41

595 40 3
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 41





Mutumin ya fara magana kaman haka ranan da Abun ya faru Ina wajan wancan dutsen a kwance duk ina kallonsu amma su basa ganina lokacin da faruk da alh Ibrahim suke magana akwai wata igiya dake kusa da kafarshi yana danja baya kafarshi ta shiga cikin igiyar Aneesa taja igiyar Wanda shine silar fadawanshi duk da bai fad'a kai tsaye ba ya ri'ke Abun gadar faruk ya mi'ka Mai hannu yana son ciro shi amma ya kasa wanda dole yasa Alh Ibrahim ya fad'a duk ina wajan ina kallonsu, Aneesa tace faruk ka kashe mahaifinka faruk ya rud'e matuka Aneesa ganin haka ta d'aura Mai hukuncin kisa din wanda bashi ya aikata ba, bayan sun bar wajan, na sami number din Aneesa na kirata akan nasan komai ta tsorata Sosai tace Tana son mu had'u, bayan mun had'u na nuna mata video din abun daya faru wanda a lokacin na d'auka da y'ar wayata, ta tsorata Sosai tace in rufa Mata asiri zata dinga bani kud'i duk wata jin haka na amince Toh kunji yanda Abun ya faru amma faruk baida laifi Aneesa ce da wannan matar ya nuna magajiya, faruk shago wuyan Aneesa yayi tare da fad'in kin cuceni kinyi amfani da tsoran da nakeji kikasa na musguna ma y'an uwana, dakyar aka kwace Aneesa daka shakar da yayi mata police sukai gaba da Aneesa da magajiya, zarah ta tsayar da police din tare da fad'in shima faruk a kama shi domin shima Mai laifi ne, tunda ya rufa ma masu laifi asiri, haka aka tasa keyar faruk aka wuce dashi, su kuma suka koma Gida cikin farin ciki, a falo suka suka zauna suna fad'in Allah yaji qan Abba Allah sarki Abba yanzu sun kashe ka, ihun mama suka ji Tana fad'in wani Abba din cikin Tashin hankali faduwa tayi kasa sumamma, cikin Tashin hankali suka nufeta kiran Dr akayi Don ya dubata, Dr yace ta tsorata ne hala in anyi Sa'a inta tashi zata iya tuna komai, sallama yayi musu Bayan yace a bishi a amso mata magani, suna nan zaune har mama ta farka tare da salati, binsu tayi da ido sai kuma tasa kuka tare da fad'in rayuwa kenan Idan Ina kallonku sai inji inama Ibrahim na nan, dukansu hamdala sukai domin sun gane ta tuna komai ganin suna hamdala yasa tace maiya faru?  Ina faruk naga ban ganshi ba a nan, zarah tace mama faruk.......  Labarin abunda ya faru suka bata basu boye mata komai ba, mama cikin kuka take tasa musu albarka tare da fad'in yanzu duk saboda ni kuka shiga wannan halin kuka zama bayi, Allah ya muku albarka suka amsa da Ameen.




Yanzu rayuwar gidan Alh Ibrahim ya canza komai ya dawo kaman da, yanzu suna jin dadinsu, gaba daya suna zaune a falo rahma tace gobe zata koma Jigawa dan karasa abunda ta Fara, zarah tace rahma tare dukanmu zamu dan bazamu Bari ki tafi ke d'aya ba dole mu tayaki, rahma taji dad'i Sosai, Washe gari da safe suka shirya su biyar a motar Haya suka tafi Bayan iyayensu sunyi musu addu'an nasara da kuma fatan sauka lafiya, Sun sauka Jigawa wajan karfe hudu duk sun gaji, Haulat tayi farin cikin ganinsu Sosai, Bayan sunci abinci sun koshi, suna d'an fira Haulat tace rahma Anya zamuyi nasara kuwa gashi saura kwana shida, rahma tace karki damu Haulat Kafin muzo nan saida muka shiga kauyen kusa kusa muka wayar musu dakai akan ilimi kuma sunyi alkawarin ranan Monday zasu turo yaransu Kinga ranan shine lokacin daya bamu, Haulat cikin jin dad'i tace Kai Alhmdlh Allah ya tabbatar mana da alkhairi,  suka amsa da Ameen.




Alh Mahmud yana office wasu mutane biyu suna ta mishi bayani akan irin ginin da zasu tsara Idan sukai nasara, shi gaba d'aya hankalinshi baya wajan tunani yakeyi ba tunanin komai yake ba saina Rahma ranan da suka fara haduwa harta fasa Mai glass din mota da zuwan da tayi ta sameshi suna meeting ta gaya Mai maganganu, murmushi yayi tare da lumshe ido, jin karan ana kiran sunanshi sir sir yasa yayi firgit, tare da kallonsu suka ce sir mun gama, yace OK, suna fita saiga wani ya shigo office din, yace sir yarinyar ta dawo, yace what? Mutumin yace jiya ta dawo garin, alh Mahmud yace ok, tare da sakin wani murmushi.




Kaman dai yanda ya fad'a hakan ta kasance, yau dai dai wata d'ayan daya basu kuma ya kasance ranan Monday , rahma dasu zarah suna ta jira suga yara sunzo amma shuru gashi Lokaci nata kurewa gaba d'aya hankalin rahma dana Haulat ya tashi Sosai, suna cikin haka saiga wata yarinya tazo da gudu ta nufi rahma tana fad'in Anty ban San maita fad'a mata ba naga ran rama ya baci Sosai domin fuskanta kawai zaka kalla kasan Tana fushi , dai dai lokacin Alh Mahmud yazo inda suke kallon rahma yayi yace time off, lokaci ya Kare kin fad'i nayi nasara, karasawa tayi inda yake ta wanka Mai Mari ji kake tas, kowa dake wajan ya tsorata musamman security dinshi dake wajan, rahma tace kayi nasara kake cewa? Nasaran cuta tun Farko inda kasan haka za kayi Mai yasa kasa wannan Wasan ka bata mana lokaci, kana kiran kanka mutum Mai kirki Ashe karya ne, dama na fad'a kai d'an kasuwa ne, baka san Asara ba sai cin riba nasan duk yanda za kayi sai kayi dan kayi nasara, yace rahma mai kike fad'a haka? Tace abunda ka aikata aika fi kowa Sani, zarah tace haba rahma miye haka? Tace zarah bari kiji abunda yayi yara Sun shiga babbar mota za'a kawo su nan yaje ya dakatar da motar dan Kar suzo shi yayi nasara, yace ni Mai kike fad'i haka? Tace ya isa haka zamu bar maka nan wajan gobe kayi duk yanda Kaga dama Tana fad'in haka tayi ciki, suma y'an uwanta da Haulat sukai ciki, alh Mahmud kam tunani yaita yi akan Mai take fad'i haka, rahma cikin kuka ta rungume Haulat Tana fad'in kiyi hakuri Haulat ban San haka Abun zai kasance ba  Haulat tace ya isa rahma nayi hakuri babu komai a raina domin haka Allah ya tsara, had'a kaya suka farayi domin motar asuba za subi,  koda alh Mahmud ya koma office sawa yayi Ayi bincike domin ance matarshi ce taje kauyen ta tare yaran, bayan anyi bincike ya gano cikin ma'aikatanshi ne sukai hakan, fita yayi cikin fushi danya samu wanda yayi Abun sai yaga mutumin yana fad'ama wani saboda ni oga ya sami filin inda badan niba daya fad'i, alh Mahmud kiranshi yayi yace ya shiga mota Jigawa suka koma inda yagansu a waje su duka da alama Haulat Tana fita da manyan kayan dake cikin gidan ne, ganin alh Mahmud yasa duka suka tsaya suna kallonshi, kusa da rahma taje yace nazo na baki hakuri domin bani naci gasar ba Kece kika ci ,kiran mutumin yayi yace ya fito yace fad'a mata abunda kayi, mutumin ya fara bama rahma hakuri yace nine na tare yaran dan Kar suzo domin abunda kika saka yara sukamin rannan, amma dan Allah kiyi hakuri, alh Mahmud yace Toh Kinji abunda ya faru ki daina zargina yanzu filin ya zama naku yana fad'in haka ya wuce, Haulat kam wani ihun murna Ta saki, saboda murna suka ce gobe zasu had'a party, bayan sun shiga ciki su zarah sukace ta kira Mahmud ta gayyaceshi party din, rahma tace Wlh kunya nake ji, ni bani ma da number dinsa, zarah tace naga card dinsa daukowa tayi tace ga number dinsa nan daukan wayan rahma tayi ta kira number din tare da mi'ka mata wayar......  Toh muje zuwa shin alh Mahmud zai amsa gayyatar rahma kuwa?






    *vote*
*comment nd share*

*maryam obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATADonde viven las historias. Descúbrelo ahora