19

502 44 0
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 20





Tana karasawa taga ko motsi baya yi ga jini yana zuba a jikinshi tako Ina ihu ta saki tare da kuka, driver din da suka zo tare yazo Ya fara kokarin daukanshi Dan suje asibiti amma Ya kasa, ya kalli mutanan dake wajan yace dan Allah ku taimaka mu sashi a mota kowa dake wajan yaki tare da fadin babu ruwan mu wannan case din police ne jin haka yasa zainab da tayi zaman durshan a kasa take ta kuka yasa ta tashi suka kamashi ita da driver suka wuce dashi asibiti suna zuwa akai emergency dashi inda aka fara dubashi ganin bai mutu ba yasa aka sa mishi oxygen domin numfashin shi ya dai daita, driver ne ya kira gidan amma basu dauka ba dan suna can suna ta hidiman birthday, lokacin da za'a yanka cake duk yan uwanshi mata suka tsaya kusa dashi Alh Ibrahim yace Ina zainab, sai a sannan kowa Ya fara dube dube, khairat tace, ta fita tace mun zata ta dawo, alh Ibrahim yace zuwa ina?  Khairat tace Wlh nima ban sani ba, daukan wayanshi yayi da nufin kiranta yaga miss call din driver, yazo zai kira zainab din kiran driver din ya kara shigowa, dauka yayi tare da fadin hello, driver yace ranka ya dade gamu a asibiti da zainab mijinta babban mota ta bigeshi rai a hannun Allah Alh Ibrahim sakin wayarshi yayi tare dayin salati, mama tace lafiya kuwa? Yace zainab na asibiti yazeed yayi hatsari babban mota ta bigeshi, kowa salati ya fara ita kam Amina tsoro ne ya kamata Kar dai ace saleh ne ya aikata hakan, fita sukai su duka suka nufi asibitin inda suka ganta zaune a katsa kusa da d'akin da yake ,dukansu sun tausaya mata, ummi ta nufeta tare da tabata rungume ummi tayi tana kuka tare da fadin ummi shikenan yazeed, ummi bana son ya mutu ummi ku fad'a mishi ya tashi da wuri, alh Ibrahim dake tsaye cikin tausayin y'ar tashi ya matso kusa da ita yana share mata hawaye tare da rungumota jikinshi wannan ne Karo na farko da mahaifinta ya taba yi mata irin haka, yace kiyi hakuri zainab zai tashi insha Allah Kinji, nan Alh Ibrahim yaita bata baki tare da rarrashinta suna nan zaune har dare domin suna son ganin farkawanshi, wasu daka ciki har sun Fara d'an gyangyadi, saleh dake asibitin tun dazu a boye Ya samu ya shige d'akin dai dai lokacin yazeed din ya fara kokarin d'aga hannu saleh ya girgiza kai yace Allah sarki yazeed banyi biyan kashe ka ba, bude ido yazeed yayi yana kallon sale, yaci gaba da fadin amma babu yanda na iya dole ka mutu tunda kaji komai eyya kayi hakuri yazeed harda matso kwalla lokaci daya kuma ya share tare da cirema yazeed oxygen din, nan ya fara zuba tare da zare ido ko minti uku baiyi ba da cirewa ba yazeed ya rasu😭 yana ganin haka yayi saurin mayar mishi yabar d'akin, yana fita Abun ya fara kara farkawa sukai tare da shiga d'akin da gudu Dr shima yazo amma ina rai yayi halinsa Amina najin haka ta fita Tana kuka tana fita suka had'u da saleh da hannu ta nunashi alaman kai ne? Yace Nina kashe shi kuma duk saboda asirinki yaci gaba da rufuwa dan haka Kinga tafiya ta, Amina zama tayi a wajan Tana kuka mai cin rai tare dayin dana sanin da saleh ya zamo d'an uwanta, ita kam zainab tunda Dr ya fad'a Ya rasu gaba d'aya ta kasa kuka sai kallonsu take da ido tana musu kallon kaman basu da lafiya, Maman yazeed taci kuka d'anta kwaya d'aya yabar duniya, haka aka dauki gawarshi zuwa gidan Alh Ibrahim ruwan da akeyi gashi yamma tayi yasa dole sai gobe aka bari a birneshi gidan Alh Ibrahim aka Kai gawar nashi, Kafin gari ya Waye har Labarin mutuwar yazeed ya baza ko Ina, zainab kam tun jiya ta kasa kuka hankalin Alh Ibrahim ya tashi Sosai domin yasan rashin kukan nata hatsari ne, yan uwanta mata babu abunda suke sai kuka tare da tausayin y'ar Uwar tasu, lokacin da akayi ma yazeed sutura mahaifiyarshi ta mishi addu'a tanayi tana kuka ita kam zainab koda tazo kallon gawan tayi da mutanan wajan tace miye haka zaman miye kukeyi mai yasa kuke kuka maiya sami yazeed bashi da lafiya ne, kowa dake wajan mamaki yake tare da tausaya mata ummi ce ta ru'ko mata hannu tare da fadin zainab yazeed ya mutu, kwace hannunta tayi tare da fadin a'a ummi ba mutuwa yayi ba, mutuwa in anyi ba'a dawowa yazeed bazai mutu yabar niba ban yarda ba, ummi tace zainab yazeed ya mutu bazai taba dawowa ba ya tafi kenan har abada wani irin ihu ta saki Wanda ya razana mutanan wajan tare da fadin shikenan yazeed lokaci d'aya ta Fara kuka ganin haka aka dauki gawar aka wuce dashi zainab kuka take mai shiga rai tare da fadin shikenan Ya tafi ya tafi kace bazaka taba bari naba mai yasa ka tafi ka barni, duk Wanda yake wajan saida yaji tausayinta Sosai.......










    *vote*
*comments nd share*

*Maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang