40

610 44 0
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 40









Aneesa na d'aki saiga kira an kirata, d'auka tayi tasa a kunnenta, ban San mai aka fad'a mata ba naga ta tashi zumbur tayi waje d'akin magajiya ta shiga, Tana shiga ta rufe kofar da karfi tare da fad'in magajiya ina kud'in da nake baki duk wata ki tura yau ya kirani yace wata uku kenan baki tura mishi ba, magajiya tace heeey ya isa haka ki daina min ihu Inba so kike wani yaji abunda ke faruwa ba,inko wani yaji kin shiga uku domin sai an kamaki rayuwar prison za kiyi ko kuma a kashe ki fit, Aneesa tace magajiya ni kike fad'a ma haka? Toh Bari kiji Indai aka kamani dole Kema a kamaki domin komai tare mukeyi dan haka maza ki fito min da kud'in da nake baki tana fad'in haka tabar d'akin, zarah dake labe duk taji abunda suka fad'a, Aneesa d'akinta ta koma tana shiga taga wayarta na kara, d'auka tayi mutumin yace ki fito waje ina wajan gidanku, aneesa tace maiya Kawo K.....  Bata gama magana ba ya kashe wayan, fita tayi tana dubawa ko akwai wanda yake ganinta, aiko tana fita taga mutumin hannu ya mi'ka ma Aneesa alaman ta bashi kud'i, duk wannan abunda suke zarah na sama na kallonsu, kallo d'aya zakama Aneesa ka gane a tsorace take, Aneesa tace ka tafi zan aiko maka dashi yanzu banda cash, yace Ina babu inda zani sai kin ban kud'i kona tona miki asiri, Aneesa ganin in bata sallameshi ba zai iya aikata komai yasa ta cire awarwaran hannunta ta bashi tare da fad'in gashi zinari ne saika saida, yana amsa yabar wajan aneesa ta dawo ciki, zarah data labe ta fita tabi bayan mutumin tana cikin tafiya taga mijinta Abubakar dake fushi da ita akan abunda takeyi ma Aneesa, yace zarah lafiya na ganki a haka? Tace Abubakar zo muje dan Allah zan maka bayani daka baya nuna Mai mutumin tayi tace dan Allah mu kamashi akwai abunda nake son sani muje binshi suka farayi ganin kaman shi suke bi yasa ya fara gudu, Abubakar shima gudun ya fara har Allah ya bashi Sa'a ya kamashi, mutumin cikin tsoro ya fara fad'in dan Allah ka sakeni in tafi, zarah tace Mai kuke boyewa kaida Aneesa fad'a min inji? Ko in kira police mutumin yace zan fad'a ba komai nake boyewa ba sai kisan alh Ibrahim mahaifinku da Aneesa sukayi, zarah da Abubakar cikin firgici sukace me? Mutumin samu yayi ya ture Abubakar ya gudu, zarah tsayawa tayi kaman an dasa gunki,ashe dama dagaske kashe mahaifinsu akayi, wani irin kuka takeyi Mai ban tausayi, Abubakar yaita rarrashinta akan tayi hakuri, yace Toh yanzu sai ki daina biye mata ai, tace Abubakar inada dalili Labarin abunda take shiryawa ta bashi, koda suka koma Gida tama ummi bayani ummi tace yanzu abunda za tayi shine ta samu dukiyar su ta dawo hannunsu Kafin a hukunta Aneesa,zarah tace hakane, Aneesa must pay for what she did.




Aneesa ce zaune cikin d'aki ita d'aya saiga zarah ta shigo ta zauna kusa da Aneesa tace lafiya kuwa Aneesa? Aneesa tace zarah faruk dazu yamin magana akan yana son yaba farida wani abu a cikin kud'in nan, zarah tace Ahap abunda nake fad'a miki kenan tun kwanaki akan ki bashi ya dawo da kud'in na d'anki ko naki signing kawai zai miki shikenan komai ya zama naki, aneesa tace hakane zarah sai yanzu nake ganin lokaci yayi daya kamata inyi haka, toh yanzu taya zan had'a komai? Ina nufin takardan yarjejeni, Amina ce ta shigo d'akin Tana fad'in gashi nan na had'a miki komai kawai kisa faruk yayi signing komai zai zama na d'anki, Aneesa cikin jin dad'i ta amsa tare da fad'in nagode nagode Bari in Kai mai yanzu kuwa, fita tayi ta nufi d'akin faruk, samunshi tayi a wajan window yana tsaye, sunanshi ta kira da faruk, waigowa yayi tace faruk gashi yace Mai nene tare da amsa, tace signing nake so kamin yanzu akai, yace takardan menene wannan? Tace so nake duka dukiyar nan ya dawo Sunan baby na ya tashi daka kan ka, yace what? Tace ina jira kamin yanzu kaban, yace mai yasa Aneesa, tace kasan Dai ina tare da sirrinka koh dan haka maza kayi min signing Kafin raina ya baci kowa yaji, d'aukan biro yayi badan ranshi yaso ba yayi mata signing ya bata cikin murna ta fita Tana shiga d'akinta ta fad'a gado tana dariya, zarah da Amina suka shigo suna fad'in Aneesa, aneesa tashi tayi ta mi'ka musu tana murna tare da fad'in da badan kuba da duka dukiyar nan yana wajan faruk daka karshe harda farida da abunda zata haifa za'aci yau gashi komai ya dawo wajena, Amina sauri tayi ta boye file din da Aneesa ta basu ta canza wani, aneesa tana ta murna, Zainab da tazo wucewa taji komai cikin rashin hankali Ta nufi ummi tana fad'a mata abunda sukayi, khairat tace zarah mai take nufi, lallai zarah daka yau mun cireta daka cikin y'ar Uwar mu, daidai lokacin zarah tazo, aysha tace zarah tafi ki bamu waje daka yau duk wani girmamaki da muke ya zube keba yar.......  Ummi tace ya isa haka ya isa, kuna zarginta akan abunda baku sani ba labari ummi ta basu, kuka suka fara tare da ro'kan zarah gafara Zainab tace Mai yasa kika boye mana kikayi komai ke d'aya,? Zarah tace zainab mubar wannan maganan yanzu tunda mun dawo da dukiyar mu sai mu dau fansa akan kashe mana mahaifi, khairat tace hakane yanzu saimu kira rahma tazo itama mu d'auki fansa tare, aysha tace toh mama Amina itama tare kukeyin aikin da ita? Zarah tace eh itama tasan komai.




Rahma tana zaune tana had'a kaya dan tafiya kaduna wajan y'an uwanta domin d'aukan fansan mahaifinsu, Haulat tace rahma kiyi sauri Kar kiyi zuwan dare rahma tace toh, jin karan mota sukayi ya tsaya kofar gidan, fita rahma tayi taga mutanan Mahmud ne mutum d'aya ne yazo inda rahma take, yace Kina lisafi koh? Bata kulashi ba ta kira yaran dake karatu tace su korashi yara suka fara mishi ihu tare da tureshi har yana faduwa, koda suka kaishi waje ranshi a bace rahma ta kwashe da dariya tace karka kara zuwa nan har sai lokacin ku ya cika, tana fad'in haka ta koma, rahma ta tawo kaduna, koda alh Mahmud ya sami Labarin tabar kauyen da kanshi yaje ya sami Haulat tace rahma ta karaya ne tabar garin? Tace ko d'aya rahma bata da tsoro a kullum bata sama ranta faduwa sai nasara dan haka zata dawo, kuma tun yanzu ka Fara sawa ka fad'i, murmushi yyi tare da barin wajan.



Aneesa tana kwance taji karan Abu ya fad'i kaman glass tashi tayi, Tana bude ido taga hotan alh Ibrahim ga jini a jiki, wani irin ihu ta saki tare da fita daka d'akin da gudu tayi kasa tana ihu, dukansu dake gidan suka fito, zarah tace Aneesa mai nene? Cikin kuka tace naga alh I....... Shuru kuma tayi tana sauke ajiyan zuciya zarah tace wa kika gani? Tace zarah bani ruwa insha, zarah kitchen ta nufa ta d'auko mata ruwa tare da fad'in muje in rakaki d'akin ki, binta tayi cikin tsoro har suka shiga d'akin bata ga komai ba, zarah tace ki kwanta aneesa babu abunda zai faru Nasan mafarki kikayi, fita zarah tayi tare da rufe ma Aneesa kofa, ranan dai kasa komawa bacci tayi dan idonta biyu har gari Ya Waye, bayan ta shiga toilet tayi wanka ta nufi mirror taga anyi rubutu da jini *Aneesa Kun kashe ni Kema saina kashe ki saina dau fansa* ihu ta saki tare da fita daka d'akin da gudu, tana ihu, da magajiya sukaci karo Aneesa tace magajiya alh Ibrahim yace zai kasheni zai d'auki fansa a ka.....  Da sauri magajiya ta toshe mata baki ganin su zainab sunzo wajan suna tambaya lafiya, aneesa cikin kuka take fad'in Wlh naga rubutu a mirror dina da jini, zarah tace muje mu duba Aneesa kin binsu tayi koda suka shiga d'akin babu komai a mirror dariya sukayi tare da fad'in u wil pay for what u did Aneesa, wayar magajiya ne yayi kara ta d'auka ban San mai aka fad'a mata ba naga taja hannun Aneesa zuwa d'akinta, magajiya tace Aneesa muna cikin tashin hankali yanzu aka kirani Wai akwai shedar da aka Bari akan kisan alh Ibrahim a wajan da muka kashe shi Kinga ya kamata muje mu gani, aneesa tace yanzu kuwa, fita sukayi harda faruk suka nufi gadar da suka kashe alh Ibrahim sai dube dube suke a wajan, suna cikin duba Abu saiga zarah da y'an uwanta sunzo Aneesa cikin tsoro tace Mai kukeyi a nan? Zarah tace munzo wajanki ne keda kika kashe mana mahaifi Munzo d'aukan fansa, baya Aneesa ta farayi aiko tana cikin yin baya ta fad'a daka gadar Allah ya taimaketa ta ri'ke karfan gadar sa  hannu d'aya, ihu ta Fara saki magajiya ta Fara kiran faruk dake mota jin ihunsu yasa faruk yazo da gudu ko Lura da Suwa suke wajan baiyi ba Ya fara kokarin kamo Aneesa yace Aneesah bani hannunki bazan bari ki mutu ba kaman yanda Abba ya mutu Nayi takaici dana kasa ceton Abba bani hannunki, magajiya dake tsaye jin faruk ya tona asiri yasa ta d'aura hannu a Kai cikin ikon Allah faruk ya ciro Aneesa sai a sannan yaga y'an uwanshi dasu ummi  da mama Amina, yace zara.... Kafin ya karasa zarah ta wankeshi da Mari zai kara magana ta kara sakar Mai wani Marin tace faruk mai Abba yayi maka da ya Fuskanki wannan sakayyan da kayi mishi faruk ka cucemu ka nuna ma duniya kai d'an sale ne ka d'auko halin ubanka dai dai lokacin police suka zo harda mutumin dasu aneesa suke bama kud'i, mutumin yace zarah faruk bashi bane ya kashe mahaifinku Bari in fad'a muku yanda Abun ya faru......... Ku biyoni danjin yanda abun ya faru






     *vote*
*comment nd share*

*maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now