17

625 41 0
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 18





Iyalan Alh Ibrahim ne zaune akan kujerun falo suna fira, yar karamar wayar Amina ta kad'a alaman kira ya shigo, tashi tayi tabar wajan saida taje d'akinta sannan ta dauka tare da fadin wai miye ne kake ta kirana? Yace na fad'a miki kudi nake so ya kamata kizo Ki aiko min dashi, d'an tsaki tayi tare da fadin saleh gaskiya kana son takura min nace maka ka Bari Idan na sami daman fita sai inzo in kawo ma, yace zuwa yaushe? Tace Idan na fito zan fad'a maka, kashe wayan tayi tare da zama akan gadon d'akin.



Su zainab sunsha soyayya Sosai,ta yarda da irin son da mijinta ke mata, yanzu haka suna cikin jirgi suna hanyar dawowa hannunta na manne da nashi, koda suka dawo Nigeria driver gidansu yazeed ne ya daukesu zuwa gidan mum dinshi, inda suka sami tarba mai kyau, duk wata kulawa mum din yazeed na bata tare da nuna mata kauna itama sai yasa zainab din ta saki jiki da ita, satinsu biyu suka koma gidansu lokacin zainab an kara kyau ga wani haske data kara kowa na gidan yaji dadin yanda yaga ta koma, su aysha Suma sun tafi katsina gidan iyayen mijinta.



Yau kowa na falo Alh Ibrahim yayi gyaran murya tare da fadin nayi ma faruk mata bikin ranan juma'a mai zuwa, Amina tace kaman ya? Yace eh kaman yanda kike tunani na zaba mishi yar gidan mutunci dan bazan kara yarda da zabinshi ba, faruk kam tunda aka fara maganan wutar dake kanshi ta dauke dan bai taba zaton haka ba, amma babu yanda ya iya dan yasan wannan auren tunda Abba ya fad'a dole sai anyi, ummi tace toh ya kamata ai mata su shiga Abun a had'a akwati Abba yace na basu komai sun had'a mata kawai daurin aure ake jira, faruk tunani yake yanzu Idan Aneesa ta Sani Ya zasu kaya? Tashin hankali dole inyi nesa da Aneesa na wani lokaci haka yaita tunani Kala Kala Ya sa'ka wannan Ya kwance, kaman dai yanda Alh Ibrahim ya fad'a hakan ko ta faru domin a kwanakin da yace aka daura auren inda aka kawo amarya gidan mai suna Farida, Farida kyakyawa ce ajin Farko gata fara doguwa ga manyan ido, koda faruk ya shiga d'akin ya ganta yayi mamaki da irin kyanta mai daukan hankali, lokaci d'aya yaji zuciyarshi ta Fara bugawa da karfi sonta yana shiga cikin ranshi, a ranan dai faruk kasa hakuri yayi saida suka raya daren, yaji dadin yanda Ya samu Farida a budurwa sai yaji Ya kara Sonta Sosai, soyayya yake nuna mata Sosai da kulawa tunda yayi aure baije wajan Aneesa ba, gashi inta kira baya dauka.



Magajiya ce ita da Aneesa suna zaune magajiya na wanki Aneesa na kusa da ita, magajiya tace wai maike damun faruk daya daina zuwa baya kuma daukan waya, Anya lafiya kuwa? Ya kamata muje mu duba fah, aneesa tace hakane ni a wannan karan gidan zan koma ma gaba d'aya dan na gaji da zama a nan gskiya magajiya tace yauwa ko kefa, inda za kiji shawarata dama Kin tashi kinzo mun tafi yanzu, aneesa bata musa ba tace magajiya ta had'a musu kaya, jiki ba bari magajiya ta Fara had'a kaya, Bayan ta gama suka nufi gidan Alh Ibrahim, da yake yau lahadi yana Gida dan babu office, nocking suka ji zainab taje ta bude baki ta saki lokaci d'aya kuma tace maiya kawo ku? Kowa dake falon ya kalli kofar ganin aneesa da magajiya yasa kowa ya tashi yayi hanyar kofar, ciki harda faruk, alh Ibrahim yace mai ya kawo ki gidana maza fita, tace Abba na dawo nan da zama ne domin Ina dauke da cikin faruk, kowa dake wajan mamaki yake ita kam Amina wani dad'i taji zata samu jika, alh Ibrahim yace dan kina da cikin faruk bazan baki daman zaman min a gida ba, dan haka ku fita, Amina tace haba haba ina zata jikanmu nefa a cikinta ta kalli mama tace mama dan Allah kiyi mishi magana, mama tace Ibrahim ka Barta ta zauna, shuru yayi can yace naji mama zan barta tunda yanzu faruk yana da mata dam kirjin aneesa ya buga, wato aure yayi.......  Katse mata tunani yayi da fadin mama Idan ta haiyu zata bar min Gida yana fadin haka ya haura sama kowa ma dake wajan yabar falon faruk yazo zai wuce tasha gabanshi tare da fadin abunda naji gaskiya ne aure kayi? Kai ya d'aga mata alaman eh, wani abu taji ya tokare mata wuya gashi faruk din yabar wajan, d'aki suka nufa ita da Magajiya aneesa tana ta sintiri tare da fadin magan ganu, ni faruk zai ma haka ina Raye zai kara aure, saina Nuna mishi ni karuwa ce, sai yayi nadama har yana cemin eh aure yayi magajiya zuciyata zata buga Wlh Ina son faruk Sosai amma saina hukunta sa akan abunda yayi min shima yaji aneesa bata yafiya duk 'kan'kanta abu Idan akayi min sai na Rama faruk yayi min laifi mai girma bazan taba bari in had'a dan da zan haifa da wasu yaran ba dan bazan bari Ayi yan ubanci ba........







     *vote*
*comments nd share*

*maryam obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang