11

843 58 0
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 11




Alh Ibrahim yayi gyaran murya sannan yace naji maganarku karku manta ko ku su Waye, ku mata ne ba zaman office bane ya dace daku zaman Gida shi yafi dacewa daku dan haka kubar maza suyi aiki, faruk yace Abba Idan ka basu dama Suma babu abunda ba zasu iya ba, amma zarah inaso kuyi hakuri Nima da kaina kaninku duk wani abu zanyi karku damu, shuru sukai su duka,zainab ce ta tashi tabar wajan zarah da khairat suka bi bayanta, aysha na kokarin tashi Alh Ibrahim ya kira sunanta da Aysha amsawa tayi da na'am yace gobe kina da ba'ko zaizo da yamma, tace toh tare da barin wajan,  koda ta shiga d'aki taga yan uwan nata sai faman zurga zurga suke alaman miye mafita, zainab ta kalli aysha tace wannan shawaran batai aiki ba dama nace har abada Abba bazai taba bamu muhimmanci, inda yasan haka zai ajiye mu mai yasa ya barmu mukai karatu?  Daya barmu cikin jahilci ta yanda za muji dadin zama matan Gida masu bauta, zarah ta dafa zainab tace kiyi hakuri zamu nemi wata hanyar, zainab tace zarah bana tunanin komai za muyi zaisa Abba ya dauke mu akan Muma y'ay'a ne ba..... Shigowan yasmin d'akin yasa sukai shuru dan murmushi tayi tare da kallon zainab tace zainab zaki Raka ni hspt gobe, zainab tace OK Allah ya kaimu, ta amsa da Ameen tare da fita, khairat tace mai za tayi a hspt? Zainab tace taya zamu sani, canza maganan sukai inda aysha take fad'a musu Abba yace gobe tana da ba'ko, tsokananta sukai tayi tare da fadin an kusa zama matar aure tashi tayi tabar d'akin ta wuce nata, dariya suka bita dashi, sannan ko wacce itama tayi dakinta.



Washe gari da safe wajan karfe 9 komai ya kammala akan dinning na breakfast, gaba daya iyalan gidan sun hallara, domin cin abincin, kowa abinci yake ci ba tare dayin magana ba, wayan Alh Ibrahim aka kira ya dauka da hello, ban San mai aka fad'a mishi ba Ya tashi rai a bace ya kalli amina yace Ina saleh? Tace baya nan ko ka manta ne? Yace ki fada mishi inya dawo Karya sauka a gida na inko ya sauka zansa a rufeshi da Farko ma dai koda ban sa an kamashi ba police nemanshi suke, amina cikin damuwa da Tashin hankali tace mai yayi? Alh Ibrahim cikin fad'a yace sata yayi musu a office na kudi wani ma'aikacinmu ya ganshi, sannan yama wata yarinya fyade, kowa dake wajan salati ya rafka, ita kam Amina kuka takeyi tare da fadin shairi aka ma saleh, Alh Ibrahim baibi ko ta kanta ba Ya fita rai bace ganin haka faruk d'a Abubakar suka bishi, d'aki amina tayi tana shiga ta doka ma saleh kira bugu biyu ya dauka tare da fadin my kanwa ya akayi cikin fad'a take cewa Wai mai yasa kai ba Zaka taba canza hali ba, tur da halinka Wlh, yace ke miye ne Wai abunda mijinta ya fad'a ta gaya mai tare da fadin yace karka kara shigo mai Gida,  saleh cikin fushi yace sai me gidanshi din banza kashe wayan yayi cikin bacin rai, Amina shuru tayi tana tunani ya kamata su hadu da saleh gaskiya amma dole in bari ya d'an huce,




Zainab da yasmin sun fita zuwa asibiti driver ya kaisu, koda suka je yasmin ita d'aya ta shiga, tayi wajan 40mnt sannan ta fito tace suje, Bayan ta fito suka hadu da wani yana ta fadin Aneesa Aneesa,  yasmin ta kalli zainab tace lah nayi mantuwa Ina zuwa, ciki ta koma da sauri, labewa tayi ganin mutumin dake ta kiranta da Aneesa tayi a gabanta zare ido tayi, yace wow kin kara kyau yau nazo garin gashi na ganki muje inda na sauka mana, cikin tsiwa tace dakata muje Ina? Bari kaji in fad'a maka ni yanzu matar aure ce, waigawan da zatayi taga zainab a bayanta ido ta bude alaman tsoro mutumin na ganin haka Ya wuce, zainab tayi murmushi tare da fadin faruk ne yake ta kira yace ya kira wayanki ba'a dauka ba gashi yana kan layi, amsan wayan tayi da sauri magana ta farayi tana kallon zainab amma daka ganin yanda zainab keyi bata ji komai ba wannan yasa hankalin yasmin ya d'an kwanta, koda suka koma Gida d'akin binta yasmin tayi inda ta sameta tana gyaran kumba, yasmin tace binta yau naga Ak, binta tace a ina?  Tace a hspt yana ta kirana da Aneesa Labarin abunda Ya faru ta bata, binta tace zainab din kin tabbata bata jiba?  Yasmin tace eh gaskiya dakyar in taji Kai bata ma jiba, binta tace Kai amma wannan ko d'an iska ya kamata ki fad'a ma faruk, yasmin tace yana dawowa kuwa.



Koda zainab taje d'aki ta Sami zarah da khairat suna tama aysha kwalliya bata ce musu komai ba ta Sami waje ta zauna, zarah tace Yadai zainab kikai shuru lafiya kuwa?  Tace zarah Anya yasmin babu wani Abun da suke boyewa kuwa?  Zarah tace name fah?  Labarin abunda Ya faru ta basu, khairat tace kina nufin yasmin tana da wani suna, sannan kuma tana bin maza da? Zainab tace toh nidai abunda naji kenan, zarah tace Idan kika ga mutumin zaki gane shi? Zainab tace eh, zarah tace shikenan koma miye zamu gano bada dadewa ba yanzu abunda ya rage shine ba'kon aysha yazo muga ko zasu daidaita, suna cikin haka ummi ta shigo tace toh khairat maza jeki rakata falon baki ba'kon yazo, tsokananta suka farayi tashi tayi wanda tayi kwalliya cikin leshi dinkin riga da skirt kayan Ya amsheta ta yafa Gayle ba karamin kyau tayi ba,  aysha Fara ce Sosai gata tana da tsawo ga idonta Manya,  fita sukayi ita da khairat har falon baki aysha na dauke da turen juice da snack khairat kuma tana dauke da cooler a tray, tunda suka shigo idonshi nakan aysha, yana dan murmushi khairat tace siriki Barka da zuwa d'an murmushi yayi tare da fadin yauwa kanwata, khairat fita tayi dan ta basu waje tace Ina zuwa, tana fita yayi gyaran murya yace aysha d'agowa tayi suka had'a ido wani irin murmushi yake sakar mata gaba daya sun kasa dauke idon nasu akan na juna, aysha tana tunanin irin haduwanshi domin kallo daya zaka mishi ka gane cewa namiji ne iya namiji, su zarah kam da khairat suna window sun labe suna kallonsu sai dariya suke ta musu tare dajin dadi dan ko ba'a tambaya ba suna son juna dan irin kallon da suke ma juna, aysha ce ta Fara yin 'kasa da Kai, murmushi yayi tare da fadin sunana jamil sannan ni d'an kasuwa ne yau Ina wancan 'kasa gobe Ina wancan 'kasa ban cika zama ba, na taba ganinki a wani super market keda wata kaman mum dinki ce, aysha cikin ranta tace tasan Amina yake magana dan in zata super market suna yawan zuwa tare, Katse mata tunani yayi da fadin tunda na ganki Allah yasa min sonki, toh sai nabi yanda addini yace na turo magaba ta akan su nema min izini in kin amince mun fahimci juna sai Ayi aure, rufe fuska tayi alaman jin kunya, dariya yayi, tashi tayi ta zuba mai juice tare da kokarin bude cooler yace Kar kisa min komai Alhmdlh, tace toh ga juice din bashi tayi garin amsa hannunsa ya d'an hade wani irin shock taji, da sauri tayi baya, shiko murmushi yayi tare da fadin an amince dani,? Kai ta d'aga tare da rufe fuska Alhmdlh Ya furta tare da fadin Allah na gode ma, su zarah dake waje Suma murnan suke, shan juice din yayi sannan yace mata zai tafi Bayan ya amshi number dinta, fita sukayi tare inda Ya bata katuwar Leda dakyar ta amsa sukai sallama akan sai sunyi waya driver yaja suka bar gidan, su zainab na ganin fitanshi suka rugo da gudu suka rungumeta, khairat ledan ta amsa ta bude wani yar takarda ta dauko da sauri aysha ta kwace tayi ciki da gudu binta sukai Suma khairat kam ledan ta dauka ta bisu a baya, key aysha tasa ma d'akinta ta fad'a kan gado tana sauke ajiyar zuciya bude takardan tayi dake ta faman kamshi........  Toh masu karatu saiku biyoni dan jin maike cikin takardan...






     *vote*
*comments nd share*

*Maryam  Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now