25

603 41 0
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*


*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 26



Alh Ibrahim wani kallo yamai Mai kama da inda inada hali dana kashe ka, saleh duk da irin kallon da alh Ibrahim yamai bai hana yaci gaba da fad'in abunda yake son fad'i ba, yace saboda ni gashi yanzu rahma zata koma Gida, kuma nayi nadaman abunda na aikat.... Alh Ibrahim ya dakatar dashi da fadin ya isa haka ya isa nace,  Bari kaji in fad'a maka daka yau karka bari in sake ganinka ko kuma Layin gidana ko wajan iyalina inko ka Bari hakan ta faru saina sa an daureka, mara mutunci ko yanzu da Kaga an fito dakai zainab ce taso hakan amma ka guji sanda zaka kara aikata min wani laifi mara mutunci yana fad'in haka Ya shige mota su mama dama sun dad'e da shiga, driver ya tada suka wuce gida,  koda suka isa Gida a falo suka Tarar dasu zainab kallo daya aysha tama rahma tace sis domin kamanta d'aya dana mamanta, zainab tashi tayi ta nufeta tare dayin hugging dinta tace Barka da dawowa sis, dariya rahma tayi cikin jin dad'i tace nagode, rahma sai kallon gidan take lallai mahaifinta Mai kudi ne jiba wannan katotan gidan Wanda sai a India ko saudiya ake wannan manya manyan gidajan amma yau gashi gidan mahaifinta babba, zama sukai Anata fira inda itama rahma aka ware mata nata d'akin.


Yau Aneesa ta tashi dana kud'a, wanda tun asuba take ta faman nishi, magajiya ganin Abun yaki cinyewa yasa ta nufi d'akin faruk taita bugawa  farida ce ta tashi ta bude, magajiya tace kira faruk yazo yakai Aneesa asibiti zata haiyu, da sauri farida ta koma ta taso faruk wanda ya fito cikin sauri tare suka nufi d'akin Aneesa din daukanta faruk yayi sukai kasa ummi jin hayaniya yasa ta fito taga abunda ke faruwa da sauri ta koma tasa hijab ta fito suka tafi asibitin tare suna zuwa akai labour room da ita, bata wani dad'e ba ta tsintilo d'anta namiji santalele kyakyawa dashi, koda Dr ya fito ya musu albishir faruk sai murna yake yana jin dadi, da aka bada izinin shiga shine na farkon shiga ya dauki baby din yana juya shi yana fad'in dani yake kama, farida ta matsa kusa dashi tana kallon baby din gwanin sha'awa sai taji dama d'anta ne, magajiya ce ta amshi baby din dan taga yana kokarin bama farida, ganin haka yasa farida ta koma baya ummi ta amshi yaron wajan magajiya Tana fad'in Kai tubarkallah yaron kyakyawa, ummi ta kalli faruk tace ya kamata ka kira gida ka fad'a musu, yace Kai Wlh nabar wayana a gida, Shigowan Dr ne yasa ummi ta nemi ya bata Aron waya dan ta kira, number din mijinta ta kira ya dauka yana jin muryanta yace Ina kika shiga tun dazu muna nan hankali tashe, tace kwantar da hankalinka muna asibiti Aneesa ta haiyu  cikin fara'a yace Alhmdlh Mai aka samu? Tace d'a namiji yace Kai Barka Bari in fad'a masu Amina, yana kashe wayan ya fara Sanar dasu, murna suka fara su duka daka nan kuma aka had'a abinci aka nufi asibitin dashi, sai daukan yaron suke tayi suna fad'in yaron kyakyawa, Aneesa dake kwance tana kallonsu tace duk ku gama ni Nasan maina shirya muku da yamma aka sallameta sukai gida.


Aneesa tunda suka koma Amina take bata wani kulawa na musamman, yaron kowa na sonshi, farida ganin haka yasa itama ta shiga damuwa taji tana son ta haiyu gashi ko bari bata taba yiba, faruk tunda akai haiyuwar bini bini yana d'akin Aneesa, bashi ma da lokacin farida Sosai haka dai akai suna wanda alh Ibrahim ya kashe naira domin yayi hakan ne dan Kar faruk din yaga an canza Mai danshi alh Ibrahim har gobe a matsayin d'a ya dauki faruk alh Ibrahim yayi ma yaro huduba da Muhammad sai suke cemai  Anan.

Tunda Aneesa ta haifi d'anta take sa faruk yake mata abubuwa masu yawa tun yanayi mata dai dai karfinshi harya Fara gajiya, alh Ibrahim harya Lura da kwana biyun nan yanda faruk yake kashe kudi masu yawa dan haka yasa aka canza mishi pin dinshi, koda faruk yaje ciran kudi yaga yasa pin kuma dai dai aka cemai incorrect pin ya kara sawa ATM din ya makale ya dai gane abba yasa an canza pin, ga Aneesa taita damunshi ya mata Abu gashi bashi da kud'i,  da dai ya gaji ya fito ya fad'a mata abunda ke faruwa tace inda dane Kafin ya gane kaiba dansa bane ai bai taba Canzawa ba sai yanzu dan kawai Kai ba dansa bane Wlh kasan abunda zaka tatsa tun Kafin dare yayi maka Inba haka ba zaka tashi tutar babu domin yau yana mutuwa baka da gado alh Ibrahim da yazo wucewa yaji tana maganar d'akin ya shigo yace ta tattara nan da minti biyar tabar Mai gida inko ba haka ba saina lahira ya fita jin dad'i mutuniyar banza kawai kina son ki canza ma d'ana tunani faruk har gobe dai dai yake da Yaran dana haifa yana fadin haka ya fita, magajiya kam ba'kin ciki ne fal cikinta tunda taji ance subar gidan faruk shima fita yayi Aneesa ta Fara had'a kaya dan barin gidan........







     *vote*
*comments nd share*

*Maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now