuska tayi tare da fadin ka bani kudin mana, yace Ina amina wannan nawa ne Dan haka kibar cewa in baki, tace amma ba sadaki na bane? Yace shine keda zaki fara samu da yawa ai kyabar min wannan, tace naji amma kadan ban wani abu, tsaki yayi tare da ciro duba biyu ya bata kallonshi tayi galala yace in baki so bani, amsa tayi dan tasan halinsa, matarshi ya kwadama kira tare da jefa mata Dari biyar yace aje a siyo komai na abinci Ayi mai dadi yau tace toh tare da dauka ta fita.


Yau Friday aka daura auren Amina da alhaji Ibrahim, Bayan an daura aure da daddare kaman yanda al'ada yake aka Kai Amara cikin makeken gidan Alh Ibrahim, ummi kam sai jin guda tayi da hayaniyan mutane Koba ta tambaya ba tasan mijinta ne Ya kara aure dan haka take ta kuka a daki domin yanzu ta tabbatar baya kaunarta tunda gashi aure ya kara ba tare da saninta tana cikin kuka zarah ta shigo itama kukan tasa ganin yarinyar na kuka yasa ummi yin shuru tare da goge ma zarah hawayen nata itama, zarah tace ummi Abba ya kara aure yanzu ya daina sonki,ummi mai yasa Abba ya tsanemu kodai muba yaranshi bane.....  Da sauri ummi ta toshe mata baki tace ku yaranshi ne Kar in kara jin kin furta wannan Kalman daka yau Kinji na fada miki, cikin kuka ta daga kai tare da fadin insha Allah ummi Kema ki daina kuka,murmushi ummi tayi tare da tambayan Ina su aysha? Tace suna daki suna bacci, ummi tace toh Kema tashi kije ki kwanta, tace toh tare da fita Bayan fitan zarah ummi taci gaba da kukanta saida tayi mai isarta sannan bacci barawo yayi gaba da ita.



Amina tana mulki a gidan Alh Ibrahim iya son ranta domin duk wani kulawa tana samu, saleh yana ta mata maganan akan shima yana son Ya dawo gidan Dan ya gaji da zama a gidanshi tace mishi Ya bari ba yanzu ba in lokaci yayi zata sa ya dawo, kwanci tashi ba wuya amina aka sami ciki, zo kuga murna wajan mama da Alh Ibrahim amina bata aikin komai yayin da ummi ta zama kaman yar aikin gidan Alh Ibrahim baya kulata, komai Amina sai abunda tace, wata rana su zarah suna wasa harda khairat da take dan tafiya wani kwaro ya shige ma khairat ido, tasa kuka da sauri zarah ta dauketa sukai ciki wajan ummi idon Kafin kace me harya dan kumbura, ummi tace zarah maiya sami idonta? Tace ummi suna wasa dasu aysha kawai tasa kuka, Jin kukan khairat din ya tsananta yasa ummi fita da sauri zuwa falo inda ta Sami su Amina da mama da sauri mama tace suje asibiti cikin masu zuwan harda amina ana zuwa akai emergency da khairat wacce take ta kuka, Dr Ya dauki lokaci Kafin ya fito inda yace su sameshi office, Bayan sun shiga office din ya fara musu bayani idonta ya samu matsala dole sai an bata glass Indai anaso ta dinga gani,ummi babu abunda take sai kuka amina ce ta iya cewa a yanka mata Toh hakan akayi aka bata na yara,  ummi tana kuka tana fadin abubuwa Kala Kala daka wannan sai wancan Allah ka bani ikon cin wannan jarabawan, gidan suka koma suna zuwa suka Tarar da Alh Ibrahim yana ganinsu Ya fara fada Wai dan mai yasa amina zata bisu in cikinta ya sami matsala fah, ummi najin haka ta wuce ciki ita da yarta shi bama ta matsalan yarsa bane damuwanshi cikin dabai zo duniya bane ya damu dashi, ummi kuka take Sosai inda zarah ta labe ta wajan window tana kallon ummi babu komai cikin zuciyar zarah sai tsanar mahaifinta.


A kwana a tashi babu wuya cikin amina ya cika wata tara harma ya Dan gota yau tunda amina ta tashi take tajin ciwon baya Abun dai taga bana karewa bane ta fadama Alh Ibrahim nan da nan ya dawo Gida suka nufi asibiti suna zuwa akace haiyuwa ne, Gida ya koma dan a kwaso kayan haiyuwa sannan su tawo da mama, Kafin ya dawo harta haiyu inda itama matar saleh aka kawota haiyuwa Dan asibiti daya suke zuwa amma ita da Abun dake cikinta duk sun rasu koda suka dawo saleh ne zaune yana ta rasga kuka, Alh Ibrahim hankali tashe yake tambaya lafiya? Cikin kuka saleh yace albishirinka Alh amina ta haifi d'a namiji, wani irin murna ne Ya kama Alh Ibrahim tare da fadin zan baka goran albishir in mun koma Gida Toh amma wannan kukan fah?saleh yace ni tawa matar ta rasu ita da abunda ke cikinta, salati Alh Ibrahim yayi tare da jajanta mishi ranan aka sallami amina inda aka sallaci gawan matar saleh aka birneta a gidanta na gaskiya, duk da anyi mutuwa saida akayi shagalin suna amma sun kira shi da sadakan bakwai amma irin abubuwan da akayi da kashe naira kaman babu gobe ya isa Ya nuna maka murna suna ake ga amina Anci kwalliya Sosai ansha gwala gwalai, anyi ma yaro Huduba  da suna Umar faruk, tun daka lokacin mutuwar matar saleh yake kwana gidan Alh Ibrahim inda amina tace ma mama ya kamata Ya zauna dasu saboda kadaici, mama ta amince tunda gidan babban Gida ne akwai dakuna da yawa Sosai, Dan dama Alh Ibrahim yayi tsarin gidan ne wanda zai iya zama shida yaranshi maza sai gashi mata Allah yake ta bashi sai yanzu Ya sami d'a namiji, duk wani kayan wasa in Alh Ibrahim ya gani saiya siyo ma faruk shi khairat tana son wasa da kayan amma babu dama, gaba daya duk wani abu mai muhimmanci akwai inda Alh Ibrahim ya ware Dan ajiyewa harda kudi koda wani abu ya taso baya nan, key din dakin yaba mama, inda mama ta bama amina key din dakin amina yanzu an kara zama babban mace sai abunda tace Idan ummi na bukatar abu wajanta zata.




Yau ummi na zaune limam yazo gidan Wanda Ya riqe ummi Bayan rayuwan iyayenta yace mata zai Koma kano da zama wajan danginsa ummi nata kuka haka dai sukai sallama da Idan yaje can zai kirata, haka rayuwa taci gaba ma ummi cikin rashin jin dadi da walwala ga Amina taita sa ummi aiki Kala Kala in ummi ta gama wannan tace tayi wannan haka dai kullum suke ummi bata da lokacin hutu in zarah na Gida shine take taya ta in kuma bata nan taje skul ita takeyi, hindu kanwar Alh Ibrahim mijinta yayi hatsari ya mutu itama ta dawo gidan haka suka hade Kai ita da amina suna wahalar da ummi........  Hmmm mai karatu yanzu Labarin zai soma kudai kuci gaba da bina sannu a hankali tare da suburbodo comments dan shine zai bani karfin gwiwan yi muku posting akan Lokaci.






    *vote*
*comments nd share*

*maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATADonde viven las historias. Descúbrelo ahora