14

674 46 1
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 14





Gaba d'aya kowa dake falon shuru yayi, su zarah da sauri sukabi mahaifinsu domin basu San wannan hukuncin zai yanke akan faruk ba, duk da yayi laifi babba amma basu taba kawo wa zai koreshi ba, alh Ibrahim yana zaune a d'aki ya zabga tagumi kallo daya zaka masa kasan yana cikin fushi Sosai su zarah ne suka karaso koda suka isa d'akin kasa magana sukai zai aysha ce tayi karfin halin fad'in Abba, bai d'ago ya kalleta ba amma yana jinta bata damu da hakan ba dan tasan dole yana jinta, tace kayi hakuri Abba Ina faruk zashi shifa d'anka ne, yanzu Idan yabar gidan nan yaje ya fad'a cikin wani hali Abba ba zaka ji dad'i ba dan......  Ya d'aga mata hannu alaman ya isa haka, zainab tace dan Allah Abba kayi hakuri cikin fad'a yace ku fita kuban waje bazan zauna da wannan fasikan matar tashi ba maz.......  Bai 'karasa ba suka ji muryan amina tana fadin ya saketa yanzu yace tabar gidan, da sauri ya kalli Amina d'aga mishi Kai tayi alaman eh ya saketa, shuru yayi can yace Ina faruk din?  Kafin ta bashi amsa saiga faruk din nan ya shigo cikin kuka tare da dur'kusawa a gaban Abba yana mai bashi hakuri tare da ro'kanshi akan ya yafe mishi bazai kara ba ya tuba, ganin irin kukan da faruk yake ga magiyan dasu zarah kemai yasa yaji zuciyarshi ta sauko amma da yayi mugun fushi da d'an nasa Wanda yake matukar so, d'ago shi yayi tare da fadin na yafe maka amma duk ranan da naji koda wasa wani abu ya had'aka da wannan yarinyar sai nayi mugun Saba maka, jin abban nasu Ya sauko yasa su zainab suka nufi d'akin Aneesa da binta inda suka samesu suna had'a kaya, zainab tace inaso in baki shawara daka yanzu sai ki koyi hankali duk abunda kayi shi badon Allah ba Toh ba zaka taba ganin albarkan Abun ba, kin auri faruk Nasan saboda kudin Abba dan Nasan ba wani sonshi kike ba, amma Allah ba azzalumin kowa bane sai gashi ya tona miki asiri cikin 'kankanin lokaci,  dan haka maza a tattara zarah ta kalli magajiya dake had'a kaya tace toh magajiya sai a koma gidan jiya suna fadin haka suka fita suna dariya, aneesa Bayan fitan su ta kalli binta tace sunyi kuskure saki d'aya faruk yayi min amma kota wani hali sai ya dawo dani sannan Idan na dawo saina tarwatsa wannan family din sai Nayi abunda zanyi dan in mallaki komai na gidan nan inko ban aikata hakan bah Toh ba sunana Aneesa ba, magajiya tace toh ni yanzu Ina zamu dosa? Aneesa tace magajiya dan Allah kibar Yimin wannan tambayar kawai ki dauki akwati mu tafi duk inda zamu in mun fita zamu tattauna.




Bayan kowa Ya nufi d'akinshi faruk ya silale yabar gidan inda ya tafi neman Ina Aneesa suka nufa tafiya yake a hanya can ya hangosu a gefen titi daka gani sun rasa mafita ne suka tsaya a wajan, magajiya tace Kai nifa Wlh na gaji tun dazu sai yawo muke, Aneesa shuru tayi kanta na faman juya mata, faruk ne ya faka matarshi daidai inda suke, Aneesa na ganinsa ta saki kuka, cikin damuwa ya fito yana bata hakuri, tace dan Allah ka kyaleni inje in mutu ka rabu dani, hakuri yaita bata yace su shiga yaje ya kaisu inda zasu kwanta Kafin gobe saiya kama musu Gida tunda wancan gidan an siyar, Aneesa tace babu inda zan bika, magajiya ta zungureta, amma Aneesa tace babu inda zata dakyar ta yarda suka shiga motar, hotel yaje ya kama musu tare da basu kudi ko zasu bukaci abu, sallama ya musu akan gobe zai dawo, Bayan fitanshi magajiya tace Kai Aneesa da kinso ki mana tsiya zaki sa mu kwana a titi, Aneesa tace ai tunda yazo bazai Bari mu kwana a titi ba wannan abun da kika ga Nayi duk cikin plan dina ne, dariya magajiya tayi tare da fadin mai kike shirin kullawa yanzu? Aneesa tace karki damu magajiya koma miye zaki gani kawai kisa min ido, saina nuna musu babu wanda ya isa ya d'aga min yatsa dariya magajiya ta saki tare da fadawa kan lafiyayyan gadon d'akin tace wow ji gado kaman Ina cikin gidan da aka koromu, tsaki ta saki ni Wlh Ina takaicin barin mu gidan nan, Aneesa tace zamu koma bada dadewa ba, wayan dake manne a jikin d'akin Aneesa ta kira tace a kawo musu abinci Bayan ta fadi abunda take so, saida yayi wajan 40mnt sannan aka kawo, ana ajiyewa magajiya ta Fara ci, ita kam Aneesa warin abincin taji Ya bugan mata hanci da gudu tayi toilet ta Fara kwarara amai, Bayan ta fito magajiya tace aneesa amai?  Kodai ciki gareki? Aneesa tace abincin ne ya sani Tashin zuciya magajiya ta saki wata Uwar guda tace Wlh ciki ma gareki gobe da safe dole muje asibiti a gwadaki, Aneesa tace inko ciki ne shine zai ban dama aikata Abun da nayi niya cikin sauki shafa cikin tayi tana murmushi tare da sa'ka abubuwa da dama cikin ranta.....







    *vote*
*comments nd share*

*maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now