34

479 34 2
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*



*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 34





Zainab ce ta shigo ta samesu cikin tashin hankali ganin irin halinda suka shiga yasa ta Fara tambaya Ummi lafiya maiya faru kuma? Ummi ce ta fad'ama zainab abunda ya faru, cikin zafin nama ta fita falon ta sami Aneesa ita da magajiya zaune ga kud'in tasa akan cinyanta Tana girgiza kafa, zainab tace Aneesa ki bani kud'in da kika amsa a hannun zarah, aneesa bata ko kalleta ba balle tasan da ita take magana Abun ya batama Zainab rai ta nufeta da nufin d'aukan kud'in dai dai lokacin su Ummi suka karaso wajan Aneesa dauke kud'in tayi tare da dauke Zainab da wani gigitaccen Mari Wanda yasa saida taga stars ga ciki, khairat da sauri ta karasa ta riko Zainab dake kokarin fad'i, Aneesa tace naga kuna kokarin wuce gonarku amma Bari in tuna sharku, mama mama Aneesa ta Fara kiran mama cikin tashin hankali suke kallonta Zainab da take jikin khairat tace Aneesa dan Allah karki fad'ama mama abunda ke faruwa dan Allah kiyi hakuri, amma Aneesa ko kallonta batayi ba sai faman kwadama mama kira take, mama ce ta fito gaba d'aya cikin tashin hankali suka nufeta, mama ta kalli ummi tace Ibrahim har yanzu bai dawo ba? Ummi tace eh bai dawo ba mama muje in kaiki d'aki ki huta, mai makon mama taje d'aki kaman yanda Ummi tace saita kara jefo mata wata tambayar da fad'in baiyi waya ba?  Ummi komai kuna boyemin wani abu ne? Yau kwana nawa har yanzu bai dawo ba, ya kuma san banda lafiya, Ummi tace Mama doctor yace ki daina sama kanki damuwa yace kina bukatar hutu muje ki kwanta ki huta, ummi ta kamata sukai ciki, Bayan sun shiga Aneesa ta kallesu tare da fad'in wannan ya zama na farko dana karshe da zan kara fad'a wani ya fad'a ko kuma inyi Abu wani yayi gigin tambaya na, Tana gama fad'in haka ta haura Sama ita da magajiya,  zarah kasa tayi tana kuka yayinda y'an uwanta suke ta rarrashinta akan tayi hakuri komai zai wuce, tace taya zai wuce? Zainab mijina yana station na kasa fito dashi babu hanyar da zan sami kud'i taya komai zai wuce, ummi ce ta karaso inda suke tace zarah kiyi imani da Allah komai zai wuce Allah baya daura ma bawa abunda yafi karfinsa kiyi hakuri.


Lokacin da rahma tabar gida rasa wajan zuwa tayi, gashi dare yayi cikin damuwa take tafiya gashi ta gaji, wani kango ta gani wanda an fara gini ba'a gama ba shiga tayi ta ajiye akwatin ta, tare da budewa ta d'auko wani zani ta shimfid'a tayi pillow da akwatin ta, jin kaman mutane a kanta yasa ta d'aga kanta wasu maza ta gani su hudu ko wanne da sigari a hannunsa, d'aya daka cikinsu yace Yadai y'an mata tare da d'aga mata gira, wani ya cabe da fad'in yarinya mai zafi irinki bai kamata ki kwanta a titi ba kizo mu baki masauki saimu kwana tare, d'aukan akwatinta tayi tare da zaninta da nufin tafiya janyota sukai suna shafa mata fuska wani kuma ya ri'ke mata hannu tare da fad'in ina zaki kuma y'an mata?fisge hannunta tayi da karfi tare da fita daka wajan amma ganin suna kokarin binta yasa ta jefar da akwatin ta Fara gudu tazo wajan titi suka kamata da yake dare ne babu kowa suna kokarin cire mata kaya sukaji jiniyan y'an sanda da gudu suka bar wajan, Allah tayi ma godiya tare da komawa ta d'auki akwatin ta tabar wajan, kusa da wani Gida taje akwai masallaci a wajan ta ra'be a barandar gidan ta kwanta, Washe gari tunda asuba tabar wajan dan zuwa neman aiki domin ta samu ta tsira da kanta, tafiya take tana hawaye domin tunawa da tayi batai karatu ba, bazata samu irin aikin da take buri ba danta taimaki y'an uwanta, haka taita yawo wajan masu saida abinci amma bata sami aiki ba dan wasu cewa ma sukai suna tsoran irinsu, wasu kuma sun ganta jikinta fresh ga kyau sai suce bazasu iya biyanta ba, haka dai ta gaji da yawo ga yamma tayi ga akwati Tana ta fama dashi ga yunwa, wani wajan gida ta nufa ta zauna, wani tsoho ne ya fito yaje masallaci harya dawo ya ganta a wajan yace yarinya lafiya kuwa? Bata kikayi ne? Cikin kuka tace eh dan Allah baba ka taimaka min, mutumin yayi shuru can yace tashi muje, cikin gidan tsohon suka shiga babu laifi yana da kyau da d'an girma, kiran matarshi yayi Mai suna Hajara yace ga Bakuwa nan a bata abinci da masauki Hajara ta amsa da Toh, rahma tace dan Allah Bari in farayin sallah tukunna bayi Hajara ta nuna mata ta shiga Bayan ta fito ta kaita d'aki ta Fara sallah, Hajara fita tayi Bayan ta kaita d'akin wajan mijinta taje inda ta sameshi tace wannan bakuwar daka ina kuma? Yace Wlh ganinta Nayi a waje a zaune ban San daka inda tazo ba koma dai daka ina take bari ta huta sai muji dan Ina zargin ta bace ne ko bata gane inda zata ba Hajara tace Allah ya kyauta ya amsa da Ameen.



Su Ummi suna kitchen suna aikin abincin dare, zarah ta kalli aysha tace aysha Wai yaushe zaki koma gidanki ne? Ummi tace Nima abunda ke raina kenan, aysha kuka tasa dukanku sukai kanta cikin tashin hankali, zarah tace aysha maiya faru lafiya kuwa? Cikin kuka tace ummi na sami matsala da Sirika ta wata y'ar uwarta tazo taita zugata suka sakani a gaba gab da Abba zai rasu suka koroni tare dayima d'anta kashedi Idan ya nemeni bata yafe Mai ba, ummi shuru tayi tare da jimami su zarah ne sukai ta rarrashinta, ummi Kam ta fad'a duniyar tunani lallai dama Idan kana da y'ay'a mata ka dinga ganin irin abubuwan nan kenan Allah yasa hakan shine alkhairi, haka sukai ta aikinsu har suka gama suka jera a dinning sukai sama inda suke kwanciya dan su huta, ummi tunani tai tayi Kala Kala akan abubuwan dake faruwa, na farko ga matsalan zarah na biyu ga zainab haiyuwa yau ko gobe, na uku ga aysha ta sami matsala da mijinta ga rahma tabar gida, wani hawaye Ummi ta matse Mai zafi lallai Allah baya barin wani dan wani yau inda mijinta yana Raye da abubuwa basu cabe haka ba, gashi y'ay'anta suna cikin matsala amma ta kasa magance musu, ta gefen zarah itama tunani ne fal cikinta taya zata fitar da mijinta daka prison, duk tayi ba'ki ta rame, jin Aneesa sukai tana fad'in kuna ina? Tashi sukai suka sauka katsa dan bata abinci.







       *vote*
*comment nd share*

*maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATADove le storie prendono vita. Scoprilo ora